Wace ƙungiya ce za ta iya ja da Liverpool a kaka mai zuwa?

Liverpool celebrate with Premier League trophy

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Karo na ƙarshe da Liverpool ta kare kambinta na Premier League shi ne 1984
    • Marubuci, Emlyn Begley
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
  • Lokacin karatu: Minti 5

Liverpool za ta samu ƙwarin gwiwar kare kambin gasar Premier League da ta ɗauka a bara bayan kashe kuɗaɗe mafiya yawa a tarihinta wajen cefano 'yanwasa da yawa a bana.

A kakarsa ta farko bayan maye gurbin Jurgen Klopp, mai horarwa Arne Slot ya ci wa Liverpool kofin gasar duk da sauran wasa huɗu a kammala kakar, inda ya bayar da tazarar maki 10.

Tawagar ta Slot zuwa yanzu ta kashe fan miliyan 269 - ciki har da fan miliyan 100 wajen ɗaukar Florian Wirtz daga Bayer Leverkusen - kuma zai iya ƙaruwa zuwa miliyan 116.

Ɗanwasan gaba Eintracht Frankfurt daga Frankfurt (fan miliyan 69), da ɗnwasan baya Milos Kerkez daga Bournemouth (fan miliyan 40), da ɗanwasan baya Jeremie Frimpong (fan miliyan 29.5) su ne sauran manyan 'yanwasan da suka ɗauka.

Akwiai kuma golan Valencia Giorgi Mamardashvili da ta saya kan fan miliyan 25 a shekarar da ta gabata.

Amma abokan hamayya ma sun kashe kuɗi.

Mun duba yadda manyan ƙungiyoyi biyar suka kashe kuɗi a wannan bazarar domin ganin ko za su iya ja da Liverpool.

Arsenal

Viktor Gyokeres

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Arsenal za ta yi fatan ɗanwasan gaba Viktor Gyokeres zai bayar da mamaki a kakar nan

'Yanwasan da ta saya: Viktor Gyokeres (Sporting), Martin Zubimendi (Real Sociedad), Noni Madueke, Kepa Arrizabalaga (Chelsea), Christian Norgaard (Brentford), Cristhian Mosquera (Valencia)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

'Yanwasan da ta sayar: Kieran Tierney, Jorginho, Thomas Partey, Takehiro Tomiyasu (duka sallamarsu ta yi)

Kuɗin da ta kashe: fan miliyan201

Wannan kakar tana da matuƙar muhimmanci ga Arsenal kuma kowa na ganin hakan a kulob ɗin. Kociya, magoya baya, ma'aikata duka na ji a jikinsu sun kai wani sabon matsayi.

Rabon da su ci wani kofi tun a 2020.

Zuwa yanzu Gunners sun kashe sama da fan miliyan 190 domin ƙarfafa tawagar, daga ciki kuma har da isar ɗanwasan gaba da aka daɗe ana jira Victor Gyokeres daga Sporting Lisbon.

Mikel Arteta ya yi ƙoƙari sosai wajen sauya Arsenal zuwa masu nuna ƙalubale da kuma samun gurbin Champions League akai-akai, amma yanzu lokaci ya yi da za su tsallaka wani matakin.

Za su sha matsi a wannan karon bayan sun kusa yin nasarar ɗaukar kofi a kakar wasanni da dama.

An ga yadda Arteta ya sauya salon wasa a Arsenal. A kwanan sukan kai ƙwallo ragar abokan hamayya da sauri domin bai wa Gyokeres damar zira ƙwallo.

Duk da cewa hakan zai ɗauki lokaci, amma indai salon ya yi nasara to tabbas wannan karon ma za su je gab ko kuma su ɗauki kofi.

Manchester City

Manchester City

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Manchester City ta sha kashi a zagayen 'yan 16 na gasar Club World Cup a hannun Al-Hilal

'Yanwasan da ta ɗauka: Tijjani Reijnders (AC Milan), Rayan Cherki (Lyon), Rayan Ait-Nouri (Wolves), James Trafford (Burnley), Sverre Nypan (Rosenborg)

'Yanwasan da ta sayar: Kevin de Bruyne, Kyle Walker (Burnley)

Kuɗin da ta kashe: fan miliyan 154

Manchester City za ta fito da fushi bayan gama kakar bara cikin rauni kuma ba tare da cin wani kofin kirki ba, ciki har da ficewa daga gasar Club World Cup.

Mai horarwa Pep Guardiola ya ƙarfafa tawagar da sababbin 'yanwasa biyar kamar ɗanwasan tsakiya Tijjani Reijnders daga AC Milan.

Kafin yanzu, karo na ƙarshe da City ta ƙare a mataki na uku a gasar Premier shi ne 2017, saboda haka akwai yiwuwar lokaci ne kawai zai fayyace yadda za ta farfaɗo daga rashin ƙoƙarin a wannan karon.

Zakarun gasar Liverpool da Arsenal na biyu a tabeuri, ana ganin kamar su ne kan gaba a neman ɗaukar kofin a wannan karon ba City ba.

Chelsea

Chelsea

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Chelsea ce ta ci kofin gas kakar nan

'Yanwasan da ta ɗauka: Liam Delap (Ipswich), Joao Pedro (Brighton), Jamie Gittens (Borussia Dortmund), Jorrel Hato (Ajax),

Cinikin da aka yi a baya kuma ya faɗa a bana: Dario Essugo (Sporting), Estevao Willian (Palmeiras)

'Yanwasan da ta sayar: Kepa Arrizabalaga (Arsenal), Joao Felix (Al-Nassr), Djordje Petrovic (Bournemouth), Mathis Amougou (Strasbourg)

Kuɗin da ta kashe: fan miliyan249

Nasarar da Chelsea ta samu 3-0 a wasan ƙarshe na gasar Club World Cup kan Paris St-Germain wata sanarwa ce cewa su ma fa sun kawo ƙarfi.

Mai horarwa Enzo Maresca ya haɗa kan rukunin 'yanwasa da suka kai darajar fan biliyan 1.4, a cewar kulob ɗin, kuma duk da cewa tawagar tasa ce mafi ƙanƙantar shekaru a tarihin Premier League, za su iya lashe gasanni.

Daga cikin manyan 'yanwasansu akwai Cole Palmer, Enzo Fernandez, Moises Caicedo da Marc Cucurella. Yanzu kuma sun ƙara da Joao Pedro, Liam Delap, Jamie Gittens, Estevao Willian, da Jorrel Hato domin rage wa kan su gajiyar buga wasanni a gasar Champions League.

Haka nan, Chelesea na hanƙoron kammala Premier a cikin 'yan huɗun farko, amma kuma ɗanwasan baya Lvi Colwill na cikin waɗanda ke nuna cewa za su iya lashe gasar ko ma Champions League a kaka mai zuwa.

Newcastle

Anthony Elanga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Anthony Elanga (dama) ya ci wa Newcastle ƙwallo a wasan sada zumunta da Arsenal

'Yanwasan da ta saya: Anthony Elanga (Nottingham Forest), Aaron Ramsdale (Southampton, aro)

'Yanwasan da ta sayar: Sean Longstaff (Leeds)

Cinikin da aka ƙulla a baya kuma ya faɗa a yanzu: Lloyd Kelly (Juventus)

Kuɗin da ta kashe: fan miliyan55

Newcastle ta kammala kakar wasan a mataki na biyar, amma kulob ɗin na da ƙwarin gwiwa bayan samun gurbi a gasar zakarun Turai ta Champions League, da kuma lashe kofi.

Sai dai wannan kaɗai ba zai zama alamar kaka mai albarka ba gare su.

Ta gaza ɗaukar 'yanwasa da yawa da so ɗauka. Cikinsu akwai Hugo Ekitike, Joao Pedro, James Trafford, Liam Delap da Dean Huijsen.

Har yanzu ba a daddale ba kan makomar Alexander Isak, kuma akwai ɗan rashin jituwa bayan daraktan wasanni Paul Mitchell ya bar ƙungiyar.

Ha yanzu Newcastle na da tawagar da za ta iya karawa da manyan ƙungiyoyi kamar yadda suka nuna a wasan ƙarshe na gasar Carabao da Liverpool. Amma kuma wnnan tawagar na buƙatar sabbin jini.