Yadda Paul Biya mai shekara 92 ke amfani da soshiyal midiya don neman ƙuri'a

Asalin hoton, AFP via Getty Images.
- Marubuci, Ousmane Badiane
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 3
Tun ma kafin shugaban ƙasar, wanda ya fi daɗewa a duniya ya tabbatar da sake tsayarwasa takara a karo na takwas, abubuwan da ake yaɗawa a shafukansa na sada zumunta sun riga sun bayyana komai ga waɗanda suka fahimci haka.
A makon jiya da Paul Biya mai shekara 92 ya tabbatar zai takara, kawai tabbaci aka samu kan abubuwan da ya bayyana a shafukan nasa.
Amma yunƙurin Biya na jawo hankalin matasan ƙasar domin su sake zaɓarsa a zaɓen na watan Oktoba, na fuskantar ƙalubale, kamar yadda masana suka bayyana wa BBC.
"Kamaru na da masu amfani da kafofin sadarwa sama da miliyan 5.4, amma kashi 95 na matasan ƙasar sun fi amfani da WhatsApp - inda shugaban ƙasar bai cika amfani da shi ba," in ji Rostan Tane, marubucin littafin Cameroon 2024 Multimedia Audience Study.
Wata matsalar kuma ita ce rashin sahihanci. "yawancin mutane sun san ba Paul Biya ɗin ba ne ke rubutu a shafokansa na sadarwa in - wanda hakan na ƙara kawo rashin yarda," in ji Hervé Tiwa, malamin fasahar sadarwa.
"Suna fitar da bayanai ne kawai ba tare da damuwa a abin da mutane suke faɗa ba. Wannan ke ƙara nuna cewa tsari ne kawai na jan hankali, ba neman jin ta bakin mutane ba."
Amma me hakan ke nufi?
Matasa sun fi yawa a ƙasar Kamaru. Kusan kashi 60 na ƴan ƙasar matasa ne ƴan ƙasa da shekara 25, kuma sama da rabin masu zaɓe ba su kai shekara 30 ba, wanda hakan ke nufin matasa za su iya sauya akalar zaɓen ƙasar.
"Ya kamata a yi amfani da kafofin sadarwa ne domin inganta dimokuraɗiyya da bayyana harkokin gwamnati a bayyane, ba kawai domin tallata takara ba," masanin sadarwa, Ulrich Donfack mai shekara 27.
Matasa suna so ne su riƙa ganin ana ɗaukar mataki a abubuwan da suks shafe su, in ji Falone Ngu mai shekara 27.

Asalin hoton, Courtesy of Falone Ngu
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Rashin aikin ya yi yawa a Kamaru, inda matasa da dama da suka kammala digiri kuma suke da sakamako mai kyau suke ta neman aiki, amma ba su samu ba. Haka kuma ƙasar na fama da cin hanci da rashin tsaro.
Amma maimakon mayar da hankali kan waɗannan matsalolin, rubuce-rubucen Biya a kafofin sadarwa sun fi mayar da hankali ne kan nasarorinsa a shekara 43 da ya yi yana mulki - lokacin da ba a haifi da yawa daga cikin ƴan ƙasar ba.
Masanin kimiyyar sadarwa, Aristide Mabatto, ya ce ma'aikatan Biya sun fi wallafa tsakure ne daga cikin jawaban shugaban ƙasar sama a guda 300 a harshe Ingilishi da Farasanci.
Sai dai da alama wannan tsarin yaƙin zaɓen samu karɓuwa ba sosai, duk da cewa an ɗan samu sauyi a kan baya.
"A baya bai cika damuwa da fitar da bayanai ba sai dai na dokoki da jawabi ga ƴanƙasa. Yadda yanzu ya fara amfani da kafofin sadarwa na nuna yunƙurinsa na tafiya da zamani da ƴan zamanin," in ji Tiwa.
A bara ne aka yi kimanin mako shida ba a ga Biya ba, lamarin da ya wasu suka riƙa tambayar ko dai rashin lafiya ne, har aka fara raɗe-raɗin ya rasu.
Magoya bayansa sun yaba da fara amfani da kafofin sadarwa da yake yi domin jan hankalin matasa.
Amma wasu na amfani da kafofin sadarwa wajen yi masa shaguɓe. A ƙasan rubuce-rubucensa yana shan suka sosai, kamar yadda muka tattara dafa Facebook da X.
"Alamu na nuna cewa sai a wannan shekarar ta 2025 ya gane akwai intanet, amma duk yana haka ne domin jan hankalin masu zaɓe," in ji wata mai suna Cynthia.
"A ƙarshe dai yanzu ya fara magana da matasa," in ji Jean-Pierre.
"Ƴan Kamaru hanyoyi suke buƙata, ba rubutu a kafofin sadarwa ba," in ji Mireille.
"Har yanzu ban samu natsuwa da kwanciyar hankali ba," in ji wani ɗankasuwa, Che Arnold.
"Muna buƙatar ayyuka ne na zahiri ba rubuce-rubuce a Facebook da X ba."
Yanzu dai Biya zai jira ne zuwa zaɓen na watan Oktoba domin ganin ko wannan sabon tsarin da ya ɗauka zai ɓille masa ta hanyar jan hankalin matasan ƙasar su kaɗa masa ƙuri'a.
Tattara bayanai da tacewa daga Natasha Booty










