Manyan mu'ujizojin Yesu Almasihu guda huɗu

Asalin hoton, Getty Images
Ana gudanar da bikin Kirsimeti ne domin tunawa da ranar haihuwar Yesu Almasihu.
Mabiya addinin Kirista a ko ina a fadin duniya na bayyana muhimmancin abubuwan al'ajabi da mu'ujizojin Yesu Isa Almasihu, wadanda malaman addinin Kirista suke jaddadawa ga mabiyansu a koda yaushe a cikin wa'azi.
Sun kuma yi amanna cewa wadannan mu'ujizoji wata babbar garkuwa ce a rayuwarsu, muddin ba su saba wa abubuwan koyin da ya zo musu da su ba.
Rabaran Joseph John Hayab, shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen jihar Kaduna, ya bayyana wa BBC cewa Yesu Isa Almasihu ya zo duniya da abubuwa na ban al'ajabi da kuma abubuwan koyi ga al'ummar duniya.
Rabaran Hayab ya kara da cewa kasancewarsa mai ceton al'umma a duniya wannan ma wani babban abin al'ajabi ne a cikin mu'ujizojinsa da suke alfahari da ita.
"Haihuwar Yesu ta kawo mana ceto, haihuwar Yesu ta kawo mana haske, haihuwar Yesu ta sada mu da Allah," in ji Rabaran Hayab.
"Don haka a kullum idan mun yi maganar Kirsimeti muna ganin ikon Allah ne, kuma shi ne dalilin Kirsimeti.''
Haka shi ma Rabaran Garba Alex Shukau, limamin Cocin Katolika na Saint Loius da ke unguwar Bompai a birnin Kano, ya bayyana wa BBC cewa Yesu Almasihu ya zo duniya tare da abubuwa na al'ajabi da mu'ujizoji da dama, yana mai cewa "mu'ujizarsa ta farko ita ce kasancewarsa mai ceto" ga dan adam.
"Abu na biyu kuma shi ne Yesu Isa Almasihu ya zo duniya domin ya kawo mana salama a cikin zukatanmu, da cikin harkokinmu da juna da 'yan uwa da makwabta har ma da magabata,'' in ji Rabaran Garba.
Ga wasu manyan mu'ujuzozi na Yesu Almasihu guda huɗu:
Warkar da mara lafiya
Rabaran Hayab ya kuma kara da cewa "babban abin al'ajabi da Yesu Kiristi ya yi shi ne na warkar da marasa lafiya."
"Lokacin da ya zo duniya ya yi ta warkar da marasa lafiya a yayin da yake yawon wa'azi, marasa lafiya sun samu lafiya, wadanda ba sa gani sun dawo suna gani, wadanda ba sa iya tafiya sun samu iya tafiya," in ji Rabaran Garba Alex.
Tayar da matattu

Asalin hoton, Getty Images
Babbar mu'ujizar da Yesu Almasihu ya nuna wadda kafin lokacinsa ba a taɓa jin inda ta afku ba ita ce ta tayar da matattu zuwa rai.
Hikimar wa'azi
Wa'azi kan kawo zaman lafiya da salama a tsakanin al'umma na daya daga cikin mu'ujizojin Yesu Isa Almasihu, a cewar Rabaran Father Garba Alex, wanda yake kokarin wanzar da zaman lafiya da kaunar juna a tsakanin al'umma.
"Akwai mu'ujiza a tare da kalaman da yake yi lokacin wa'azinsa, ta yadda yakan ja hankulan mutane zuwa gare shi cikin hikima da nuna kamala, yana bayyana cewa fada da rashin jituwa duka ba zaman rayuwar duniya mai kyau ba ne,'' in ji shi.
Haske a lokacin zuwansa duniya
Har ila yau, Rabaran Father Garba Alex ya kuma bayyana cewa zuwan Yesu Isa Almasihu duniya da haske wani muhimmin al'amari ne.
A cewarsa "lokacin da ya zo duniya ya haska ta domin littafi mai tsarki ya bayyana mana cewa lokacin da ya zo ya haskaka duniya, da zukatan al'umma."
''Ya zo domin ya zauna tare da mu, ya zo ne domin ya kawo mana haske, haske wanda zai haskaka a cikin rayuwarmu da zukatanmu, da gidajenmu domin ya ba mu zaman salama da zaman ceto."











