Waɗanne ƙasashe 'masu tasowa' Trump ya ce zai hana su cirani a Amurka?

Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 5

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa zai hana cirani a Amurka ''har abada'' daga duka ''ƙasashe masu tasowa.''

Trump dai bai yi ƙarin bayani kan shirin nasa ba kuma bai kai ga lissafa ƙasashen da lamarin zai shafa ba.

Shugaban ƙasar ya kuma zargi masu gudun hijira da kawo ''taɓarɓrewar zamantakewa a Amurka'' kuma ya sha alwashin tasa ƙeyar ''duk wanda ba ya kawo ci gaba ga Amurka''.

Kalaman na sa na zuwa ne kwana guda bayan wani ɗan Afghanistan ya harbi wasu dakarun rundunar sojin tarayya a birnin Washington DC, wanda ya yi sanadiyar mutuwar ɗaya daga cikinsu a ranar 27 ga watan Nuwamba.

"Zan dakatar da ƙaura na dindindin daga duk ƙasashe masu tasowa na duniya don bai wa Amurka damar farfaɗowa, zan dakatar da batun miliyoyin mutanen da Biden ya ba su izinin shigowa ƙasarmu ba bisa ƙa'ida ba, gami da waɗanda Sleepy Joe Biden ya yi amfani da alƙalami mai sarrafa kansa domin ba su izini, da kuma korar duk wanda ba shi da wata gudumawa da zai bayar ga cigaban Amurka," in ji shi a dandalin sada zumunta na Truth Social.

A baya dai Trump ya bayyana harbin a matsayin babbar barazana ga tsaron ƙasar kuma ya yi alƙawarin ɗaukar matakin kawar da duk wani baƙo "daga kowace ƙasa da wanda bai dace ya zauna a nan ba".

A ranar Laraba, Amurka ta dakatar da aiwatar da duk wasu buƙatu na shige da fice daga ƴan ƙasar Afganistan, gwamnatin ta ce ta yanke shawarar ne har sai an sake nazarin "ƙa'idojin tantancewa saboda batu na tsaro ".

A saƙon da ya wallafa a daren ranar alhamis, Trump ya kuma yi alƙawarin "soke duk wani tallafi na tarayya hda ake bai wa duk waɗanda ba ƴanƙasa ba".

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tun da farko a ranar Alhamis ɗin hukumar kula da shige da fice ta Amurka ta ce za ta sake nazari kan katin iziznin zama a ƙasa da aka bai wa mutanen da suka yi hijira zuwa Amurka daga wasu ƙasashe 19.

Da BBC ta tambayi ko waɗanne ƙasashe ne ke cikin jerin sunayen, hukumar ta yi nuni da wata sanarwa da fadar White House ta fitar a watan Yuni da ta ambaci; Afghanistan da Cuba da Haiti, da Iran da Somalia da Venezuela.

Sauran ƙasashen da za a sake nazarin takardunsu sun haɗan da Burma da Chadi Jamhuriyar Congo da kuma Libya.

Gwamnati ba ta bayar da ƙarin bayani game da yadda za a sake yin nazarin takardun ba.

Sanarwar guda biyu na zuwa ne bayan da rahotanni suka ce wanda ake zargi da aikata harbin na Washington DC ya shiga Amurka a shekarar 2021 a ƙarƙashin wani shiri na ba da kariya ta musamman ga ƴan Afghanistan bayan ficewar Amurka daga Afghanistan.

Jami'ai sun ce wanda ake zargin mai suna Rahmanullah Lakanwa ya taɓa yin aiki tare da hukumar leƙen asiri ta CIA a Afganistan kuma ya taimaka wajen gadin sojojin Amurka a filin jirgin Kabul a lokacin da aka kwashe su, kamar yadda wani tsohon kwamandan sojan da ya yi aiki da shi ya shaida wa Sashen Afganistan na BBC.

Waɗanne ƙasashe ne 'masu tasowa' da Trump ke magana a kai?

Trump da jami'ansa ba su bayar da cikakken bayani kan shirin ko sunan ƙasashen da abin ya shafa ba.

Amma Joseph Edlow, wanda shi ne Darakta a hukumar kula da shige da fice ta Amurka, ya ce bisa ga umarnin Trump, ya ba da umarnin yin cikakken nazari kan takardun kowane ɗan cirani ko baƙo daga kowace ƙasa da ake da damuwa a kanta.

To, su wane ne waɗannan ''ƙasashen da ake da damuwa a kansu' kuma menene matsayinsu?

Shugaba Donald Trump na watan Yuni ya rattaba hannu kan wata doka ta zartarwa wadda ta sanya cikakken takunkumin hana shiga Amurka daga ƙasashe 12 tare da dakatar da shigar ƴan wasu ƙasashe bakwai waɗanda ya kira wanda ake da damuwa a kansu.

Sun haɗa da:

  • Afghanistan - Cikakkiyar dakatarwa
  • Burma - Cikakkiyar dakatarwa
  • Chad - Cikakkiyar dakatarwa
  • Republic of DR Congo - Cikakkiyar dakatarwa
  • Equatorial Guinea - Cikakkiyar dakatarwa
  • Eritrea - Cikakkiyar dakatarwa
  • Haiti - Cikakkiyar dakatarwa
  • Iran - Dakatawar wani ɓangare
  • Libya - Cikakkiyar dakatarwa
  • Somalia - Cikakkiyar dakatarwa
  • Sudan - Cikakkiyar dakatarwa
  • Yemen - Cikakkiyar dakatarwa
  • Burundi - Dakatawar wani ɓangare
  • Cuba - Dakatawar wani ɓangare
  • Laos -Dakatawar wani ɓangare
  • Sierra Leone - Dakatawar wani ɓangare
  • Togo - Dakatawar wani ɓangare
  • Turkmenistan - Dakatawar wani ɓangare
  • Venezuela - Dakatawar wani ɓangare

'Me ake nufi da 'ƙasashe masu tasowa'?

Batun rarraba ƙasashen duniya bisa yadda suka ci gaba ya samo asali ne daga yaƙin cacar baka, lokacin da duniya ta rabu tsakanin ƙasashen yammacin turai masu goyon bayan Amurka da kuma ƴan gurguzu na gabashin Turai. Sauran ƙasashe ƴan 'ba ruwana' sai aka sanya su a ɓangaren ''ƙasashe masu tasowa'' .

Galibi sun ƙunshi ƙasashe ne da ake kwatanta su da masu fama da talauci.

Majalisar Dinkin Duniya ta zayyana takamaiman jerin sunayen waɗannan ƙasashen bisa la'akari da raunin tattalin arziki da zamantakewa, wanda suka haɗa da ƙasashe kamar Afghanistan da Bangladesh da Haiti, da Yemen.

A halin yanzu, kasashe 44 ne ke cikin ƙasashen da Majalisar Dinkin Duniya ke kallo a matsayin masu raunin ci gaba

Kasashe 32 sun faɗo ƙarƙashin Afirka:

  • Angola
  • Benin
  • Burkina Faso
  • Burundi
  • Jamhuriyar Afrika ta tsakiya
  • Chadi
  • Comoros
  • Jamhuriyar Dimokrɗiyar Congo
  • Djibouti
  • Eritrea
  • Habasha
  • Gambia
  • Guinea
  • Guinea Bissau
  • Lesotho
  • Liberia
  • Madagascar
  • Malawi
  • Mali
  • Mauritania
  • Mozambique
  • Nijar
  • Rwanda
  • Senegal
  • Saliyo
  • Somalia
  • Sudan ta kudu
  • Sudan
  • Togo
  • Uganda
  • Tanzania
  • Zambia

Kasashe 8 ne a nahiyar Asiya:

  • Afghanistan
  • Bangladesh
  • Cambodia
  • Jamhuriyar Lao
  • Myanmar
  • Nepal
  • Timor-Leste
  • Yemen

Ƙasa ɗaya ce a yankin Caribbean:

  • Haiti

Ƙasashe uku ne a yankin Pacific:

  • Kiribati
  • Solomon Islands
  • Tuvalu

Wani kwamiti mai kula da manufofin ci gaba ne ke bitar jerin sunayen waɗannan ƙasashe bayan kowace shekara uku, ƙungiyar ƙwararrun masana masu zaman kansu waɗanda ke ba da rahoto ga Majalisar Tattalin Arziki (ECOSOC) ta Majalisar Dinkin Duniya.

Za a yi bita ta gaba a shekarar 2027.