Shin Malaman jami'o'i na aikinsu yadda ya dace ko ci-ma-zaune ne ?

Asalin hoton, Festus Keyamo/Twitter
'Yan Najeriya da dama na ci gaba da zazzafar muhawara, musamman a shafukan sada zumunta, dangane da tirka-tirkar da ke yi tsakanin gwamnatin kasar da kungiyar ASUU, game da kin biyan malaman jami'o'i albashi saboda yajin aikin da suke gudanarwa.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar ta tsawaita yajin aikin bayan ganawar kwamitin zartarwa a hedikwatar Kungiyar da ke Jami'ar Abuja, babban birnin Najeriya.
Kungiyar ASUU dai ta shiga yajin aiki ne a watan Fabrairu, saboda gaza biya mata tarin bukatunta daga bangaren gwamnatin tarayayyar kasar.
Hakan ne ya sa gwamnatin kasar ta ki biyansu albashin watanni da suka shafe suna yajin aikin, saboda a cewarta malaman ba su yi aiki ba cikin wadannan watanni
To sai dai wannan batu na rashin biyan malaman albashi na ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya, inda kungiyar ta sanya shi cikin sabbin bukatun da take so gwamnati ta amince da su kafin janye yajin aikin, suna masu cewa ba koyarwa ba ne kadai aikin malamin jami'a.
Me masana ke cewa?

Asalin hoton, Twitter/ASUU
Masana da dama a kasar na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu game da batun, inda wasu ke ganin bai dace a biya malaman wadannan kudade ba saboda ba sa ayyukan da suka dace, daga cikin masu irin wannan ra'ayi har da Limamin babban masallacin kasar Farfesa Ibrahim Maqari wanda tsohon malamin jami'a ne.
A wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta a kasar an ga malamin na cewa mafiya yawan malaman ba sa aikin da ya dace a matsayinsu na malaman jami'o'i, yana mai zargin malaman da rashin gudanar da bincike, da daukar ayyukan wasu wadanda a cewarsa galibi dalibansu ne su harhada domin samun karin girma.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya kara da cewa da zarar sun samu abin da suke butaka to shikenan sai alkalamin bincikensu ya bushe.
Farfesa Maqari ya kuma zargi malaman da yin aiki na dan karamin lokaci, inda ya ce wasunsu na aikin sa'o'i hudu ko biyar zuwa shida a mako, yana mai cewa da wuya a samu malamin jami'a da yake aiki sa'o'i goma a mako.
Haka kuma shi ma Abdulaziz Abdulaziz, wani fitaccen dan jarida a kasar a wani rubutu da yi a shafinsa na Facebook, yana ganin bai dace gwamnati ta biya malaman ba saboda ba su yi aiki cikin wadannan watanni ba.
''Mene ne hukuncin mutum ya ci kuɗin aikin da bai yi ba? Me ye madogarar ɗan ASUU da ya dage sai an biya shi albashin watannin da ya yi baya aiki (don raɗin kansa!)? Na daɗe ina wannan tunanin!"Matambayi ba ya ɓata! '' Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.
To sai dai ba duka aka taru aka zama daya ba, a yayin da wasu ke ganin bai dace a biya malaman ba, wasu na ganin tilas ne a biya malaman hakkokinsu.
Dakta Marzouk Ungogo na da irin wannan ra'ayi inda yake cewa ba koyarwa ba ne kadai aikin malamin jami'a domin kuwa malamin jami'a na da ayyuka iri uku da suka hadar da koyarwa, bincike da aikin al’umma.
''Idan an bai wa lakcara 4 credit units ya koyar, hakan na nufin zai ga ‘dalibai ya yi musu lakcar awa hudu a sati. Amma ana bukatar ya shirya tsaf kafin ya je gabansu. Yawanci ana bukatar yin shiri na ninkin lokacin lakca sau biyu. Wato, idan za kai lakcar awa hudu, to ka ware awa takwas ko sama da hakan domin shiri.
''A iya tunanina, In banda ma’aikatan asibiti, har gobe babu ma’aikatan da suke kokarin cin halak a Najeriya kamar lakcarori. Akwai baragurbi a cikin lakcarori, amman ni na yi imani ba su kai na kwarai yawa ba,'' kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Haka kuma shi ma Farfesa Ibrahim Malumfashi na Jami'ar Jihar Kaduna, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, yana da wannan ra'ayi inda yake ganin baiken mutanen da ba sa goyon bayan a biya malaman albashinsu.
Yana ganin ya kamata mutane irin su Abdulazizi Abdulaziz su mai da hankali wajen sasanta tsakanin gwamanti da kungiyar ASUU a maimakon ganin baiken kungiyar ASUU.
Me daliban Jami'a ke cewa game da batun?
Jamilu Muhammad, wani dalibi ne a kasar ya kuma shaida wa BBC cewa ''hakikanin gaskiya wasu malaman ba sa abin da ya dace domin kuwa sai ka samu malami yana koyarwa a jam'i'oi uku ko sama, kuma ba zai fara koyarwa kan lokaci ba, sai lokaci ya fara kurewa ko ma zangon karatu ya zo karshe sai ya zo yana sauri, yana muku bura-bura, domin kammala koyarwarsa''
Haka shi ma Abdullahi Bala ya ce ''mafiya yawan malaman basa abinda ya kamata saboda sun dauki abin da ya fi karfinsu dan haka ba sa abin da ya dace a jami'o'in.
Amma a ganin Khadija Dankani malaman jami'o'in sun cancanci a biya su hakkokinsu, saboda kokarin da suke yi, ta ci gaba da cewa ''Gaskiya malamai suna kokari, saboda banda aikin koyarwa akwai duba ayyukan dalibai za ka iske malamai guda daya yana duba ayyukan daliban digiri akalla 30, da na digiri na biyu akalla bakwai sai kuma na digirin digirgir akalla mutum mutum uku, sannan sai ya duba kowanne aiki kuma ya yi masa gyara a kai.
Shima yusuf Sa'ad Jibya ce wa ya yi ''Ina cikin daliban da suke son a biya malaman jamai'a kudadensu da aka rike musu domin kuwa hakkinsu ne
A Najeriya dai rike wa malaman jami'o'i albashi a lokacin da suke cikin yajin aiki ba sabon abu ba ne , to sai dai a wasu lokutan gwamnatin kasar kan biya su albahin bayan sun janye yajin aikin nasu.











