Ko Paul Biya zai 'kai labari' a zaɓen shugaban ƙasar Kamaru?

Asalin hoton, AFP/Getty Images
- Marubuci, Paul Njie
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
- Aiko rahoto daga, Yaoundé
- Lokacin karatu: Minti 6
Shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya, mai shekara 92, Paul Biya ya yi wa masu zaɓe a Kamaru alƙawarin cewa za su ''ƙara kwankwaɗar romon mulkinsa nan gaba'' yayin da ya ke neman wa'adin mulki na takwas a zaɓen shugaban ƙasar da za a yi ranar Lahadi.
Shugaban ya ɗare karagar mulkin Kamaru tun a 1982, kuma samun ƙarin wa'adin mulki na shekara bakwai na nufin zai mulki ƙasar na tsawon shekara 50, kuma zai cika shekara 100 a duniya idan ya cimma nasarar hakan.
Ya yi kunnen ƙashi ga kiraye-kirayen neman ya jingine aniyarsa ta sake tsayawa takara, kuma yana shan suka kan rashin bayyana a wajen yaƙin neman zaɓe, bayan ya halarci gangami ɗaya kacal daga cikin duk lokacin da aka shafe ana yaƙin neman zaɓe.
Suka da aka riƙa yi mashi bayan fitara da wani bidiyon yaƙin neman zaɓensa da aka haɗa da ƙirkirarriyar basira ta tilasta garzayawa gida daga Turai, da kuma bayyana a wani gangami a arewacin ƙasar.
A gangamin da aka yi a birnin Maroua mai ɗimbin ƙuri'u a ranarTalata, shugaba Biya ya yi jawabi ga magoya bayan jam'iyyarsa, inda ya nemi goyon bayan mata da matasa, yana mai yi masu alƙawarin bayar da fifiko ga buƙatunsu idan ya yi nasara a zaɓen.
Ya ce "Zan cika alƙawarina," yana mai jaddada buƙatar su ba shi "ƙuri'unsu masu daraja".
Amma mai sharhi a kan siyasa, Immanuel Wanah ya shaidawa BBC cewa tunda ya karɓi mulki, shugaba Biya ya mayar da hankali ne kawai ga yadda zai ci gaba da riƙe madafun iko, "lokuta da dama kuma yana kawar da kai daga buƙatun ƴan ƙasa domin cimma burin nasa".
Shi ma Dr Tilarius Atia, wani mai sharhi kan siyasar na da irin wannan tunani a kan shugaba Biya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masu sharhin na ganin cewa mutanen Kamaru sun fi sanin shugaba Biya fiye da sauran ƴan takarar, saboda fiye da kashi 60 na jama'ar ƙasar da yawan su ya kai miliyan 30, matasa ne ƴan ƙasa da shekara 25.
Matashiyar ƴar gwagwarmayar siyasa, Marie Flore Mboussi ta mayar da hankali ga fatan samun "sabon jini" saboda yaƙinin da take da shi cewa "daɗewar shuga a kan mulki na kai shi ga sakewa da rashin jajircewa ga aiki".
Ta shaidawa BBC cewa "Bayan shekara 43, jama'ar Kamaru sun gaji da shi".
Zaɓen shugaban ƙasar na zuwa ne a tsakiyar koken da ake yi game da hauhawar farashi da ƙalubalen tsaro da rashawa da kuma rashin aikin yi a Kamaru.
Mafi yawan ƴan takarar sun mayar da hankali wajen tattauna matsalar rashin aikin yi tsakanin matasan Kamaru.
Wata ƙididdiga da hukumar kula da masu yin ƙaura ta duniya ta fitar ta nuna cewa aƙalla kashi 40 ma matasan Kamaru masu shekara 15 zuwa 35, waɗanda kuma kashi 23 a cikin su suka kammala karatu, suna fama da matsalar samun aikin yi.
"Matasan sun fi mayar da hankali ga neman tsallakewa ƙasashen waje domin neman aikin yi, domin sun yarda cewa babu wata dama a cikin ƙasar su,'' In ji Vanina Nzekui, wata matashiya mai shekara 26, wadda ta kammala karatun ta.
Ta ce matasan na "Faɗa wa kansu cewa duk tsofaffi sun mamaye wuraren da ya kamata su yi aiki da mukaman da ya kamata su riƙe,''
Amma Aziseh Mbi, mai shekara 23 na ganin cewa bai kamata yawan shekaru ya zama abin dubawa wajen tantance shugaba nagari ba.
Mai rajin kare haƙƙin bil adaman ya ce shugaba Biya ya gudanar da ayyukan ci gaba da dama, ciki harda na bunƙasa matasa.

Asalin hoton, Reuters
Bayan rashin aikin yi tsakanin matasa, wani abu da ya ɗauki hankali a shirye shiryen zaɓen shi ne dambarwar cire sunan Maurice Kamto daga jerin ƴan takara.
A watan Yuli, hukumar zaɓe ta haramta wa jagoran adawar Kamaru mai shekara 71, Maurice Kamto tsayawa takara saboda wani ɓangare na jam'iyyar ya gabatar da wani ɗan takara na daban.
Matakin wanda kotun kundin mulkin ƙasa ta tabbatar ya sha suka sosai, lamarin da wasu ke ganin hanya ce ta hana ɗan takara mai ƙarfi fuskantar shugaba Biya a zaɓen na ranar Lahadi.
Bayan zuwa na biyu a zaɓen 2018, Kamto ya yi iƙirarin nasara kuma ya jagoranci zanga-zanga a kan titunan ƙasar.
"Cire sunan Kamto daga takara ya janyo koma baya ga ingancin dimokuradiyyar mu, saboda ya kamata a bari kowa ya yi takara in dai ya cancanta,'' in ji Dr Artia.
Ƴan takara 12 aka amince su yi takara a zaɓen, cikin su harda Issa Tchiroma Bakary da Bello Bouba Maigari - dukkansu tsaffin abokan ɗasawa da shugaba Biya da suka fito daga yankin arewacin ƙasar. Sun ajiye muƙaminsu na minista domin fafatawa da ubangidan nasu a zaɓe.
Dan majalisa Cabral Libii da shugaban jam'iyyar adawa ta Social Democratic Front (SDF) Joshua Osih da kuma mace ɗaya tilo a cikin su, Patricia Tomaïno Ndam Njoya duk suna cikin takarar shugaban ƙasar.
Akwai kuma ƴan takara biyu da suka janye aniyar su domin goyon bayan Maigari na jam'iyyar NUDP, cikin su harda fitaccen lauya, Akere Muna. Wannan na nufin ƴan takara 10 ne za su fafata a zaɓen shugaban ƙasar na ranar Lahadi.

Asalin hoton, Michel Mvondo / BBC
Kafin zaɓen wanda zagaye daya kawai za a yi domin fitar da ɗan takarar da ya fi yawan ƙuri'u a matsayin wanda ya yi nasara, an yi ta kiraye-kirayen ganin ƴan adawa sun haɗa kai domin gabatar da mutum ɗaya a cikinsu domin karawa da shugaba Biya, wanda bai taɓa faɗuwa zaɓe ba.
Tchiroma Bakary ya samu goyon bayan Union for Change, wata gamayyar ƙungiyoyin siyasa da na fararen hula fiye da 50 da suke fatan ganin ya zama shugaban ƙasa.
Amma yunƙurin bai kankama ba saboda ya gaza samun goyon bayan sauran masu ruwa da tsaki.
Kamto ya ce ya zauna da wasu ƴan takarar, ciki harda na yankin Arewa, Tchiroma Bakary da Maigari, domin ƙarfafa masu gwiwa sun yi haɗaka domin fuskantar shugaba Biya, amma bayan ya gano babu mai niyyar janyewa a cikinsu, sai ya buƙaci ƴan Kamaru su zaɓi wanda ya fi kwanta masu a rai.
Dr Atia na da ra'ayin cewa rashin dunƙulewa domin goyon bayan mutum ɗaya zai janyo wa ƴan adawa rashin nasara a zaɓen.
A lokacin yakin neman zaɓe, Tchiroma Bakary, mai shekara 76 na jam'iayyar Cameroon National Salvation Front party kuma tsohon kakakin gwamnati ya riƙa tara ɗimbin mutane, kuma wasu masu sharhi na ganinsa a matsayin babban abokin karawar shugaba Biya a zaɓen.
A ranar Lahadin makon jiya, dubban magoya baya suka jira a cikin ruwan sama domin halartar yaƙin neman zaɓensa a birnin Doula.
Ya yi alƙwarin sauya akalar tsarin da ya shafe shekaru 20 yana cikin masu tafiyar da shi.
Duk da cewa Tchiroma Bakary yana da ɗimbin magoya baya a arewaci, masu sharhi na ganin cewa Biya zai iya kayar da shi, da kuma sauran ƴan adawar.
"Shugaba Biya na buƙatar rinjaye ne komai tazararsa domin lashe zaɓen, kuma ina ganin zai yi nasara duk da yunƙurin ƴan adawa,'' Dr Atia.

Asalin hoton, Michel Mvondo / BBC
Bayan kaɗa ƙuri'a a zaɓen na ranar Lahadi, majalisar kundin mulkin ƙasa tana da kwanaki 15 ta sanar da sakamakon zaɓe.
Tuni dai ministan harkokin cikin gida ya yi gargaɗin cewa ba a amince da ƴan takara su fito suna sanar da sakamakon zaɓe tun kafin a fitar da shi a hukumance ba.

Asalin hoton, Getty Images/BBC











