Kotu ta umarci ASUU ta koma bakin aiki

Asalin hoton, OTHER
Kotun Ma'aikata ta Kasa ta umarci kungiyar malaman jami'o'i ta janye yajin aikin da take yi.
Da yake gabatar da hukunci kan bukatar wucin gadi da gwamnatin tarayya ta nema, Mai shari'ah Polycarp Hamman ya hana kungiyar ASUU ci gaba da yajin aiki har zuwa lokacin yanke hukunci kan shari'ar.
A farkon watan nan ne gwamnatin ta gurfanar da ASUU a gaban kotun kan yajin aikin da ta kwashe wata bakwai tana yi.
Mai shari'ah Polycap Hamman, wanda alkali ne da ke sauraron shari'ah a lokacin da kotun ke hutu ya kuma mayar da karar zuwa ga shugaban kotun ma'aikata don ya sake bai wa wani alkali wannan shari'ah.
Ma'aikatar kwadago ta kasar ta ce gwamnati ta dauki mataki ne bayan tattaunawa da kungiyar malaman jami'o'in ta ci tura.
A zamanta na farko, kotun karkashin jagorancin mai shari'a, Polycarp Hamman ta dage sauraren karar zuwa yau Laraba bayan ta saurari bayanai daga wurin masu shigar da kara da wadanda aka shigar kara.
Gwamnatin tarayya tana son kotun ta bayyana halarci ko haramcin yajin aikin na ASUU.

Asalin hoton, OTHER
Hukuncin kotun ma'aikatan na ranar Laraba na zuwa ne sa'o'i bayan kungiyar dalibai ta kasa NAN ta yi barazanar kawo cikas ga harkokin yakin neman zaben kasar da za a fara a Najeriya, matukar jami'o'i ba su koma aiki ba.
A farkon makon nan kungiyar ta yi zanga-zanga inda dalibai suka tilasta rufe harkoki a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Lagos, yayin da suka yi barazanar ci gaba da datse harkoki a filayen jiragin saman kasar.
Gwamnatin Najeriya dai na son kotun ma'aikata ta yi fashin-baki kan dokar kwadago mai sakin-layi 18 LFN 2004, musamman game da hukuncin shiga yajin aiki ana ci gaba da tattaunawa tsakanin ministan kwadago da malaman jami'o'i.
Tun da farko, Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ya bayyana cewa sun yi iya bakin kokarinsu wajen ganin an kawo karshen yajin aikin na ASUU.
ASUU ta shiga yajin aiki ne a watan Fabrairu sakamakon abin da ta bayyana gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatun jami'a na kasar.











