Waiwaye: Buhari ya halarci taron MDD, Kotu ta aika dan China kurkuku bisa zargin kisan Ummita

Shugaba Buhari

Asalin hoton, OTHER

A wannan makon ma, mun duba wasu labarai da suka fi jan hankali a Najeriya. Ga wasu daga cikinsu:

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya nanata kudurinsa na tabbatar da cewa an gudanar da sahihin zabe a kasar a 2023.

''A matsayina na Shugaba, daya daga cikin tarihin da nake son bari shi ne na ga cewa an gudanar da sahihi kuma tsabtataccen zabe. Ta hakan ne 'yan Najeriya za su zabi shugabannin da suke so,'' in ji Buhari.

Shugaban ya kara da cewa ''A yanzu muna shirin gudanar da babban zabe a Najeriya a watan Fabrairun badi. Saboda haka a taron Majalisar Dinkin Duniya na 78, za ku ga sabuwar fuska ne a kan wannan munbari'', a cewar Shugaba Buhari.

Shugaban zai kammala wa'adin mulkinsa karo na biyu a watan Mayun badi, inda zai mika mulki ga sabuwar gwamnati.

Za mu tabbatar doka ta yi aiki game da kisan Ummita - Ganduje

Ummita

Asalin hoton, FACEBOOK/UMMULKHAIRI SANI BUHARI

Dr. Abdullahi Umar Ganduje yayin wani jawabi da ya gabatar a fadar gwamnatin jihar ya ce "Kisan nata zub da jini ne, don haka dole maganar shari'a ta shigo kuma sai doka ta yi aikinta''.

Tuni aka gurfanar da mutumin da ake zargi da kisan Ummita, Mr Geng Quanrong mai shekara 47, a gaban kotu wadda ta tura shi kurkuku

Kotu ta umarci ASUU ta janye yajin aiki

Kotun ma'aikata

Asalin hoton, Getty Images

Da yake gabatar da hukunci kan bukatar wucin gadi da gwamnatin tarayya ta nema, Mai shari'ah Polycarp Hamman ya hana kungiyar ASUU ci gaba da yajin aiki har zuwa lokacin yanke hukunci kan shari'ar.

A farkon watan nan ne gwamnatin ta gurfanar da ASUU a gaban kotun kan yajin aikin da ta kwashe wata bakwai, inda ta ce tana son kotun ta bayyana halarci ko haramcin yajin aikin na ASUU.

To amma a nata bangare kungiyar ASUU ta ce za ta daukaka kara kan wannan hukunci.

INEC ta fitar da jerin sunayen ƴan takarar shugaban ƙasa na 2023 da ƴan majalisar dokoki

.

Asalin hoton, INEC

A ranar Talatar da ta wuce ne Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC, ta fitar da jerin sunayen ƴan takarar shugaban ƙasa da majalisar dattawa da kuma na majalisar wakilai na dukkan jam’iyyun ƙasar da za su fafata a zaɓukan 2023.

Hukumar zaben ta wallafa jerin sunayen ƴan takara daga dukkan mazaɓun ƙasar a shafin intanet.

Za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na majalisun dokokin tarayya ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, sai na gwamnonin da majalisun dokokin jihohi ranar 11 ga watan Maris din 2023.

A jerin sunayen, akwai ƴan takarar shugaban ƙasa da mataimakansu 18 daga jam’iyyu daban-daban, sai kuma ƴan takarar majalisun tarayya daga jihohi 36 da babban birnin ƙasar Abuja, ƙarƙashin jam’iyyu daban-daban.

Ba ni da hurumin sanya Iyorchia Ayu ya yi murabus - Atiku

Atiku Abubakar

Asalin hoton, AFP

Sannan kuma a cikin makon da muke bankwana da shi din ne dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a Najeriya Atiku Abubakar, ya fitar da wata sanarwa inda yake cewa ba shi da hurumin sanyawa ko hana shugaban jam'iyyarsu Iyorchia Ayu yin murabus.

A cikin sanarwar Atiku Abubukar ya ce ''Ce- ce-ku-cen da ake yi kan neman shugaban jam'iyyarmu ya aiye aiki, ina so na nanata abin da na riga na fadi a baya cewa mataki ne da Dr Ayu kadai zai iya dauka, ni ko wani daban ba mu da hurumin yanke wannan hukunci''.

Martanin na Atiku na zuwa ne jim kadan bayan bangaren Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike ya sanar da ficewa daga yakin neman zaben dan takarar a 2023, har sai Mr Ayu ya sauka daga mukaminsa kuma an nada sabon shugaba daga kudancin kasar.

Jam'iyyar PDP dai fada rikicin cikin gida ne tun bayan gudanar da zaben fitar da gwani na dan takarar shugaban kasa, zaben da ya bai wa Atiku Abubukar nasara.