Me ya sa kiristoci ke kiran ranar da aka gicciye Yesu ‘Good Friday’?

Wani mutum

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

''Good Friday'' ita ce ranar da mabiya addinin kirista ke tunawa da ranar da aka gicciye Yesu Almasihu.

To me ya sa ake kiran ta Juma’a mai kyau ko kuma Juma’a mai tsarki?

Littafin Injila ya ce an zane Yesu, aka tursasa masa daukar katakon da aka yi amfani da shi wajen gicciye shi, sannan aka kashe shi.

Babu wani abu mai kyau a cikin haka wanda zai sa a kira ranar a matsayin mai kyau, wato “good”.

Wani bayanin na cewa rana ce mai kyau kasancewar ta rana mai tsarki. Wasu kuma na cewa an baddala kalmar “God’s Friday” ne zuwa “Good Friday”, wato daga ”Ranar Allah” zuwa “Rana mai kyawu”.

Sai dai babbar edita a wajen tsara kamusun turanci na Oxford English Dictionary, Fiona MacPherson, ta ce a al’adance Good Friday na nufin “wata rana ko lokaci da ake yin ayyuka na ibada”.

Kamusun harshen Ingilishi na Oxford ya ce “abu mai kyau a nan na nufin lokacin da masu zuwa coci ke ayyukan addininsu”, inda suke yi wa juna gaisuwar samun alkhairai, wato “good tide”.

Baya ga Good Friday, akwai kuma ranar ''Good Wednesday'' wadda ba a cika magana a kanta ba, wadda ita ma ke nufin Larabar da ke zuwa gabanin ranar Easter.

Hoton mabiya Addinin Kirista

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Lokaci na farko da aka san an fara amfani “goude friday” shi ne a wani littafi da ake kira ‘The South English Legendary“, wanda aka rubuta a wajajen shekarar 1290, kamar yadda kamusun ya nuna.

Shi kuwa littafin Baltimore Catechism - na mabiya Katolika a Amurka wanda ya samo asali daga shekarun 1885 zuwa 1960, ya ce ranar gicciye Yesu rana ce mai kyau kasancewar Yesu “ya bayyana matukar kaunarsa ga dan’adam tare da nemar masa dukkanin alhairai”.

Babban kamusun mabiya Katolika, wanda aka fara wallafawa a shekarar 1907 ya bayyana cewa babu tabbas kan asalin sunan ‘Good Friday.

Amma ya ce wasu majiyoyi sun ce sunan ya samo asali ne daga “God’s Friday” ko kuma ‘Gottes Freitag’, sai dai wasu sun tsaya kan cewa ya samo asali ne daga ‘Gute Freitag’ na harshen Jamusanci.

Ya kuma bayyana cewa mutanen Anglo-Saxons sukan kira ta da ‘Long Friday’ wato doguwar rana.

Har wa yau babban kamusun ya ce ana kuma kiran ranar “rana mai tsarki kuma kasaitacciyar Juma’a” a harshen Girka.

Akan kira ta da “Juma’a mai tsarki“ a harsunan Romance Languages. Akan kuma kira ta da Karfreitag (Ranar Alhini) a harshen Jamusanci.