Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko kudu maso gabashin Najeriya 'zai jingine batun shugabancin ƙasa' a zaɓen 2027?
Kalaman Ministan Ayyuka na Najeriya, David Umahi na ci gaba da yamutsa hazo a fagen siyasar Najeriya.
A farkon makon nan ne ministan ya yi kira ga al'ummar yankinsa na kudu maso gabashin Najeriya cewa su haƙura da takarar shugabancin ƙasar a 2027, su kuma mara wa Shugaba Tinubu na APC baya.
Al'ummar kudu maso gabashin Najeriya dai sun jima suna hanƙoron samun shugaban ƙasa, bayan ƙorafin da suka jima suna yi na mayar da su saniyar ware a fagen siyasar ƙasar.
Kalaman nasa sun janyo zazzafan martani daga jam'iyyun hamayya daban-daban na ƙasar.
Kodayake wasu ba su ga baiken kalaman nasa ba kasancewarsa minista a ƙunshin gwambatin Tinubu.
Me David Umahi ya ce?
Yayin da yake jawabi ga manema labarai ranar Laraba, Mista David Umahi ya maimaita kalaman nasa inda ya ce ya kamata al'ummar Igbo su jira lokacinsu.
"Abin da ya kamata yanzu shi ne al'ummar Igbo su goyi bayan wani yankin, idan suna so wani yankin ya goyi bayansu'', in Umah wanda ya fito daga yankin na kudu maso gabashin Najeriya.
"Al'ummar Igbo ba za su samu shugaban ƙasa ta hanyar ɓangaranci ko kalaman ƙiyayya ko rashin faɗin gaskiya ba. Abin da zan ce shi ne Shugaba Tinubu ya yi mana komai ta fuskar ayyukan raya ƙasa kuma babu wanda zai musanta haka'', in ministan na ayyuka.
Dangane da zargin wasu al'ummar yankin na nuna musu wariya a rabon muƙaman gwamnatin tarayya, ministan ya ce ai yankin ya samu cigaban da tai taɓa samu ba a baya.
"Kuna manta ayyukan ci gaba, kuna magana kan muƙamai. Tambayata a nan ita ce tsakanin muƙami da ayyukan ci gaba, wanne ne ya fi muhimmanci? Yana da kyau mutanenmu su zama wayayyu''.
"Kowa zai iya zama shugaban ƙasa idan lokacin al'ummar Igbo ya zo, muna da ƙwararrun mutanen da za su iya, masu basira, gaskiya da kuma riƙon amana,'' in ji shi.
Me kalaman nasa ke nufi?
Dakta Yakubu Haruna Ja'e na Jami'ar jihar Kaduna, kuma mai sharhi kan siyasar Najeriya ya ce kalaman na Minista tamkar daƙushe fatan tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar LP , Peter Obi ne.
Peter Obi ya kasance mutumin yankin na baya-bayan nan da ya samu ƙuri'un da ba a yi zato ba kuma ake ganin zai iya zama barazana ga Shugaba Tinubu a 2027.
Masanin ya ce su dama al'ummar Igbo da ke kansu ba a haɗe yake ba, musamman a fagen siyasar Najeriya.
''Idan ba mu manta ba a zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar APC a zaɓen 2023, duka ƴan takara daga yankin kudu maso gabas janyewa suka yi, maimakon kuma su janye wa wani daga cikinsu, sai suka riƙa janye wa Tinubu wanda ya fito daga wani yanki''.
A zaɓen fitar dai gwanin dai an fafata ne tsakanin Tinubu da Osinbajo da suka fito daga kudu maso yamma, sai Rotimi Amaechi daga kudu maso kudu da Ahmed Lawan daga arewacin Najeriya.
Masanin ya ƙara da cewa babu wanda aka shiga zaɓen fitar da gwani da shi a APC daga yankin kudu maso gabashi, duk kuwa da yawan ƴan takarar da suka nuna shawa'ar, ciki har da David Umahi
To sai dai Bashir Yahatu Jentile mai sharhi kan al'amaran yau da kullum a Najeriya na da saɓanin ra'ayi, domin shi a ganinsa al'ummar Igbo mutane ne da kansu ke haɗe, wadanda kuma ke karɓar umarni daga sarakunan gargajiyarsu.
''Misali a 2023 ai Peter Obi ba shi da tasirin da zai iya samun adadin ƙuri'un da ya samu, amma saboda sarakunansu da jagororinsu sun ce su yi shi sai da ya samu ƙuri'un da babu wanda ya yi zato'', in ji shi.
Ya bayar da misalin yadda Peter Obi ya kayar da mataimakin Atiku Okowa a Delta, saboda yawan al'ummar Igbo a jihar.
Mene ne zai yi tasiri a zaɓen 2027?
Bashir Jentile na ganin zaɓen 2027 da ke tafe babban abin da zai yi tasiri shi ne addini da ƙalibalanci.
Idan ka duba tarihi a fagen siyasa al'ummar Igbo a kodayaushe sun fi ƙulla ƙawance da Hausawa a yankin arewacin ƙasar.
''Don haka idan al'ummar Igbo suna son samun nasara a siyasarsu, sai sun ƙoma sun ƙulla ƙawance da ƴan arewa'', in ji shi.
''Kuma ko mataimakin Peter ya yarda zai yi wa Atiku ina mai tabbatar ma al'ummar Igbo za su zaɓe su''.
Ya ce idan aka duba tarihin siyasar Najeriya tun daga 1999 zuwa 2019 al'ummar Igbo da ke yankin kudu maso gabashin Najeriya PDP suke zaɓe.
''Amma saboda ƙabilanci a 2023 sai dukkansu suka juya suka zaɓi Peter Obi saboda shi ne ɗan ƙabilarsu kuma ɗan yankinsu'', in ji shi.
Saboda haka ne Jentile ke ganin cewa zaɓen 2027 zaɓe ne da ƙabilanci da addini zai taka muhimmiyar rawa.
"A 2027 idan Peter Obi ya tsaya takara, Tinubu ya tsaya takara a APC, Atiku ya tsaya a ADC sannan Jonathan kamar yadda ake yayatawa ya tsaya a PDP, to nan za ka ga tsantsar ƙabilanci, domin kowane yanki nasu za su zaɓa'', in ji shi.
Wane tasiri ƙuri'un kudu maso gabas ke yi?
Yankin Kudu maso gabashin Najeriya ya ƙunshi jihohi biyar da suka haɗa da Enugu da Imo da Anambra da Ebonyi da kuma Abia, waɗanda kuma dukkansu ba su da yawan al'umma idan aka kwatanta da sauran yankunan ƙasar.
Kan haka ne Dakta Yakubu Haruna Ja'e ke ganin yankin ba shi da wani tasiri a nasarar zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya.
''Idan ka duba za ka ga ƴan siyasa ba su fiya mayar da hankalinsu yankin ba, saboda ba su yawan da za su iya kai ɗan takara ga nasara''.
''Dukkansu idan ka haɗa su ba su kai al'ummar Kano da Kaduna ba, to ka ga duka sauran yankunan sun zarta su yawan al'umma, shi ya sa ɗan siyasa suka fi mayar da hankali wasu yankunan'', in ji shi.
Alƙaluman da Jaridar The Cable ta fitar a zaɓen 2023, sun nuna cewa kashi 5.8 cikin 100 kawai Tinubu ya samu a ƙuri'un da aka kaɗa a yankin kudu maso gabashin ƙasar.
Haka ma a lokacin Buhari alƙaluman na The Cable sun nuna cewa a 2015 ya samu 403,000 daga ƙuri'a fiye da miiyan 1.7 da aka kaɗa a yankin.
Inda a 2019 kuwa ya samu ƙuri'a kimanin 198,000 cikin ƙuri'u kusan miliyan 2.6 da aka kaɗa a yankin, kamar yadda alƙaluman na The Cable suka nuna.