Man United za ta hana Mainoo tafiya, Roma na harin Zirkzee

Lokacin karatu: Minti 1

Mai horar da ƴan Manchester United Ruben Amorim, zai toshe kafar ɗan wasan ta na tsakiya na barin Kobbie Mainoo daga barin ƙungiyar a watan Janairu yayin da shi kuma ya ke son komawa Napoli. (Metro)

Chelsea da Bayern Munich na harin ɗaukar ɗan wasan Man United din dai Mainoo. (Caught Offside)

Roma na harin ɗan wasan Manchester United mai shekaru 24, Joshua Zirkzee a watan Janairu. (Gazzetta - in Italian)

Tottenham za ta jira zuwa kakar wassani na gaba, don ɗauko ɗan wasan Brighton mai shekaru 25, Jan Paul van Hecke. (Football Insider)

Spurs za su siyar da ɗan wasan su, mai shekaru 24 Brennan Johnson, duk da ɗukar sa da Crystal Palace ke son yi. (Teamtalk)

Barcelona sun yi sanyi wajen siyen ɗan wasan Serbia Dusan Vlahovic mai shekaru 25, yayin da ake sa ran zai koma AC Milan daga Juventus. (Sport - in Spanish)

Real Madrid da Paris St-Germain na harin dan wasan Bayern Munich Dayot Upamecano, sai dai Bayern Munich ɗin sun ce suna son sake tattunawa da ɗan wasan wajen sabunta kwantaraginsa. (Bild - in German)

Tottenham,da Aston Villa da West Ham na son ɗaukar ɗan wasan Brentford mai shekaru 24 Igor Thiago. (Caught Offside)

Tottenham za ta maye gurbin mai horar da ƙungiyar da tsohon kocin Barcelona Xavi. (Fichajes - in Spanish)

Manchester United za su ɗauko ɗan wasan Uruguay Manuel Ugarte mai shekaru 24 a watan Janairu. (Football Insider)

AC Milan sun kamala shirin daukar ɗan wasan West Ham mai shekaru 32, Niclas Fullkrug. a watan Janairu. (Calcio Mercato)