Abu tara da kwamitin bincike ya gano kan kwamishinan Kano

Lokacin karatu: Minti 3

Kwamishinan sufurin jihar Kano da ke arewa maso gabashin Najeriya ya ajiye muƙaminsa kan zargin alaƙarsa da mutumin da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a jihar.

Gwamnatin jihar Kano ce ta sanar da murabus ɗinsa a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Laraba.

Ibrahim Ali Namadi ya ajiye muƙaminsa na kwamishina ne bayan gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamitin binciken zargin sa da hannu a belin Sulaiman Aminu Danwawu, wanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a jihar.

Batun belin Danwawu da ake zargin da hannun kwamishinan, ya ja hankalin jama'ar Kano da ma Najeriya.

Kwamishinan ya ce ya yanke shawarar yin murabus ne saboda buƙatar al'umma da kuma tasirin al'amarin.

"A matsayin mamba na wannan gwamnati wanda ke kan gaba wajen yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, mataki ne da ya dace na ɗauka," a cewar sanarwar.

Sai dai a sanarwar, Kwamishinan ya ci gaba da kare kansa a matsayin marar laifi tare da nisanta kan shi da zargin da ake masa.

"Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus ɗin kwamishinan, tare da yi masa fatan alheri," kamar yadda Sunusi Bature Dawakin Tofa ya shaida wa BBC.

Ya kuma ce gwamnatin Kano ta bayyana matakin kwamishinan a matsayin wani muhimmin cigaba a ƙoƙarin gwamnati wajen tabbatar da gaskiya da kuma riƙo da amanar al'umma.

A ranar Litinin ne kwamitin binciken badaƙalar belin Danwawu, ƙarƙashin jagorancin Barrister Aminu Hussaini ya miƙa rahoton bincikensa ga sakataren gwamnatin jihar.

Abu 9 da kwamitin ya gano

  • Kwamishinan ya amince da ya tsayawa mai lefin domin raɗn kansa a ranar 18 ga watan Yulin 2025.
  • Rantsuwa: Kwamishinan ya yi rantsuwa kan belin a matsayinsa na kwamishina mai ci kuma ya yi alƙawarin cika dukkan sharuɗɗan beli har zuwa ƙarshen shari'ar.
  • Kwamishinan ya fahimci cewa kwamishina kuma ɗn majalisar zartarwa na jiha ne kawai zai iya tsaya wa wani a harkar shari'ar bisa tanade-tanaden sharuɗɗan kotu.
  • Kwamishinan bai yi takatsantsan ba: Kwamishinan bai yi takatsantsan ba kafin ya ɗauki wannan matsaya ta tsaya wa wani da ake zargi da laifi da ke fuskantar babbar tuhuma da ta jiɓanci safarar ƙwaya.
  • Kwamishinan yana da cikakkiyar masaniyar haƙiƙanin girman tuhumar da ake yi wa mutumin da ta jiɓanci safarar ƙwaya.
  • ‎Kwamishinan ya saɓa dokokin gwamnatin Kano dangane da matsayarta da ke fili ta ƙyamar safarar ƙwaya da ta'ammali da ƙwayar da ɓata matasa da sauran laifuka da suka jiɓance su.
  • ‎Babu shaidar da ke nuna kwamishinan na da wata alaƙa da wanda ake tuhumar kafin yanzu.
  • ‎Kwamitin bai samu wata shaidar da ke nuna yin amfani da kuɗi ko wata kadara ba domin jan hankalin kwamishinan kafin ya aikata belin.
  • Kwamishinan bai ajiye ko kwabo ba na beli ciki kuwa har da naira 5,000,000 da ake magana akai. Wannan kawai yana ƙunshe ne a cikin takardar rantsuwar da wanda ake tuhumar ya rubuta.

Zargin Namadi da ƙarbar belin Danwawu, mutumin da ake zargi da dillancin miyagun ƙwayoyi, ya janyo zazzafar muhawara a Kano da Najeriya inda wasu ke ganin bai kamata mutum mai matsayi irin na kwamishina ya karɓi belin mutumin da ake zargi da taimaka wa masu ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a jihar ba.

Lamarin da ya sa wasu al'ummar jihar ke ta kiran lalle sai gwamnati ta ɗauki mataki a kan kwamishinan.

Sai dai gwamnatin ba ta bayyana ko matakin da za ta ɗauka ba zai shafi Ibrahim Ali Namadi bayan ajiye muƙaminsa na kwamishinan sufurin jihar Kano.