Yawan mutanen da suka mutu a wata fashewa a Iran ya kai 40

Lokacin karatu: Minti 3

Hukumomi a Iran, sun ce aƙalla mutum 40 ne suka mutu, wasu 800 kuma suka jikkata a wata gagarumar fashewa da ta auku a Daya daga cikin manyan tasoshin jirgen ruwan ƙasar.

Har yanzu ba a tabbatar da abin da ya haddasa fashewar ba a tashar Shahid Rajaee, inda har yanzu wutar ke ci, amma kuma kafofin yada labarai na kasar na nuna yuwuwar hannun Isra'ila a lamarin.

Fashewar wadda ta auku ranar Asabar da safe ta kasance ne a daya daga cikin manyan tashoshin jirgin ruwa na kasuwanci, da ke kusa da birnin Bandar Abbas na kudanci.

Fashewar ta lalata motoci da tagogi da rufin gine-ginen da ke kusa da wajen . Sannan mazauna unguwannin da ke nisan kilomita 30 sun ji kararta.

BBC ta tabbatar da sahihancin wasu hotunan bidiyo da ke nuna wuta na ci ganga-ganga kafin fashewar da da ta auku a wani gidan ajiyar kaya, inda mutane ke gudun tsira da kuma wasu yashe cikin jini a gefen titi kusa da tarkacen da ke cin wuta.

Hoton da aka dauka daga sama ya nuna akalla wuri uku da wutar ke ci inda ministan harkokin cikin gida ya tabbatar da cewa wutar na bazuwa daga sunduki ko kwantaina zuwa kwantaina .

An bayar da umarnin da kada a bude makarantun da ke kusa da wajen a ranar Lahadi.

Wani kamfanin al'amuran da suka shafi tsaro na ruwa ya ce yana ganin kwantainonin da wutar ta tashi suna dauke ne da makamashin da za a hada makamai masu linzami ne da su.

Kamfanin na Ambrey Intelligence ya ce yana ganin wutar ta tashi ne sakamakon rashin alkinta makamashin yadda ya dace.

Kamfanin ya kara da cewa yana sane cewa wani jirgin ruwa na Iran ya sauke wannan makamashi a tashar ruwan a watan Maris da ya gabata.

Ko a can baya daman jaridar Financial Times ta ruwaito cewa wasu jiragen ruwa biyu sun yi dakon makamashi daga China zuwa Iran.

Daga bisani hukumomin kwastan na kasar ta Iran sun fitar da sanarwa da tashar talabijin ta kasar ta bayar da rahoto a kai cewa , fashewar kila ta auku ne sakamakon wutar da ta tashi a wani rumbun ajiyar makamashi da ke kusa.

Haka kuma a wasu karin bayanai da hukumomin suka fitar kamfanin na Ambrey ya ruwaito hukumar kai dauki ta kasar na cewa tun a baya jami'anta sun yi gargadi ga tasahr jirgin ruwan dangane da yadda aka adana wannan makamashi.

Shugaban kasar ta Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana takaicinsa da damuwa tare da jajanta wa wadanda fashewar ta shafa, sannan ya bayar da umarnin a gudanar da bincike.

Ya kuma tura ministan cikin gida ya jagoranci binciken.