Yadda hayaƙin bola ya turnuƙe wani birnin Indiya

Hoton bola da hayaƙi

Asalin hoton, ANI

Bayanan hoto, Ko a shekarar 2021 ma an samu tashin wuta a wannan wuri

Ƴan kwana-kwana a Indiya suna can suna ta fafutukar kashe wata wuta da ta tashi a wani tarkacen shara, wadda ta haifar da hayaƙi mai guba da ya rufe yankuna da dama a birnin Kochi da ke jihar Kerala.

Tun a makon da ya gabata ne wutar ta tashi a wata masana’anta da ake sarrafa tarin shara a kullum.

An shawarci jama’a da su zauna a gidajensu, idan kuma har ya zama dole su fita to su tabbatar sun sanya takunkumi na musamman samfurin N-95.

Hukumomin birnin sun ce za a rufe makarantun ƙananan yara.

Sai dai kuma daga baya gwamnatin jihar ta ce an yi nasarar shawo kan wutar inda take sa ran za a kashe ta zuwa wani ɗan lokaci.

Ana yawan samun tashin wuta a manyan ramuka da ake cike wa da shara a Indiya, yawanci saboda gubar da ke cikin sinadarai (methane), yayin da sharar ke rubewa.

Jami’ai sun ce daman ana yawan samun tashin gobara a wannan lokacin na shekara saboda tsananin zafi da ake yi.

Tun a baya jama’ar yankin sun riƙa ƙorafi a kan wutar inda suke kokawa a kan haɗarin da ke tattare da hayaƙin da ke fita saboda robobin da ake ƙonawa a wurin.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Zuwa yanzu ba a san abin da ya haddasa wannan wutar ba.

Wani jami’in kashe gobara ya faɗa wa ƴan jarida cewa tarin tarkacen ledoji da roba da ke ƙarƙashin inda wutar ta tashi ya jinkirta kashe ta.

Bayanai sun nuna cewa hayaƙin da wutar ta haifar ya sa wasu tarin ma’aikatan kashe gobarar hajijiya ko juwa.

Rahotanni sun ce aƙalla ƴan kwana-kwana 20 suka gamu da matsala ta numfashi sakamakon hayaƙi mai guba da suka shaƙa.

Ministar lafiya ta jihar, Veena George ta shawarci tsofaffi da yara da mata masu juna biyu da kuma mutanen da suke da wata larura ta numfashi da su tabbatar sun kauce wa hayaƙin.

Ms George ta ce gwamnatin jihar ta yi tanadi sosai a dukkanin asibitocin birnin domin kula da marasa lafiya masu larurar numfashi.

Amma kuma ta ce zuwa yanzu babu wani da aka samu da wata babbar larura.

Ƴan sandan birnin sun ce ana gudanar da bincike kan abin da ya haddasa wutar.

Hukumar da ke sanya ido don hana gurɓata yanayi da muhalli ta jihar ta umarci hukumomin yankin da su biya tarar rupee miliyan 18 ko dala dubu 220, saboda kasa bin dokokin kula da shara.