El-Rufai da gwamnati na cacar-baki kan sulhu da ƴanbindiga

Lokacin karatu: Minti 5

Sabuwar cacar-baki ta kunno kai tsakanin Nasir El-Rufa'i da gwamnatin tarayya bayan tsohon gwamnan ya caccaki gwamnatin tare da zargin ta da ta'azzara matsalolin tsaro ta hanyar "ƙarfafa ƴanbindiga" maimakon ƙoƙarin kawo ƙarshen matsalar baki ɗaya a sassan ƙasar.

El-Rufai ya yi zarge-zargen a zantawarsa da tashar talabijin ta Channels a ranar Lahadi, inda ya ce gwamnatin na taimakon ƴanbindigar ta hanyar ba su maƙudan kuɗaɗe ta bayan fage.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya take ta bayyana nasarorin da ta ce tana samu a yaƙin da take yi da ƴanbindiga da sauran matsalolin tsaro a ƙasar.

A ƴan makonnin baya ne gwamnatin ta sanar da wasu manyan nasarorin da ta ce ta samu a yaƙi da matsalar tsaro a faɗin ƙasar, ciki har da kama jagororin ƙungiyar Ansaru da ake zargi da kitsa hari kan gidan yarin Kuje, sannan kuma aka daɗe ana neman su ruwa a jallo.

Haka kuma gwamnatin ta sanar da kashe wasu jagororin Boko Haram, sannan ta sanar da ceto wasu mutane masu yawa daga hannun ƴanbindiga.

Sai dai wasu na zargin cewa kuɗin fansa aka biya, lamarin da masana harkokin tsaro a ƙasar suke ganin duk da ana samun nasarar kamawa da kashe wasu manyan ƴanbindiga, akwai sauran aiki a gaban gwamnati.

'Biyan ƴanbindiga alawus'

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya zargi gwamnatin Najeriya da mayar da ƴanbindiga shafaffu da mai ta hanyar ba su abin da ya kira "alawus na wata-wata da abinci".

A cewarsa, "gwamnatin na biyan ƴanbindiga alawus na wata-wata sannan tana aika musu da abinci duk da sunan amfani da sasanci wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro a Najeriya.

"Ni dai ba zan taɓa iya bai wa ƴanbindiga kuɗi ba, ko in aika musu da abinci. Kawai ana ƙarfafa ƴanbindiga ne."

A game da waɗanda yake zargi da jan ragamar matakan gwmnatin, ya ce, "tsarin gwamnatin ne da ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro ke jan ragama, kuma jihar Kaduna na cikin tsarin."

Ya kuma soki tsarin na gwamnatin da ya ce ana gyara halin ƴanbindiga maimakon a tabbatar suna fuskantar hukunci, wanda a cewarsa hakan ne ya sa matsalolin tsaro suke ƙara ta'azzara a ƙasar.

"Ni na daɗe ina faɗa cewa tubabben ɗanbindiga shi ne wanda ya mutu. Kawai mu kashe su, a yi ta musu luguden bama-bamai, sai a ƙarshe wataƙila kamar kashi biyar da suke son tuba, sai a gyara tunaninsu."

Ya ce bai kamata a ƙarfafa maƙiyi ba, "bai dace ka ba shi kuɗi ba domin zai sayo manyan makamai ne na ƙara shiri."

A game da nasarorin da gwamnatin ke cewa tana samu, El-Rufa'i ya ce farfaganda ce kawai, "za su iya yin farfaganda da rufa-rufa, amma mazauna Katsina da Zamfara da Kaduna sun san haƙiƙanin abin da ke faruwa," in ji shi, inda ya ƙara da cewa a ƙaryata shi, "zan fito da komai."

'Maganganu ne marasa tushe'

Da yake mayar da martani kan zarge-zargen da ya yi, Nuhu Ribadu ya ce kalaman na El-Rufa'i "ba gaskiya ba ne, kuma ba su da tushe ballantana makama," in ji shi a wata sanarwa da Zakari Mijinyawa ya fitar a madadin ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro.

"A wannan gwamnatin ba a taɓa samun inda ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro ko wata hukuma ta gwamnatin take jagorantar biyan ƴanbindiga kuɗin fansa ko take ƙarfafa masu laifi. Zarge-zarge ne waɗannan marasa tushe da makama."

Sanarwar ta ƙara da cewa sun daɗe suna gargaɗin ƴan Najeriya a kan rashin dacewar biyan kuɗin fansa ga ƴanbindiga, "don haka zargin El-Rufai' ya saɓa da abin da yake na zahiri."

Ofishin ya ƙara da cewa tun a farkon wannan gwamnatin suka amince da amfani da tsare-tsare biyu ne wajen yaƙi da matsalar tsaro, inda ya ce suna amfani da ƙarfin bindiga da kuma lalama.

Ya ce tsarin na lalama ya yi amfani a ƙananan hukumomin Igabi da Birnin Gwari da wasu sassan Kaduna, inda a cewarsa a yanzu an samu sauƙi bayan kasancewa cikin tashin hankali a baya.

"A Kaduna kaɗai jajirtattun jami'an tsaronmu sun kashe manyan ƴanbindiga irin su Boderi da Baleri da Sani Yellow Janburos da Buhari da Boka da wasu.

Haka kuma a kwanakin baya an kama shugabannin Ansaru da suka taɓa kafa sansani a Kaduna," kamar yadda sanarwar ta nuna, inda ta ƙara da cewa har wasu sojoji ƙasar ta rasa a wannan ƙoƙarin.

A watan Yulin da ya gabata ne Nuhu Ribadu ya ce matsalolin tsaro a arewacin Najeriya sun ragu matuƙa a shekara biyu da fara gwamnatin shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Ya bayyana haka ne a wani taron dattawan arewa da Gidauniyar Ahmadu Bello ta gudanar a jihar Kaduna, inda ya ce zuwa watan Mayu, sun samu nasarar kuɓutar aƙalla mutum 11,259 daga hannun masu garkuwa.

Sulhu ko amfani da ƙarfi?

Matsalar rashin tsaro ta daɗe ta na addabar yankuna da dama na Najeriya, inda masu ɗauke da makamai ke kashe mutane tare da tarwatsa su daga muhallansu da kuma sace waɗanda suka faɗa hannunsu domin karɓar kuɗin fansa.

Duk da ikirarin da gwamnatin Najeriya ke yi na ɗaukar matakan kawo ƙarshen lamarin, amma abin ya ci tura.

Ko a baya-bayan nan an samu rahoton munanan hare-haren ƴan fashin daji a jihohin Zamfara da Katsina, inda aka yi asarar rayuka masu yawa.

A Zamfara masu garkuwa da mutane sun kashe aƙalla mutum 38 da suke garkuwa da su duk kuwa da cewa sun karɓi kuɗin fansa, a Katsina kuma irin wadannan ƴan fashi sun kashe masu ibada a masallaci aƙalla 28 lokacin da suka kai hari a wani kauye.

Wasu na ganin cewa baya ga amfani da karfin soji, ya kamata gwamnati ta duba yiwuwar tattaunawa da ƴan fashin dajin domin kawo ƙarshen matsalar, sai dai ba kowa ne ya yadda da hakan ba.

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal - wanda jiharsa ta kasance cbiyar wannan rikici - ya sha nanata cewa ba zai taɓa yin sulhu da ƴan fashin daji ba.

Amma gwamnatin jihar Kaduna ƙarƙashin gwamna Uba Sani ta yi sulhu da ƴan fashin daji a wasu daga cikin ƙananan hukumomi da irin wannan matsala ta yi wa katutu.

Har yanzu batun yin sulhu ko kuma amfani da ƙarfi domin magance matsalar ƴan fashin dajin na cikin abubuwa da suka fi rarraba kawunan gwamnonin jihohin yankin arewa maso yammacin ƙasar, waɗanda ake ganin wajibi ne su hada kai domin yin aiki tare ta yadda za a kawo ƙarshen matsalar.