Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matsalar ruwa a Kano: 'Yadda muke shan ruwa tare da dabbobinmu a rafi ɗaya'
- Marubuci, Abubakar Maccido
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Reporter
- Aiko rahoto daga, Kano
- Lokacin karatu: Minti 5
Dutsen Bakoshi wani ƙauye ne a ƙaramar hukumar Shanono da ke jihar Kano, arewacin Najeriya inda masu zama a cikinsa ke shan wahala sosai sanadiyyar rashin tsaftataccen ruwan sha da na amfani, musamman a lokacin rani.
Mafi yawan lokuta mutanen ƙauyen na samun ruwa ne daga ruwan sama da ya taru a ƙorama. Haka nan kafin su samu ruwan sai sun yi tafiya ta kimanin awa ɗaya.
Su na samun ruwan ne a wuri ɗaya da inda dabbobinsu ke shan ruwa.
Mazauna ƙauyen sun ce sun daɗe suna fama da wannan matsara ruwa, tun lokacin kaka da kakanni, fiye da shekara 50, duk kuwa da cewa sun koka wa gwamnati amma babu abin da ya faru.
Sun ce sun fi shiga cikin matsanancin yanayi ne a lokacin rani, inda a wasu lokuta mutane kan yi tafiya zuwa garin Shanono ko kuma Gwarzo duk domin neman ruwa.
A irin wannan lokacin wasu mutanen sai su kai tsawon mako ɗaya ba tare da sun yi wanka ba, kuma akan rufe makaranta saboda yara su taimaka wa iyayaensu wajen neman ruwa.
Wata mata da ke zaune a ƙauyen na Dutsen Bakoshi, Fa'iza Yakubu Adam ta shaida wa BBC cewa matsalar ruwan na zame musu babbar matsala, musamman a lokacin rani.
"Ba mu da ruwa mai tsafta ko kaɗan. Kowace rana sai mun taka sayyada domin ɗebo ruwa a rafi, kuma ruwan da muke samu a lokacin damina ba shi da tsafta," in ji ta.
Ta ce dole sai sun bi wasu matakai kafin su iya amfani da ruwan.
"Idan za mu yi amfani da ruwan dole sai mun tafasa shi ko kuma mu yi amfani da kyalle mu tace."
Fa'iza ta ce ana fama da matsalar ruwan tun kafin a haife su:
"Ana fama da wannan matsalar ruwan tun kafin a haife mu, musamman a lokacin rani, yanzu kuma da ake yin ruwa sai mun yi tafiya mai nisa ta tsawon sa'o'i kafin mu samu ruwan da za mu yi amfani da shi ko mu sha ko girki."
Ta ƙara da cewa matsalar ruwan na shafar ta a matsayin mace.
"A matsayin mace, wannan matsala tana ci min tuwo a ƙwarya. Ya kamata mace ta yi wanka sau biyu ko uku a rana, to amma wani lokaci zan zauna haka nan ba tare da na yi wanka ba."
Ta kuma ce makarantu da dama a yankin kan rufe a lokacin rani sanadiyyar ƙarancin ruwa.
"A lokacin rani makaranta na rufewa saboda yara su samu damar ɗebo wa iyayensu ruwa."
Hakimin yankin, Ibrahim Ahmad Dutse ya shaida wa BBC cewa sun daɗe suna fama da matsalar ruwa a yankin.
"Tun lokacin kakanninmu ake fama da wannan matsalar ruwa. Ana fama da wannan matsala tun kafin a haife ni."
Duk da cewa yanzu lokacin damina ne, ya bayyana cewa ruwan ba ya da kyau, kuma hakan na shafar lafiyarsu.
"Ruwan da muke sha, shi ne dabbobinmu ke sha, kuma hakan na haifar mana da lalurori. Wasu na kamuwa da amai da zawo, ko ƙuraje ko wasu cutukan da dama," in ji Ahmad.
Ya kuma bayyana cewa sun kai kokensu wurin gwamnati a lokaci daban-daban amma har yanzu ba a yi komai ba.
"Mun kai wa gwamnati kuka, amma babu abin da ya canza," in ji shi.
BBC ta tuntuɓi shugaban ƙaramar hukumar Shanono, Abubakar Barau Shanono wanda ya ce yana sane da matsalar ruwan ta Dutsen Bakoshi saboda ya taɓa zuwa ya duba da kansa.
Ya ce an yi nazari kan wasu madatsun ruwa shida da ke yankin domin ganin yadda za a iya samar wa al'umma tsaftataccen ruwan sha, ko da kuwa na rabin shekara ne.
"Mun rubuta wa gwamna wasiƙa game da madatsun ruwan, muna son gwamnati ta gyara su ta yadda al'umma za su samu tsaftataccen ruwa, ko da na rabin shekara ne domin rage matsalar ruwa da al'umma ke ciki."
Ya kuma ce sun samar da famfon burtsatse guda biyu a Dutsen Bakoshi tare da taimakon wasu ƙungiyoyi, wadanda a yanzu mutane ke amfani da su.
Ya ƙara da cewa ya rubuta takarda zuwa ga gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf yana roƙon shi ya taimaka a gina ƙarin famfunan burtsatse a ƙauyen tare da gyara wadanda suka lalace, kuma ya ce gwamnan ya amince.
A halin yanzu, a cewar shugaban ƙaramar hukumar, suna duba wuraren da ke cikin ƙangin rashin ruwa domin ganin yadda za su magance matsalar ta hanyar samar da burtsatse.
"A cikin Dutse, inda aka fi shan wahala, koda an gina rihiyar burtsatse ba a samun ruwa. Shi ya sa ba za mu iya cewa kawai za mu gina rijiyar ba, dole ne sai mun nemi inda za a samu ruwa, ko da kuwa zai zama a wajen ƙauyen ne."
Matsalar da ake fuskanta a yankin shi ne ba a samun ruwa a ƙasa idan an gina rijiyar burtsatse saboda dutse da ke ƙarkashin ƙasar.
Matsalar ruwa a Najeriya
Matsalar ruwa da ake fama da ita a Dutsen Bakoshi misali ne na yadda ake fama da matsalar ruwa a Najeriya, inda al'umma da dama ke rayuwa babu ruwa mai tsafta.
Asusun tallafa wa yara na Majalisar Dinkin Duniya, Unicef ya ce ruwa maras tsafta da rashin tsaftar muhalli a Najeriya na haifar da cutuka da ma kashe ƙananan yara fiye da 70,000 a kowace shekara.