Asara da illolin da sauyin yanayi ke haifarwa

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Navin Singh Khadka
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Environmental Correspondent, BBC World Service
Manyan abubuwa biyu da za a mayar da hankali a kai a taron sauyin yanayi na wannan shekara a ƙasar Masar ba zai wuce kan asara da kuma rashi da sauyin yanayi ke haddasa wa ba.
Amma me ake nufi da hakan takamaimai? Me ya sa ake ce-ce-ku-ce a kai?
Yarjejeniyoyi da ake son cimmawa kan sauyin yanayi ba ya wuce na batun yadda kamfanoni za su rage fitar da gurbataccen iska da kuma yadda za a shawo kan tasiri da sauyin yanayin ke kawowa.
Batu na uku da za a tattauna a taron kuma shi ne – ko kasashe da ke da manyan masana’antu da ke haifar da matsala, za su biya kasashen da sauyin yanayin ke shafa wasu kudade.
Bala’o’i kamar ambaliyar ruwa da fari da mahaukaciyar guguwa da girgizar kasa da kuma gobarar daji na ci gaba da afkuwa sakamakon sauyin yanayi, inda kasashen da sauyin yafi shafa ke son a biya su diyya na tsawon shekaru don ganin an rage musu raɗaɗi.
Wannan shi ake nufi da ‘asara da kuma illoli na sauyin yanayi’’. Asarar ta kuma shafi tattalin arziki – rashin gidaje da filaye da gonaki da kuma wuraren kasuwanci – da sauran abubuwa kamar asarar rayuka da rasa wuraren al’adu ko kuma na kabilu daban-daban.
Kudin da wadannan ƙasashe ke bukata yana kuma cikin tsarin nan da ƙasashe masu arziki suka amince cewa za su bai wa matalautan ƙasashe $100bn domin taimaka musu wajen:
. rage gurbataccen iska da kamfanoni ke fitarwa
. daukar mataki domin rage tasirin sauyin yanayi
"Mutane na fama da asara da kuma illolin da mahaukaciyar guguwa da ambaliyar ruwa da kuma zubar dutsar ƙankara suka haifar, inda mutane da ke ƙasashe masu tasowa basa samun taimako da ta kamata domin sake gina wurare ko farfadowa daga bala’o’i,’’ a cewar Harjeet Singh, shugaban sashin siyasa na wata kungiya mai zaman kanta da ke son rage bala’in sauyin yanayi.
''Al’ummomi ma na da hannu wajen haifar da wadannan bala’o’i da ake fuskanta a duniya.''
Ta ya ya girman kudurin asara da kuma illolin sauyin yanayi yake?
Wani sabon rahoto da hadakar masu bincike 100 da kuma masu ruwa da tsaki a fadin duniya suka fitar kan asara da kuma illolin sauyin yanayi, ya nuna cewa ƙasashe kusan 55 sun samu asara ko kuma ko ma baya na tattalin arziki wanda ya kai sama da rabin dala tiriliyan tsakanin shekarar 2000 da 2020.
Hakan kuma zai iya ƙaruwa zuwa wani rabin tiriliyan a shekaru goma masu zuwa.

Asalin hoton, Getty Images
"Kowane dumamar yanayi da aka samu, hakan na nufin za a gamu da tasirin sauyin yanayi, inda aka kiyasta cewa asara da sauyin yanayin zai haifar a ƙasashen da suka ci gaba zai kai tsakanin dala biliyan $290 da kuma dala biliyan $580 zuwa shekara ta 2030,’’ a cewar Harjeet Singh.
An samu ƙaruwar yanayi zuwa maki 1.1 na ma’aunin celcius a duniya, idan aka kwatanta da lokacin da babu masana’antu.
Matalautan ƙasashe da basu da masana’antu da yawa, sun ce sauyin yanayi na kawo cikas ta wajen samun ci gaba a bangaren tattalin arziki.
Wasu kuma sun ce bashi ya yi musu katutu, inda suke ciyo bashin domin sake gina abubuwan da aka rasa.
Tsawon wane lokaci aka dauka ana tattaunawa kan biyan ƙasashe da suka yi asarar kudi?
Shekaru bakwai da suka gabata, yarjejeniya da aka cimma a birnin Paris, ya duba muhimmancin ‘karewa da ragewa da kuma shawo kan asara da aka samu a bangaren sauyin yanayi’’. Amma ba a taba yanke shawar yadda za a yi hakan ba.
''Asara da aka samu ya kasance batu da aka yi ta magana a kai na tsawon shekaru, kuma mun ga zafafan muhawarori tsakanin ƙasashen da suka ci gaba da kuma masu tasowa,’’ a cewar Jochan Flasbarth, sakataren harkokin cikin gida a ma’aikatar tattalin arziki da ci gaba a ƙasar Jamus.
''Akwai alamun damuwa a ƙasashen da suka ci gaba cewa za a sanya batun shari’a ga kamfanonin da ke fitar da gurbataccen iska. Wannan ya zama abin tayar da jijiyoyin wuya tsakanin kasashen da suka ci gaba.’’
A dalilin haka, matalautan ƙasashe da dama basa neman a biya su diyya, sai dai neman taimakon kudi daga wajen ƙasashen da suka ci gaba.

Asalin hoton, Getty Images
"Muna neman taimakon kudi domin rage raɗaɗin da ƙasashe masu tasowa suke fuskanta a kullu yaumin,’’ a cewar Alpha Oumar Kaloga, babban mai shiga tsakani na sauyin yanayi a wata kungiya ta Afirka a tarukan Majalisar Dinkin Duniya.
"Sai dai, batun baya karewa, yayin da muke ci gaba da fuskantar ƙaruwar asara daga sauyin yanayi. Ana ganin hakan kamar wani yunkuri na jinkirta abubuwa daga ƙasashen da suka ci gaba.''
Shin za a tattauna kan batun asara na sauyin yanayi a taron COP27?
Ƙasashe masu tasowa na son a tattauna kan batun ‘biyan kudin asara da sauyin yanayi ya haddasa’ a taron da za a yi a Masar, sai dai za a yanke shawara a kan batun ne kafin fara taron – kuma dukkan ƙasashe sai sun amince kan hakan.
"Pakistan ta bijiro da maudu’in a madadin ƙasashe masu tasowa, kuma ana son amincewa da shi a farkon taron na COP27,’’ a cewar Saleemul Huq, darektan wata cibiya ta ƙasa da ƙasa kan sauyin yanayi da kuma ci gaba a Bangladesh.
"Idan har akwai ƙasar da taki amincewa da maudu’in da har ya sa aka ajiye shi, to hakan zai nuna gazawar taron na COP27 tun kafin fara shi.’’
Me zai sa a samu bambance-bambance kan batun na asarar sauyin yanayi?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Da wuya ƙasashe su amince kan kungiyar da za ta kula da kuɗaɗen da za a biya na asarar sauyin yanayi.
Ƙasashen da suka ci gaba sun ce akwai tsarin da hukumar da ke kula da suayin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya ta kirkiro kan wanda za a bai wa alhakin kula da batun kuɗaɗen.
Ƙasashe masu tasowa sun ce babu wata kungiya a yanzu da za ta iya rike kudin da za a biya.
"Alal misali, ina wadannan kungiyoyi suke lokacin da ambaliya ta ɗaiɗaita Pakistan, ko ambaliya a Najeriya, ko kuma lokacin da mahaukaciyar guguwa ta Ian ta lalata yankin Caribbean? A cewar Michael Robertson, mai shiga tsakani kan sauyin yanayi na kungiyar hadakar jihohin ƙananan tsibirai, wanda ya kunshi ƙananan ƙasashe guda 39 da ke aiki tare a tarukan sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya.
"Ba sa magance asara."
Dukkanin kungiyar ƙananan tsibiran da kuma wata a kungiya Afirka, suna fafutukar neman a biya su ƙudade, amma shi ya bambanta da kungiyoyi da ke samar da kudi na sauyin yanayi da ake da su. Sai dai, Mista Flasbarth ya ce bukatar wuri guda daya kadai ba zai samar da taimakon da ake bukata ba.
Shin akwai wani ci gaba da aka samu gabanin taron na COP27?
Lokacin taron COP26 a bara, yankin Scotland ya yi alkawarin bayar da taimakon $1m kan asarar sauyin yanayi. A watan da ya gabata, Denmark ta sanar da cewa za ta taimaka da $13m.
Ko a makon da ya gabata ma, ‘yan majalisar Turai, sun yi kiran mai da hankali kan taimakawa ƙasashe masu tasowa da bukatar bayar da tallafi maimakon bashi domin karewa da kuma rage hadarin asarar da sauyin yanayi ke haifarwa.

Asalin hoton, Getty Images
A tarukan G7 da na V20, kungiyar matalautan ƙasashe 55, sun amince da kirkiro da wani tsari da za rage barazanar sauyin yanayi a duniya. Tsari zai kuma samar da taimakon kuɗaɗe, ta hanyar wani shirin inshora.
Aosis ta ce hakan ba zai yi wani tasiri ba saboda V20 bata da ko rabi na mambobi da Aosis ke da shi.
"Ya kamata G7 ta tafi da kowa," a cewar mai shiga tsakanin Michai Robertson, ‘ba wai ƙasashe da suka zaba kadai ba.’’
Shin ƙasashe matalauta na iya karɓar ƙarin kuɗin sauyin yanayi?
Ayyukan hukumomin samar da kuɗaɗe na duniya na daukar tsawon lokaci kafin samar da kuɗi.
Sannan akwai matsalar rashin kyawun gwamnati da kuma cin hanci a wasu ƙasashen da ke samun kuɗaɗen.
Duk da haka, matalautan kasashe ba za su dauki wannan a matsayin hujja ta tura asarar da sauyin yanayi ya haddasa ba zuwa bangare daya.











