Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƴansiyasar Najeriya shida da suka tura mota ta baɗe su da ƙura
Babu wata gwamnatin siyasa da ke tabbata ba tare da goyon bayan wasu makusantan ɗantakara ba, amma a wasu lokutan akan ci kuma a cinye gwamnatin ba tare da su ba bayan hawa mulki.
Wannan shi ne abin da 'yansiyasa a Najeriya ke kira sun tura mota ta tashi amma ta baɗe su da hayaƙi.
An sha ganin 'yansiyasa cikin irin wannan yanayi tun bayan fara mulkin dimokuradiyya a ƙasar da ke yammacin Afirka a 1960.
Sai dai yayin da wasu daga cikinsu kan sauya jam'iyya bayan ɓatawa da abokan siyasar tasu, wasu kan ci gaba da zama har zuwa lokacin da za su samu sakayya daga wata gwamnatin daban.
Siyasar Najeriya ta dogara ne kusan kacokam kan ubangida, kuma a lokuta da dama akan samu matsala da zarar yaro ya gaji ubangidansa.
Wannan maƙala ta duba wasu daga cikin irin waɗannan 'yansiyasa da suka yi wa wani mai mulki hidima kuma ba su shiga gwamnatin ba.
Buba Galadima
An daɗe ana damawa da Buba Galadima a harkokin siyasar Najeriya tun daga shekarar 1978, kamar yadda ya shaida wa BBC a cikin wata hira.
A duka shekarun da ya yi, an fi saninsa da goyon bayan tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya ce sun fara mu'amalar siyasa tun 2002.
Buba ya goyi bayan Buhari lokacin da ya fara takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar APP a 2003, sannan ya sake yi a 2007 bayan ta koma ANPP.
Bugu da ƙari, Buba na cikin mutanen da suka kafa jam'iyyar Congress for Progressive Change (CPC), wadda marigayi Buhari ya yi wa takarar shugaban ƙasa a 2011, har ma ya zama sakatarenta na ƙasa.
Buhari ya zama shugaban ƙasa a 2015 bayan jam'iyyarsu ta CPC ta dunƙule wajen kafa haɗakar APC, kuma a wannan lokacin ma Buba na cikin 'yan kwamatin amintattu na jam'iyyar.
Sai dai babu daɗewa da hawa mulki aka fara takun saƙa tsakanin Buba da gwamnatin ta Buhari, abin da ya kai shi ga yin zazzafar adawa da Buhari da ma jam'iyyarsu tasu ta APC a 2019, har ma ya bar ta zuwa NNPP a 2023.
Har Buhari ya kammala wa'adi biyu na shekara takwas bai taɓa bai wa Buba Galadima wani muƙami a gwamnatinsa ba.
"Buhari na ɗaya daga cikin mutanen da nake ganin girmansu a ido na.
Nasir El-Rufai
Tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya fara siyasa ne tun daga shekarun 2000, lokacin da tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya ba shi muƙamin ministan birnin Abuja.
Kazalika, yana cikin mutanen da suka kafa jam'iyyar tsohuwar jam'iyyar CPC, da kuma APC ta haɗaka mai mulkin Najeriya a yanzu.
Alaƙarsa da Shugaban Najeriya Bola Tinubu ta ƙullu ne bayan fara yaƙin neman zaɓe na 2023, inda tsohon gwamnan ya tsaya kai da fata wajen nema wa abokin siyasar tasa ƙuri'un 'yan jiharsa ta Kaduna da ma na arewacin Najeriya.
El-Rufai na ɗaya daga cikin gwamnonin Najeriya da suka kai gwamnatin tarayya ƙarƙashin Muhammadu Buhari ƙara kotu saboda sauya takardun kuɗi na naira da ta yi ana dab da gudanar da babban zaɓe na 2023.
Gwamnonin sun zargi gwamnatinsu ta APC cewa matakin sauya kuɗin, wanda ya jawo wahalhalu mas tsanani saboda ƙarancin tsabar kuɗi, zai shafi farin jinin ɗantakararsu Bola Tinubu a zaɓen.
Yayin wata hira da BBC, El-Rufai ya taɓa cewa "a matsayinmu na gwamnonin arewa za mu yi iyakar ƙoƙari wajen ganin mulkin Najeriya ya koma kudu", yana mai nufin hannun Bola Tinubu.
Alaƙar Tinubu da El-Rufai ta lalace ne bayan shugaban ya gaza bai wa tsohon gwamnan muƙamin minista, inda majalisar tarayya ta ƙi tantance shi saboda wani rahoton da ta ce jami'an tsaro sun gabatar a kan sa.
Jim kaɗan bayan haka El-Rufai ya fara adawa da APC da gwamnatin Tinubu, inda a watan Maris na 2025 ya sanar da ficewarsa zuwa jam'iyyar PRP, kuma a yanzu yake cikin gaba-gaba wajen ƙulla haɗakar 'yan'adawa a ADC.
Sanata Rufa'i Sani Hanga
Rufai Sani Hanga sananne ne wajen taimaka wa tafiyar marigayi Muhammadu Buhari tun daga shekarun 2003 a jam'iyyar APP, kuma yana cikin 'yansiyasar da ba su shiga gwamnatin marigayin ba.
Bayan Buhari ya yi takara sau biyu ba tare da samun nasara ba a APP da ANPP, Sanata Hanga na cikin jiga-jigan da suka kafa jam'iyyar CPC kafin zaɓen 2011.
Bayanai sun nuna cewa jam'iyyar ta yi amfani da gidansa da ke birnin Abuja a matsayin hedikwatarta ta ƙasa, har ma ya riƙe matsayin shugabanta na riƙon ƙwarya.
"Ya yi hakan ne saboda amincewa da aƙidar Buhari ta nuna gaskiya a lokacin," kamar yadda Malam Kabiru Sufi, masanin kimiyyar siyasa, ya shaida wa BBC.
Rufai Hanga ya shafe tsawon shekara na takwas na mulkin Buhari a matsayin ɗan'adawa, kafin ya koma jam'iyyar NNPP kuma ya ci kujerar sanatan Kano ta Tsakiya a majalisar dattawa a zaɓen 2023.
Hakeem Baba-Ahmed
Hakeem Baba-Ahmed ya kasance cikin na kusa da tsohon shugaban Najeriya marigayi Muhammadu Buhari.
Baya ga rawar da ya taka wajen renon jam'iyyar APC a jihar Kaduna, daɗin-daɗawa, Hakeem shi ne wakilin Muhammadu Buhari da jam'iyyar APC a zauren sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na shekara ta 2015.
A lokacin da Muhammadu Buhari ya karɓi shugabanci an riƙa ambato Hakeem a cikin wadanda ake ganin za su iya samun muƙamai masu tsoka, musamman kasancewar shi mutum mai matuƙar gogewa a harkar gwamnati.
Yana cikin mutanen da suka gana da Muhammadu Buhari a lokacin da ake rabon mukamai, wani abu da ya ƙara ingiza raɗe-raɗin samun muƙami a gwamnatin.
Sai dai abin mamaki shi ne a tsawon shekara takwas na mulkin Buhari babu wani muƙami da tsohon mai magana da yawun ƙungiyar dattijan ta Arewa ya samu, in ban da muƙamin mai bai wa shugaban Majalisar Dattijai, Bokula Saraki shawara.
Daga ƙarshe ma ɓaɓewa tsakanin Hakeem da Buhari ta ƙara fitowa fili ne lokacin da Hakeem ya riƙa sukar gwamnatin Buhari, tare da bayyana mulkin Buhari a matsayin abin kunya.
Sule Yahaya Hamma
Sule Yahaya Hamma na cikin na hannun daman marigayi Shugaba Buhari kuma ɗaya daga cikin iyayen tsohuwar jam'iyyar CPC.
Sai dai ba kamar sauran 'yansiyasar da muka ambata a baya ba, ba a cika jin Hamma yana sukar tsohon shugaban ba a duka tsawon mulkisa duk da cewa ba a yi gwamnatin da shi ba.
Yana ɗaya daga mutanen da suka fara shaida wa BBC labarin kafa CPC a watan Fabrairun 2010 bayan ficewarsu daga jam'iyyar ANPP.
Kazalika, ya riƙe muƙamin daraktan kamfe na Muhammadu Buhari a jam'iyyar APC gabanin zaɓen 2015.
Babu tabbas ko Sule Hamma ya taɓa tsayawa takara, amma dai ya riƙe muƙamai ciki har da na sakataren gwamnatin jihar Kano, kuma har Buhari ya kammala wa'adin sekara takwas Hamma bai shiga gwamnatin ba.
Musa Musawa
Marigayi Musa Musawa ɗaya da ne daga cikin 'yansiyasar arewacin Najeriya da suka bayar da gudummawar kafa gwamnatin Olusegun Obasanjo ta jam'iyyar PDP a 1999.
Tsohon ma'aikacin BBC Hausa, Musawa ya taka rawa sosai a zaɓen da shi ne farko a Jamhuriya ta Uku, kuma kamar saura shi ma ba a ci gwamnatin da shi ba tsawon shekara takwas da Obasanjo ya yi a kan mulki.
Ta yaya za a magance matsalar?
Masanin kimiyyar siyasa Kabiru Sufi ya ce daga cikin dalilan da ke jawo irin wannan matsala irin ta siyasa akwai ƙyashi tsakanin abokan tafiya.
Haka nan, masanin ya ce bambancin aƙida ma kan jawo ɓatawa tsakanin 'yansiyasar.
Sai dai ya ce ba lallai ne 'yansiyasar su gyara da kansu ba sai sun ji matsi.
"Ɗaya daga cikin hanyoyin shi ne sai sun ga jama'a na saka musu ido suna bibiyar abin da suke aikatawa," a cewarsa. "Kuma ɗaya daga cikin yadda za su gane hakan sai da rahotonni irin naku na 'yanjarida."