Wace dama ta rage wa arewacin Kamaru a zaɓen 2025?

..

Asalin hoton, BBC/Collage

Lokacin karatu: Minti 3

A karon farko arewacin Kamaru ke samun ƴan takarar neman shugabancin ƙasa guda biyu a zaɓen 2025 da za a yi a watan Oktoba.

Masana harkokin siyasa na cewa wannan ce damar da ta rage wa yankin wajen ganin ya samu ya karɓi mulkin da ya suɓuce masa fiye da shekaru 43.

Shugaba mai ci a yanzu Paul Biya, mai shekara 92, shi ne shugaban ƙasar da ya fi kowanne tsufa a duniya.

Shi ne shugaban ƙasar tun shekarar 1982, kusan shekara 43.

Arewacin Kamaru da ya ƙunshi lardunan Adamawa da Arewa da kuma Arewa Mainisa na taka muhimmiyar rawa a zaɓen jamhuriyar.

Bayanai sun nuna cewa akwai masu ƙuri'a fiye da miliyan biyu a yankin Arewacin da ke iya sauya alƙiblar zaɓe.

Aƙalla mutum miliyan takwas ne suka yi rijistar zaɓe daga cikin mutum miliyan 30 na yawan al'ummar jamhuriyar.

Mutum biyu ƴan arewacin jamhuriyar Kamaru ne suka shiga sahun masu fafatawa da shugaban ƙasar Paul Biya da ke neman sabon wa'adi.

Mutanen sun haɗa da tsohon ministan yawon buɗe ido na ƙasar, Bello Bouba Maigari da tsohon kakakin gwamnati, IssaTchiroma Bakary.

'Arewacin Kamaru zai ɓarar da damarsa'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bello Bouba Maigari, mai shekara 78, ƙwararren ɗan siyasa ne da ya fito daga arewacin Kamaru mai ɗimbin ƙuri'u kuma yana takara ne a jam'iyyar National Union for Democracy and Progress (NUDP).

Sai kuma Issa Tchiroma Bakary ɗan shekara 75 ya tsaya ne a jam'iyyar Cameroon National Salvation Front (CNSF).

Ambasada Muhammad Sani, daya daga cikin dattawan yan siyasar ƙasar ta Kamaru, ya shaida wa BBC cewa dattawan yankin sun ce fitowar mutum biyun ba zai zame wa yankin alkairi ba.

"Muna cikin ɗarɗar dangane da siyasar Kamaru saboda Allah ya ba mu damar ficewa daga masifa da bala'i da muke ciki fiye da shekara 40. Damar ta zo amma muna neman mu ɓarar da ita. Mun samu mutum biyu suna neman su kawo son rai.

Dukkanninsu tsakanin Bouba Bello Maigari da Issa Ciroma Bakary sun gaza haɗa kai. Wannan na nuni da cewa za mu ɓarar da damar da mu ƴan arewa muke da ita. Muna son su zo su dunƙule a mara wa mutum ɗaya baya. Wannan ita kaɗai ce damar da Allah ya ba mu na sauya siyasar. Kuma idan dai suka haɗe kai to da izinin Allah za mu ƙwace sarauta ba su isa ba." In ji Ambasada Muhammad Sani.

Wane ne Issa Tchiroma Bakary?

..

Asalin hoton, Getty Images

Issa Tchiroma Bakary - fitaccen minista kuma daɗaɗɗen abokin tafiyar shugaba Paul Biya ya bar kujerarsa ta ministan sadarwa domin ƙalubalantar tsohon ubangidan nasa a zaɓe mai zuwa.

Watanni huɗu kafin babban zaɓen jamhuriyar ta Kamaru, Tchiroma ya ce al'ummar ƙasar sun yanke ƙauna da gwamnatin Paul Biya, inda daga nan ne sai ya koma wata jam'iyyar ta masu hamayya.

"Babu yadda za a yi ƙasa ta ci gaba a ƙarshin mutum ɗaya," in ji Bakary.

Wane ne Bello Bouba Maigari?

..

Asalin hoton, Getty Images

Bello Bouba Maigari, mai shekaru 78 ya kasance abokin tafiyar shugaba Paul Biya a tsawon fiye da shekaru 30. Maigari ya kasance tsohon firaiminista a jamhuriyar ta Kamaru.

Yanzu haka zai yi takarar domin ƙalubalantar Paul Biya a jam'iyyar NUDP duk da cewa bai ajiye muƙaminsa na ministan harkokin yawon buɗe ido ba.

Shi ne ministan gwamnati na biyu daga arewacin ƙasar da ya bayyana aniyarsa ta takarar neman shugaban ƙasa a baya-bayan nan wani abu da ke nuna ɓaraka tsakanin shugaba Paul Biya da masu faɗa a ji a arewacin ƙasar.