Sauyin yanayi: Me ake nufi da adana iskar carbon, shin zai iya ceto duniya?

Masanin kimiyya na kwaso samfurin sediment, da zai auna yawan iskar Carbon din da tsirrai ke rikewa a jikinsu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masana kimiyya sun ce ya kamata mu gane cire iskar Carbon abu ne mai muhimmanci, matukar mu na son ceto duniya
    • Marubuci, Daga Nidale Abou Mrad
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

Idan duniya na son kauce wa fuskantar sauyin yanayi mafi muni, ana bukatar masana'antu su tabbatar sun daina fitar da gurbataccen hayaki baki daya daga nan zuwa 2050, hakan na nufin za mu cire irin iskar carbon daga sararin samaniya ta kowacce fuska.

Hakan dai masana kimiyya na Majalisar Dinkin Duniya ke fata, wadanda suka yi gargadin muna cikin tsaka mai wuya sakamakon yadda ake samun karuwar digiri biyu na gurbataccen hayaki.

Wannan zai sanya wurare da dama a doron kasa su yi matukar wuyar zama.

Masanan sun ce abubuwa kamar dasa bishiyoyi da kimiyya, kamar kama carbon da adanawa, za su sanya a kauce wa mummunan bala'in sauyin yanayi. Sai dai ga yawancin masu rajin kare muhalli, wannan babbar barazana ce kuma bai dace ba sam.

Ta yaya ake kamawa da adana carbon?

Ana farawa da dasa bishiya, zuwa sauya yadda muke yin noma, da daina kona bishiyoyi a gonaki, wanda ke kara haddasa dumamar yanayi. Matukar za a kauce wa hakan lallai za a samu gagarumin sauyi.

Tun a shekarun 1970, aka samu ci gaban kimiyya wadanda aka yi wa lakabi da kamawa da adana carbon, daga lokacin ake ta samunsu cikin kankanin lokaci.

"Akwai hanyoyi da zabi da dama, wanda aka fi sa ni shi ne kama gurbataccen hayakin da masana'antu ke fiutarwa. Daga nan sai a adana shi cikin bututu a kuma adana shi," in ji Samantha McCulloch, da ke jagorantar shirin kamawa da adana Carbon a cibiyar kamakashi ta duniya.

Presentational grey line

Shirin ya hada da zukewa da adana carbon cikin bututun da ke dauke da sinadari solvent, ana kama carbon ana kuma sakin sauran iskar gas. Amma masana kimiyya na amfani da zafi wajen kebance carbon.

"Wata hanyar ta kama carbon shi ne a cirewa kai tsaye daga sararin samaniya ta hanyar iska.Koma wacce hanya aka bi, babu shakka wannna hanya ce ta dumama duniya,'' in ji ta.

'Lasisin fitar da karin mai'

Sai dai wasu masu rajin kare muhalli sun nuna damuwa, damuwar kuwa ita ce hanyar da za a bi a kama carbon zai sake ingiza fitar da gurbataccen hayaki cikin sauri maimakon hana fitarsa baki daya.

A shekarar 2021, babban taron kasashen duniya kan sauyin yanayi, ya ga irin tarin bincike da nazarin kimiyya da aka gudanar da zai taimaka wajen cimma wannan manufa.

A solar power station is seen under the shadow of peach blossoms in Zaozhuang, East China

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Investing in carbon capture technology slows down the transition to renewables, some environmentalists say

Babbar hanyar kaucewa fitar da hayakin da ke gurbata muhalli, ita ce kaucewa kona daji, kamar yadda Piera Patrizo da ke bincike kan sauyin yanayi Kwalejin Imperial da ke Birtani ta bayyana.

"Yawancin masu kare muhalli sun amince kudaden da ake kashewa wajen kama carbon, kamata ya yi ayi amfani da su wajen bunkasa samar da makamashi mai tsafta," in ji ta.

'Matakin da ya dace a dauka domin kauda gurbatacciyar iska

Masana kimiyya sun bukaci sai an tanadi makamashi mai inganci, sannan ne za a kaucewa gurbacewar muhalli, da fiytar da gurbatacciyar iskar da ke janyo mummunann dumamayar yanayi a duniya. Sun karkare da kare bayanan ta hanyar tarasu a wani kundi da aka wallafa rahoton a farkon watan nan.

Wasu na ganin cire carbon dioxide na daga cikin hanyoyin da suka rage da za a magance rage gurbataccen hayaki, misali irin hayakin da manyan masana'antu da kamfanoni ke fitarwa, wanda ke yin illa ga muhalli da duniya baki daya.

Uwa da 'yar ta na shuka a gona

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shuka bshiya sassaukar hanya ce kuma mai inganci wajen kama carbon

"Wannan hanya na bukatar tsananin zafi. Sannan kusan kashi daya cikin uku na hayakin da masana'antu ke fitarwa na dauke da sinadarai masu gurbata muhallai, ana kum abutara daukar matakn kare hakan," in ji Samantha McCulloch.

Hanya mafi sauki, da kare afkuwar abin da masana kimiyya da masu rajin kare muhalli ke kokarin kaucewa, shi ne samar da sabbin dazuka ko alkinta wadanda ake da su, hakan hanya ce ta kaucewa lalata muhalli da gurbataccen hayaki ke haifawar a duniya. Sai dai Patrizio ta ce akwai kuma yanayin da akan shiga da ba sa yi wa muhalli illa sosai, amma hakan ba abin dogaro ne ba.

"Manufar shuka bishiyoyin kamar na wucin gadi ne, matukar ba za a dauki matakin kaucewa yin abin da ke haddasa gurbacewa da fitar da hayakin gurbatacce, har sai an tabbatar da alkinta dazukan da ake da su," ta kara bayani.

Sai dai masana na cewa a wasu kasashen duniya, lamarin babu sauki wajen zuba jari a fannin makamakashi mai inganci, ba kuma kowa ake bari ya yi hakan ba. Sannan a kasashen da suke sahun gaba a fitar da gurbataccen hayakin, lamarin mai sauki ne.

Sabuwar hanya ce kuma mai tsada

Fanka a wata ma'aikata da ke kama iska kai tsaye a wata cibiya da ke Zurich a kasar, Switzerland

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Amfani da iskar fanka na kama carbon tare da adana su a karkashin kasa

"Sai dai har yanzu sabuwar hanyar kimiyya ce da ba a waye da ita ba," in ji Christoph Beuttler, shugaban kungiyar Climework, cibiya ta farko ta 'yan kasuwa da ke aikin kama carbon kaiu tsaye daga iska.

"Aikinmu shi ne samar da fankoki a manyan ma'aikatu da masana'antu da kamfanoni, domin cire carbon daga sararin samaniya, tare da adanawa ta dindindin a karkashin kasa," in ji shi.

Bayani kan yadda ake kama carbon ta amfani da fanka

Asalin hoton, Climeworks

Bayanan hoto, Ana amfani da fanka wajen zuke iska tare da adana ta

Hoton sama ya nuna yadda kai tsaye ake kama carbon ta amfani da iskar fanka, kuma ba tare da wata babbar barazana ko matsala ga muhalli ba.

Sai dai a yanzu abin tambayar shi ne, ta yaya za a ci gaba da yin amfani da iskar fankar wajen kama carbon, sannan ko hakan zai yi tasari nan gaba.

Buri nan gaba

Wata matashiya rike da allon da aka rubuta 'Ba mu da wata duniyar bayan wannan' a lokacin machin da aka yi kan sauyin yanayi a Toulouse, da ke Faransa a shekarar 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu na gani duniya na bukatar ayi amfani da iskar da ke dumama yanayi, amma ana bukatar a san yadda za a yi amfani da su domin kar su zama illa ga muhalli

Masu goyon bayan yaki da sauyin yanayi (CCS) sun ce ko da an daina amfani da makama daga nan zuwa shekarar 2030 ko 2040, tsohon hayakin da ya gurbata iska ya na nan. Wannan shi ne kwararru suka kira carbon mai tsohon tarihi da ake bukatar kakkabewa.

"Shin hayakin ya gurbata mana duniya ne? kuma ta yaya za a magance hakan? wadanda ke goyon bayan ci gaba da amfani da gurbatacciyar iska ba su yi adalci ba. Wasu na ganin kamar ba mu damu ba, mun damu matuka," in ji Patrizio ta Kwalejin Imperial da ke Landan.