Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da muka sani kan 'farmakin da aka kai fadar Sarkin Kano'
Fadar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ta fitar da sanarwa inda ta ce wasu ƴan daba waɗanda ta yi zargin masu goyon bayan sarkin Kano na 15 ne ssun kai hari a Gidan Rumfa da ke Ƙofar Kudu.
Bayanai sun ce ƴan daba ne ɗauke da makamai suka kutsa fadar bayan karya babbar ƙofar shiga gidan tare da jikkata jami'an tsaron da ke bai wa fadar tsaro da kuma lalata wasu motocin jami'an ƴansanda da ke ƙofar gidan.
An dai ce maharan sun kai harin ne a daidai lokacin da Aminu Ado ke wucewa ta fadar bayan ziyarar ta'aziyya a gidan marigayi Alhaji Aminu Ɗantata.
Ana kallon wannan lamari a matsayin ci gaba da takun-saƙa da ke tsakanin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.
Zaman ɗarɗar game da abubuwan da ke faruwa kan halin da ake ciki a masarautar Kano ya kai matuƙa ne tun bayan matakin da majalisar dokokin jihar Kano ta soke dokar da ta kawo Aminu Ado kan mulkin Sarkin Kano.
Me fadar Sarki Sanusi ta ce?
Sanarwar da Fadar Sarki Sanusi ta fitar, wadda ta samu sa hannun Saddam Yakasai, ɗaya daga cikin jam'ian yaɗa labarai na fadar, ta zargi Sarki Aminu Ado da hannu a harin da aka kai Gidan Rumfa.
Fadar ta ce "ƴan daban Aminu Ado ne suka kutsa cikin Gidan Rumfa bayan ɓalla ƙofa, suka kai wa masu tsaron gidan hari tare da jikkata wasu, sannan suka lalata abubuwa da dama ciki har da motocin jami'an tsaro da ke ajiye a fadar".
Sanarwar ta ƙara da cewa "da gangan Sarki Aminu ya bi ta wannan hanyar domin mutanensa su kai hari a fadar lokacin da yake komawa gida bayan yi wa iyalan Aminu Alhassan Dantata ta'aziya."
Ɓangaren Sarki Sanusi ya kuma ce ba wannan ne karon farko da Aminu Ado ke bin hanyar ba, "a baya ma ya taɓa bin hanyar domin ya razana mutanen unguwar".
Me ɓangaren Aminu Ado ya ce?
Ɓangaren Aminu Ado Bayero ya musanta zargin cewa yana da hannu cikin harin da aka kai a Gidan Rumfa, Fadar da Sarki Muhammadu Sanusi II ke da zama.
Makusancin Aminu Ado Bayero wato Aminu Babba Dan Agundi ya ce tabbas ba wannan ne karon farko da tawagar Aminun ke bi ta hanyar Gidan Rumfa ba - Fadar Sarki Sanusi - "sai dai babu wani abu da ya taɓa faruwa".
Aminu Dan Agundi ya ce "mun je ta'aziya gidan Alhaji Aminu Dantata, muka biyo ta cikin gari, za mu wuce ta ƙofar gidan sarki na gidan Rumfa, sun saka ƴan daba, muna wucewa suka fara jifa suka yo kan mutane.
"Mutanenmu da suka ga haka sai suka kora su, kuma akwai bidiyo, kowa zai iya gani," in ji Dan Agundi.
Makusancin na Sarki Aminu ya zargi fadar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da ƙoƙarin shafa masu kashin kaji ta hanyar zargin su da kai harin.
"Saboda haka wannan abu da suke faɗa ba gaskiya ba ne, su sun sani," kamar yadda Dan Agundi ya shaida wa BBC.
Mene ne asalin rikicin?
Masu lura da al'amuran yau da kullum na alaƙanta taƙaddamar masarautar ta Kano ne da neman nuna ƙwanjin siyasa tsakanin tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da kuma tsohon maigidansa Rabi'u Kwankwaso.
A shekarar 2020 ne gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta tsige Sarki Muhammadu Sanusi II daga matsayin Sarkin Kano.
Gwamnatin ta ɗauki matakin ne bayan raba masarautar ta Kano zuwa masarutu biyar, inda Aminu Ado Bayero ya kasance sarkin Bichi - nan ne alaƙa ta fara yin tsami tsakanin sarakunan biyu.
Bayan tsigewar, aka naɗa Aminu Ado a matsayin sarkin Kano.
Sai dai bayan ƙwace mulkin jam'iyyar hamayya ta NNPP a zaɓen shekara ta 2023 sai wata taƙaddamar ta sake kaurewa.
Inda a watan Mayun 2024 ne majalisar dokokin jihar Kano ta rushe dokar da ta samar da masarautun jihar biyar, wadda ita ce ta haifar da naɗin Aminu Ado Bayero.
Sannan kuma ba tare da ɓata lokaci ba gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya sake mayar da Muhammadu Sanusi II kan kujerar sarautar Kano.
Sai dai tun wancan lokacin ne ɓangarorin biyu ke jayayya game da rawanin, lamarin da har yanzu ke a gaban kotu.