Me ya sa ake saka jar hula a lokacin bukukuwan Kirsimeti?

..

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

A lokutan bukukuwan Kirsimeti da mabiya addinin Kirista ke yi a faɗin duniya, kamar yadda ake ƙawata wurare da bishiyoyi masu lantarki haka ma za ka mutane na saka jar hula mai tulluwa da rastin fari a wuraren liyafa da taruka.

A wasu wurare kuma kamar manyan shaguna da ma'aikatu za ka ga an kakkafa hular a kusa da bishiyar lantarki ta Kirsimeti.

Ana dai kiran wannan hula da suna hular Santa.

Wannan ya saka jama'a da dama tambayar ko mene ne alaƙar wannan hula ja da Kirsimeti? Sannan wane ne shi Santa ɗin?

Wane ne Santa Claus?

..

Asalin hoton, Getty Images

Santa wani mutum ne da ya yi suna a al'adar Kiristocin Yammaci wanda aka ce yana kai wa jama'a kyautuka da yammacin jajiberin Kirsimeti.

Sai dai kuma wani kaulin ya nuna cewa Santa Claus ya kasance mutumin da ya shahara a tatsuniyoyin ƙarni na huɗu da ke kira da Waliyyi Nicholas wanda mutum ne mai son ƙananan yara sannan kuma ya sanu da irin kirkinsa da yawan kyautuka.

Ana dai yawan kamanta Santa da fitaccen mutumin nan da Turawan Ingila suke kira da Father Chrismas inda kuma a yanzu haka ake kallon dukkannin su a mutum ɗaya - Father Chrismas shi ne Santa Claus.

Halayyar da aka sani ta Santa ita ce mutum ne mai ƙiba mai farin gemu inda wani lokaci ke sanye da gilashi sannan sanye da jar hula mai tulluwa da ratsin fari da kuma jar kwat da wando da takalmin ruwa.

A koyaushe Santa na cikin farin ciki da nishadi ɗauke da jakaleda.

Father Chrismas, mutum ko tatsuniya?

Wani matashi ya yi shigar Father Chrismas yana ɗaukar hoto da waya.

Asalin hoton, Getty Images

Kamar yadda bayani yana gabata ana alaƙanta cewa Santa Claus ko kuma Saint Nicholas shi ne dai Father Chrismas, to sai dai wasu masana tarihi na ganin cewa tarihin Father Chrismas yana komawa ga ƙarni na 16, lokacin Sarkin Ingila Henry VIII.

Father Chrismas ya kasance, kamar yadda ake kwatanta shi, mutum ne shi mai fara'a da haba-haba a lokacin bikin Kirsimeti, inda yake sanya jama'a farin ciki tare da kai musu abinci da giya da sauran su.

To sai dai a wani ƙaulin kuma, masana tarihi na cewa Father Christmas ba wani mutum ba ne illa dai tatsuniyar da ke nuna sadar da salama da kyautuka da kuma farin ciki ga mutane a lokacin bukukuwan Kirsimeti.

Wani Kirista a ƙasar Pakistan yana murnar Kirsimeti a kan raƙumi.

Asalin hoton, Getty Images

Wannan dai na nuni da cewa Kiristoci da ma masu taya su murnar bukukuwan na sanya jar hular ta Santa Claus ne da manufar nuna farin ciki da nishaɗi da kuma sada jama'a da salama da ba su kyautuka.

Za a iya cewa a yanzu haka jar hula mai tulluwa ta Santa Claus ta zama wani alami na addinin Kiristanci musamman a lokutan bukukuwan Kirsimeti da ke nuni da kyautatawa da sada zumunci da kuma bayar da kyautuka.