Me ya janyo rabuwar Cocin Ingila da Fadar Fafaroma?

Asalin hoton, Getty Images
A wani lamari da ba a taba ganin irinsa ba a kusan karni biyar, Sarki Charles III da Fafaroma Leo, sun yi zaman addu'a tare a cikin cocin Sistine da ke fadar Fafaroma - Vatican.
An bayyana wannan haduwa a matsayin mai tarihin gaske, wajen neman sasanta bangarorin biyu da suka yi karni da dama a rabe.
Sarki Henry VIII na Ingila, shi ne ya raba Cocin Ingila daga Cocin Katolika.
To amma wane ne wannan sarkin? Kuma mene neya janyo rabuwar?
Farko da kuma mulkinsa
An haifi Sarki Henry VIII ranar 28, ga watan Yunin1491 a Greenwich kusa da London, kuma ya mutu ranar 28, ga watan Janairun 1547 a London, kamar yadda kundin tarihi na Birtaniya (Encyclopedia Britannica) ya nuna.
Ya mulki Ingila tsakanin 1509 da 1547, kuma ya kasance daya daga cikin manyan sarakunan Ingila, kasancewar ya yi mulki a farkon zamanin bunkasar Ingila da kuma lokacin sauye-sauye na addini, wanda ya sauya harkar addini a Turai.
Henry ya yi aure sau shida, kuma shi ne da na biyu na Sarki Henry VII, da kuma Elizabeth - 'yar Sarki Edward IV.
Lokacin da yayansa Arthur ya rasu a 1502, Henry ya zama yarima mai jiran gado.
Daga cikin dukkanin sarakuna Ingila na wannan zamani, shi kadai ne ya yi yarintarsa cikin zaman lafiya yayin da yake jiran zama sarki, abin da ya kara masa kwarjini.

Asalin hoton, Getty Images
Lokacin da Henry VIII ya hau sarauta a 1509, mutane na cike da buri na irin abubuwan da zai samar. Shekarunsa a lokacin 18, ga shi da kazar-kazar da kuzari a wasanni da farauta da kuma rawa.
Saboda wannan yanayi nasa ake ganin za a samu gagarumin sauyi daga salon mulkin mahaifinsa da ya gada, Henry VII.
Jim kadan bayan da ya hau sarauta, Henry ya auri Catherine ta Aragon, wato matar yayansa Arthur, wanda ya rasu.
Wannan aure ya karfafa alaka tsakanin Ingila da Sifaniya, kuma ya sa sarkin ya samu karbuwa a wajen Fafaroma Julius II.
Sai dai kuma bikin da aka yi na kasaita na wannan aure ya lakume yawancin dan takaitaccen arzikin da masarautar take da shi.
Henry da babban limamin Ingila
A wannan lokacin, babban limamin Ingila - Cardinal Thomas Wolsey ya kasance a matsayin dattijon kasa da ke cike da buri, wanda ya shirya harin soji na farko na Henry a Faransa.
Zuwa shekara ta 1515, Wolsey samu daukaka har ya kai ga zama babban abokin sarkin, da ke zaman kamar mai mulkin kasar.
Yayin da duniya ke kallon Wolsey a matsayin mai mulkin Ingila a zahiri, Henry ya kwana da sanin cewa har yanzu shi ne da mulki a hannunsa.
Daga baya Wolsey ya nemi mukamin Fafaroma, tare da goyon bayan Hery, wanda ya dauki samun wannan kujera ta Fafaroma a matsayin wata dama da za ta karfafa tasirin Ingila a kan Turai.
Sai dai burin nasa ya yi karo da yanayin siyasar da ake ciki a lokacin kuma hakan ya hana shi cimma wannan buri.

Asalin hoton, Getty Images
Manufofin Thomas Wolsey sun harzuka al'umma, inda duk yunkurin da ya yi na gyara abubuwan da suka gabata wadanda ba su yi wa jama'a dadi ba, ya kasa gamsar da talakawa, sannan kuma ya harzuka manyan kasa, al'amura suka kai kololuwar cabewa a tsakanin 1523 da 1524.
Bayan shekara daya, yunkurin da ya yi na sanya wani haraji na daban ya gamu da tirjiya sosai, abin da sa Henry ya hakura.
Sarkin ya dora alhakin rashin samun nasarar sanya wannan haraji a kan Wolsey, daga nan kuma kimar Limamin ta fara raguwa.
Nan da nan gagarumin buri da fatan da ake da shi na samun mulki da za a yaba da shi a kan Henry, suka dusashe saboda yanayin halin da kasar ke ciki a lokacin.
Sai dai duk da zaman dar-dar da ake ciki na siyasa a lokacin Henry ya ci gaba da kasancewa da kwarjininsa a matsayin sarki mai ilimi wanda ya kare Cocin Katolika.
Rikici da Rum
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Yayin da Sarki Henry VIII ya kai shekara arba'in al'amura suka fara sauya masa tsakanin rayuwarsa da kuma siyasa.
Bayan sama da shekara ashirin da aure, ya gamu da matsala da matsara, Catherine of Aragon, saboda ba ta haifi da namiji ba wanda zai gaji sarautar.
Duk wani kokari da ta yi na ganin ta haifar masa magaji ya gagara, inda ko dai ta yi bari ko kuma, ta haifi dan ba rai, inda suka kasance da 'ya mace kadai, Gimbiya Mary, wadda aka haifa a1516.
A zamanin ba abu ne da yake cikin tsari ba a ce mace ta yi gadon sarauta, saboda abin da hakan zai iya haifarwa na rikicin siyasa da gwagwarmayar kama mulki.
Kamar dai yadda ya saba Henry ba ya ganin wannan matsala daga wajenshi sai dai ta wajen matarsa.
Sarkin ya dora hakan inda ya danganta matsalar rashin samun da namijin da mutuwar wadanda take haifa a kan auren matar yayansa da ya yi,a don haka ya tilasta rabuwa da ita inda ya danganta hakan da saba wa addini.
A maimakon matarsa tasa Catherine sai ya auri jakadiyarta Anne Boleyn, bayan wajen shekara shida.
Wannan aure da ya yi ya tayar da kura tare da janyo juyin-juya-hali na addini, wanda ya sauya tarihi, kan neman saki daga matarsa, Catherine.

Asalin hoton, Getty Images
A karan kansa ya gamsu cewa aurensa na farko da Catherine ya saba wa doka bisa ayar littafin Leviticus na Baibul, wadda ta haramta mutum ya auri matar dan uwansa da ya rasu.
Henry ya tafi birnin Rum inda ya nemi Fafaroma Clement VII ya kashe aurensa.
A al'ada dole ne Fafaroma ya amsa bukatar sarakai a kan irin wadannan abubuwa, to amma Henry bai zje a lokacin da ya dace ba.
Catherine kanwar mahaifiyar Sarkin- sarakuna Charles V, shugaban daular Rum, kuma Fafaroma ya kasance fursunansa a tsakanin 1527 da 1528, wanda hakan ya sa ba zai iya yin hukuncin da zai bata wa abokinsa mafi karfi a Turai rai.
Sannan kuma Clement VII ba ya son ya ayyana takardar izinin da Fafaroma ya bayar da ta amince da auren Henry da Catherine ba.
A kan wadannan abubuwa Fafaroman ya zabi ya kare mutuncin kujerarsa maimakon ya dadada wa Sarkin na Ingila.
Wannan ne ya zama abu na farko da ya bude kofar rikicin da a karshe ya kai ga raba Cocin Ingila da Fadar Fafaroma (Cocin Katolika) da kuma samar da 'yancin cin gashin kai ga Cocin Ingila.
Mutuwa da gado

Sarki Henry na takwas ya mutu a ranar 28 ga watan Janairun 1547, a Fadar Whitehall yana da shekara 56, inda aka binne a kusa da matarsa Jane Seymour, wadda ta haifa masa magajinsa daya tilo.
Dansa Edward VI, ne ya gaje shi, inda ya ci gaba da gudanar da sauye-sauye a bangaren addini, kuma 'yarsa Mary, wadda 'yar Katolika ce ta dawo da wasu daga cikin dokoki da tsare-tsaren Fadar Katolika, kafin zuwa Elizabeth I, wadda ita kuma a karshe ta tabbatar da 'yancin kai na Ingila a bangaren addini da kuma siyasa.
Tarihin Sarki Henry na uku ya kasance sababin sauyin da aka samu wanda ya haifar da rabuwa a Cocin Katolika, da kuma samar da Cocin Ingila mai cin gashin kanta, inda ya kawo karshen zaman Ingila a karkashin Fadar Fafaroma - Vatican.
Wannan ne ya sa Sarkin Ingila ya zama shugaba na addini da kuma siyasa.










