Me ya sa mata ke samun sauye-sauyen halayya a lokacin jinin al'ada?

Asalin hoton, getty image
- Marubuci, Aisha Babangida
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
- Aiko rahoto daga, Abuja
“Idan na fara al'ada, a ranar farko gaba ɗaya nake rasa mene ne ke min daɗi, kawai zan dinga jin ƙyamar mutane, abu kadan yake bata min rai."
Fatima ƴar shekara 28 ce kuma tana da aure, ta ce duk lokacin da take al'ada, daga ranar farko take samun sauyi a halayyarta daga yadda take ji har canji a jikinta.
Ta ce "Kwanaki biyu na farko ba na ma iya cin abinci sosai amma sai marmarin kayan zaƙi, wanda nake kasa hana kaina."
"Amma ni da yake kwana takwas nake dauka idan ina al'ada, a kwana na huɗu zan ji na daina jin abubuwan da nake ji."
Mata da dama kan shiga yanayi irin na Fatima, sai dai wasu lamarin nasu kan sha bamban.
Misali, Maryam Dauda, ƴar shekara 19 ce wadda ba ta riga ta yi aure ba, ta ce idan ta fara jinin al’ada, ba ta yawan samun bacin rai ko kuma saurin fushi, amma kuma tana yawan samun faɗuwar gaba da kuma ciwon mara.
"Ni fa idan na fara, wallahi daga rana ta farko sai kawai gabana ya rinka fadi, sai kuma ciwon mara sosai da kuma yawan cin abinci."
Dakta Kabir Dara, ƙwararen likitan mata ne a wani asibiti mai zaman kansa da ke a jihar Katsina, ya ce wasu mata sukan samu wasu ‘yan sauye-sauye a yanayin zamartakewarsu ko na yanayin jikinsu ko kuma yadda suke ji kamar yawan saurin fushi da bacin rai da sauransu wato 'mood swing' a turance.
A cewarsa wani abu ne da tamkar ruwan dare ne ga mata, sai dai kowace da irin nata sauye-sauyen da take samu.
A wasu lokuta irin wadannan sauye-sauye kan zamo kalubale tsakanin mata da miji, musamman sabbin aure, a lokacin da miji bai gama fahimtar abin da ke faruwa ba.
Kalubale ga maza
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Isma'il lawal na daga cikin mazan da matansu ke shiga cikin irin wannan yanayi, ya ce a duk lokacin da matarsa za ta fara al’ada, kusan komai ne yake ɓata mata rai, ko da kuwa bai taka kara ya karya ba.
Ya ƙara da cewa matarsa ba ta walwala kuma magana ma kan yi ma ta wahala, idan kuma ta tashi yin maganar ba lallai ne ta faɗi abu mai daɗi ba, ya ce haka za ta kasance ranta a bace na wani tsawon lokaci.
"Galibi takan fara shiga wannan yanayin ne kwanaki biyu ko daya kafin ta fara."
"Da farko dai ban gane cewa abin lalura ba ce wanda hakan ya sa muka rika samun ce-ce-ku-ce a duk lokacin da abin ke faruwa saboda ni ban san dalilin da zai sa haka nan kawai yanayin mutum ya sauya ba kuma ya shiga halin bacin rai da kunci."
Lawal ya ce a lokacin da ya gano dalilin da ya hakan ke faruwa da matarsa, sai ya fara kokarin kauce wa musayar kalamai da ita a duk lokacin da ta shiga wannan hali, sannan ya rika kokarin ganin yadda zai taimaka mata, ta hanyar lallashi da kuma gudanar da wasu ayyukan gida saboda ta samu hutu.
"Ina ƙoƙarin na ga cewa na yi hakuri da yanayin nata a wannan lokacin ganin cewa ba abu ne mai dorewa ba." in ji Lawal.
Kamar Lawal, Fatima ma ta ce mijinta yakan fahimci halin da take ciki, har ma yakan taimaka mata.
Ta ce "A duk lokacin da nake fuskantar irin wadannan sauye-sauye, mijina yana fahimta, duk abin da na yi na bacin rai, ba ya yin komai, lallashi na ma yake yi, amma kuma yana hana ni shan zaƙi.
Me ya sa mace ke samun sauye-sauye a lokacin al’ada?
Dakta Kabir Dara ya ce ba lokacin haila kaɗai mata ke fuskantar sauyi na dabi’a ko mu’amala ba, ya ce yanayinsu na sauyawa ne tun daga mako ɗaya ko biyu kafin su fara al'ada din.
Ya ƙara da cewa abin da ke kawo waɗannan canje-canje na yanayi ya haɗa da wasu canji daga sinadarai na jiki wanda ake ce wa 'hormones'.
Dakta Kabir ya ce zagayowar jinin al'ada, an raba shi ne kashi biyu, akwai abin da ake ce wa 'follicular phase' wanda shine daga rana ta farko zuwa rana ta goma sha hudu akwai kuma wanda ake ce wa 'luteal phase' wanda shine daga rana ta goma sha huɗu zuwa ranar ta ashirin da takwas kafin mace ta yi al'ada.
"Wannan 'luteal phase' din ake samun matsalar canjin yanayin jiki (mood swings) inda za a ga wasu mata suna damuwa, nan da nan suna samun ɓaccin rai", in ji likitan.
"Wani lokaci sai na mace ta rasa me ke mata dadi, sai ta ga ba ta yawan mai da hankali kan abubuwa kamar irin wajen karatu, rubuta jarabawa ko wajen interview na neman aiki da sauransu, sai suga suna kuka hakannan."
"Tsakanin ma'uarata kuma sai a ga ana yawan samun faɗa tsakanin mata da miji ko tsakanin kishiyoyi a lokacin."
"Toh, wannnan canjin yanayi na jiki da kuma yadda mata ke ji na faruwa ne kawai saboda canjin sinadare na jiki ne kawai."
"Akwai sinadarin jiki da aka kira da 'Progesterone' wanda shi ne ke sanya waɗannan canjin yanayin jiki ko yadda ake ji."
"Kuma a wannan lokacin akwai wanda ake kira da 'serotonin ko happy hormones' wanda ke raguwa a lokacin da na mace ke samun canjin yanayi a jikinta ko yadda ta ke ji.
Likitan ya ce akwai sauran abubuwa da ke janyo canjin yanayin mace lokacin al'ada da suka haɗa da rashin taimaka musu lokacin da suke buƙata da damuwa da kuma idan aiki yayi musu yawa.
Dukkan mata ke samun wannan canjin yanayin?
Dakta Kabir ya ce ba dukkan mata ke samun wannna canjin yanayi na jiki ba da yadda mata ke ji.
Likitan ya ce wasu matan sun riga sun daidaita yanayin mu’amalarsu da sauye-sauyen da kan zo musu lokacin al’ada ta yadda sukan ci gaba da rayuwarsu ba tare da wani ya san akwai wani sauyi a tattare da su ba.
Ya ce kuma wasu irin waɗannan matan suna samun taimakon da suke buƙata sosai daga mazansu da danginsu da yaransu da kuma abin bai dame su ba sosai.
Likitan ya ƙara da cewa na wasu na iya tsananta da har ya zamo musu matsalar da zai kai ga kwantar da su a asibiti da sauransu.
"A ƙasashen da matsin lamba ya yi yawa sosai, wasu matan har suna iya yuƙurin kashe kansu, amma ba dukkan mata ke samun irin haka ba."
"Ya danganta ne da yanayin matsin lambar da mace ke ciki da kuma taimakon da take samu na kusa da ita."
"An lura cewa akwai abubuwan da ke ta'azara samun wannan canjin yanayin jiki da yadda mata ke ji da suka hada da cin abubuwa masu zaƙi sosai, da abubuwa masu gishiri."
Wane irin taimako mata ke buƙata a wannan lokaci?
Dakta Kabir ya ce abin da ake so idan mace na cikin wannan yanayi shi ne samun lallashi da cikakken taimako wajen mazansu ko ƴan uwansu ko danginsu.
Ya ƙara da cewa a yi ƙoƙarin a tabbatar da an janye abubuwan da ake tunanin cewa suna iya ta'azara wannan canjin yanayi kamar su sukari da gishiri da maiƙo, da caffaine, da shan taba idan masu sha ne da shan barasa da dai sauransu.
"Su ma matan su dage wajen hana kansu shan abubuwan zaƙi saboda a lokacin, sune abin marmari sosai, sai mata sun dage sosai."
"Idan kuma a fuskanci cewa waɗannan mata na samun matsalar baccin rai, na kusa da su su dage su ƙauracewa irin abubuwan da zai ɓata musu rai, na ɗan ƙanƙanin lokaci ne, komai zai zo ya wuce."
Likitan ta ƙara da cewa idan an fahimci abin da suke buƙata, idan mai yiwuwa ne, a dage da yi musu, idan kuma ba mai yiwuwa bane, a san yadda za a bi da su da lallashi domin gujewa ɓaccin rai.
Shin samun canjin yanayin jiki ko yadda mace ke ji lokacin al'ada cuta ce?
Dakta Kabir ya ce samun canjin yanayin jiki ko yadda mace ke ji a lokacin al'ada ba cuta bace indai ba abin da aka lura cewa ya wuce gona da iri ba kamar samun su 'premenstral syndrome' wato alamomin da mata da yawa ke samu mako daya ko biyu kafin al'adarsu, ana iya zuwa a ga likita wanda shima shawarwari ne zai bayar sai kuma maganin rage jin zafi haka.
Likitan ya kuma ce sai da canjin yanayin a jiki zai iya haifar da ciwon kai ko ciwon mara, samun yawan cin abinci haka da dai suaransu, ya ce su ne da ƴan rashin lafiyar da mace za ta iya yi, amma samun canjin yanayi a jiki ko yadda ake ji ya ce ba cuta ba ce.














