Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda aka tsaurara matakan tsaro saboda zaɓen gwamna a Anambra
Yayin da a yau Asabar ake gudanar da zaben gwamna a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya, inda gwamna mai ci na jam'iyyar APGA zai fafata da sauran 'yan takarar wasu jam'iyyu, al.'ummar jihar sun yaba da irin matakan tsaron da aka dauka.
An yi tanade-tanaden da suka kamata, don ganin an gudanar da zaben yadda ya kamata cikin kwanciyar hankali.
Alhaji AbdulLahi Araba, mataimakin Sarkin Hausawa na garin Nnewi, ya shaida wa BBC cewa ya gamsu kwarai da gaske da irin matakan tsaron da aka dauka.
Ya ce,"Wannan zaben ya sha banbam da zabukan baya saboda a wannan karon an jibge jami'an tsaro sosai wanda hakan zai sa mutane su daina fargaba abin da zai iya biyo bayan zaben kamar tashin hankali da sauransu, da farko mutane gaskiya sun ji tsoro har ma suna cewa ba za su iya fitowa su kada kuri'a ba, to amma ganin yadda aka tanadi jami'an tsaro yanzu mutane na ta zumudin fita don kada kuri'arsu."
Baya ga inagantar matakan tsaro a jihar ta Anambra, an kara baza jami'an tsaro a wuraren daban-daban dangane da wannan zabe.
Mista Emmanuel Elias, wani mutumin garin na Nnewi ne, ya shaida wa BBC cewa an kawo sojoji da 'yan sanda da yawa kuma suna nan suna sintiri.
Ya ce," Jibge jami'an tsaron da aka yi a sassan jiharmu zai kwantarwa da mutane hankali su fita su yi zabe don naga da yawa yanzu mutane na cewa za su je su kada kuri'arsu saboda sun gamsu da yadda aka dauki matakin tsaro don kare duk wata fitina."
Wannan zabe dai wani zakaran gwajin dafi ne, game da kamun ludayin hukumar zaben Najeriya, kasancewar shi ne na farko, tun bayan rantsar da sabon shugaban hukummar, Farfesa Joash Ojo Amupitan, makwanni biyu da suka gabata.
Ana kuma sa ran zaben zai kawo sauye-sauyen da samar da zabe mai tsafta da inganci.
Jihar Anambra na da matuƙar muhimmanci a Najeriya saboda tana daga cikin jihohin da ke haɗa kudu maso gabas da sauran sassan ƙasar.
Saboda haka mutane da yawa na sa ido sosai kan abin da ke faruwa a jihar.
Hukumar INEC ta amince da 'yan takara 16 da suka haɗa da mata 2 da maza 14 da za su fafata a zaben, ciki har da gwamnan jihar, Chukwuma Soludo, wanda ke neman mulkin jihar karo na biyu.
Wasu daga cikin 'yan takarar sun tsaya takara a zaɓen da ya gabata, kuma suna fatan a wannan karon za su yi nasara.