Tambayoyi shida da ya kamata ku san amsarsu dangane da ranar Kirsimeti

Fafaroma Leo XIV a dandalin St Peters

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Yau ce ranar 25 ga watan Disamba da mabiya addinin Kirista a faɗin duniya ke bukukuwan murnar haihuwar Yesu Almasihu, wanda Kiristoci suka yi amannar cewa shi ne mai ceto.

A duk lokacin wannan biki, mabiya addinin na Kirista na shagulgulan murna da suka hada da abinci da sanya sabbin sutura da musayar kyautuka da kuma sada juna da salama.

Albarkacin wannan rana BBC ta zaƙulo wasu muhimman abubuwa dangane da ranar ta Kirsimeti.

Yaushe aka haifi Yesu Almasihu?

..

Asalin hoton, Getty Images

BBC ta nemi wannan amsar daga wurin fitaccen malamin addinin Kiristanci kuma Shugaban Ƙungiyar Kiristoci reshen jihar Kaduna, Joseph John Hayab.

"Ba a haifi Yesu Kiristi a ranar 25 ba. Wannan shi ne gaskiya. Ba a haife shi a watan Disamba ba, wannan shi ne gaskiya." kamar yadda ya shaida wa BBC a 2024.

Malaman addinin Kirista da dama dai sun yi amannar cewa babu wata tabbacciyar ranar da za a ce ita ce aka haifi Yesu Almasihu sai dai kawai a yi kintace.

A wane gari aka haifi Yesu?

Wannan ce cocin da ake kira Church of Nativity da ke Bethlehem a yankin Yamma da Kogin Jordan a Falasɗinu.

Asalin hoton, Getty Images

Dangane da haihuwar Yesu Almasihu, tarihi ya nuna cewa an haifi Yesu ne a garin Bethlehem wanda ke yankin Falasɗinawa a yau amma a lokacin tana ƙarƙashin daular Romawa.

Me ya sa ake Kirsimeti a Disamba?

..

Asalin hoton, Getty Images

"A ciki ƙarni na huɗu Rumawa da wasu Turawa su kan yi amfani da lokacin Disamba domin yin wasu bukukuwan da ba lallai na addinin Kirista ba. Sai aka duba aka ga abin da littafin babil ya faɗa dangane da lokacin da aka haifi Yesu, sai aka ga ya dace da wannan lokaci.

Sai suka ce tunda ana bukukuwa tare da bayar da kyautuka to me zai hana a yi bikin Kirsimeti a daidai wannan lokaci. Kuma a lokacin sai aka ringa yin bikin ranar 6 ga watan Disamba da kuma 6 ga watan Janairu.

Sai kawai aka ce to tunda duk lokacin iri ɗaya ne to me zai hana a mayar da shi bai ɗaya shi yasa aka mayar da ranar 25 ga watan Disamban kowace shekara," in Rabaran Joseph Hayab.

Wane ne ya fara bikin Kirsimeti?

..

Asalin hoton, Getty Images

Tarihi ya nuna cewa an fara bikin Kirsimeti a daular Roma a ƙarni na huɗu a shekarar 336 bayan rasuwar Yesu, a zamanin Sarki Constantine wanda ne ya ɗabbaƙa addini Kirista a matsayin addinin daular a hukumance.

Sai dai kuma Rabaran Joseph Hayab ya ce an ɗaukaka bikin Kirsimeti ne a 1931 lokacin da aka fara bikin a yadda yake a yau ɗin nan kamar yadda Kiristoci ke yin sa a faɗin duniya.

Mene ne muhimmancin Kirsimeti?

Fastor Dakta James Mobel Wuye ɗan ƙungiyar tuntuɓa tsakanin Musulmi da mabiya addinin Kirista ya shaida wa BBC cewa rana ce ta musamman.

" Asali idan Kirista na ƙwarai ne, ya tuna da mutuwar Isa Almasihu mai cetonsa, kuma a yi masa godiya. Wasu da dama na kuma tafiya ne domin ganin, 'yan uwansu, domin tattauna al'ummaran rayuwa da kuma yadda za su ci gaba".

"Ana kuma raye-raye da wake-wake da kuma cin abinci da yaɗa salama da kyautuka domin tuna wa da ranar."

"Muna kuma kira da mutane da su guji mugayen ayyuka a lokacin, domin lokaci ne na tuba da kuma ibada." In ji pasto Wuye.

Me ya sa wasu Kiristoci ba sa Kirsimeti?

..

Asalin hoton, Getty Images

Yayin da al'ummar Kirista suke gudanar da shagulgulan bukukuwan Kirsimeti a tsakiyar makon nan, wasu Kiristocin kan ƙaurace wa bukukuwan a kowace shekara.

Misali, ƴan ƙungiyar Jehovah Witnesses ba sa yin Kirsimeti saboda a cewarsu a littafi mai tsarki ba a ambaci lokacin da aka haifi yesu ba sannan kuma ba a ambaci Kirsimeti ba.

"Babu wasu tsofaffin littattafan tarihi da suka bayyana cewa an haife shi ranar 25 ga watan Disamba, duka ijma'i ne kawai la'akari da tsofaffin bukukuwan mutane da" in ji Sunday Bulus wani mabiyin Jehavah Witnesses.

Wannan shi ne babban dalilin da ya sa wasu Kiristoci ba sa bukukuwan Kirsimeti, saɓanin mabiya ɗariƙar Katolika da wasu daga dama cikin mabiya Protestants, da suka ɗauki ranar da muhimmanci a addininsu.