Abubuwan da ba ku sani ba game da ƙasar Somaliya

Asalin hoton, SORAYA ALI
A cikin jerin wasikunmu daga 'yan jarida na Afirka, Soraya Ali ta yi ƙoƙarin kwatanta rayuwa a Somaliya a lokacin kwanciyar hankali da kuma halin tashin hankali da ƙasar ke ciki a yanzu.
Ban taɓa zuwa gida ba sai cikin makonnin nan.
Ƙasar da nake jin yaren, kuma ina kama da ƴan ƙasar amma ban taɓa zuwa ba.
Nan shi ne Somalia.
Amma a wannan watan, na bi sahun yan ƙasashen wajen da suke shiga ƙasar inda ni ma na yanki tikitin zuwa ƙasar tawa.
An haife ni a Landan kuma a can na girma, kimanin nisan mil 6,000 (kilomita 9,700) daga tushen iyalina.
Lokacin da nake girma, ko yaushe nakan yi tunanin cewa wurare biyu ne masu matuƙar bambanci.
Ina jin labarin babban birnin ƙasar, Mogadishu a kafafen yaɗa labaru - a matsayin birnin mutuwa da tagayyara, wanda aka bayyana a matsayin "wuri mafi hatsari a duniya".
To amma iyayena kan rinƙa faɗin bayanai masu daɗi game da "Xamar" kamar yadda mutanen garin ke masa laƙabi.
Sukan kwatanta shi a matsayin wani kyakkyawan birni, wanda ke a bakin teku da ke kan iyakar Afirka mafi tsayi, wanda mutane da yawa suka sani da "lu'u-lu'u na Tekun Indiya".
Na fahimci cewa duka nau'ikan biyu suna da gaskiya.

Asalin hoton, SORAYA ALI
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Yawancin ’yan Afirka mazauna waje, kamar ni, sun koma ƙasarsu ta asali.
Lokacin da na isa, na ji alamun kamar na dade ina zama a ƙasar amma a lokaci guda, rashin jin daɗi game da bambance-bambancen da kasancewa a cikin ƙasashen waje ya haifar.
An haifi iyayena a Mogadishu a ƙarshen shekarun 1950 kuma, kamar yawancin ƴan Somaliya, suna da abubuwan tunawa da su na ƙasar.
"Mun kasance muna shiga wurare a cikin dogayen kaya da suke da budi, kuma muna iya saka duk abin da muke so,
"mahaifiyata takan tuna abubuwan da suka faru a rayuwarta har ma da salon gyaran gashi.
Amma a zamanin yanzu, ana sa ran mata su saka kaya ma su rufe jiki gaba daya
"Abin da kike da shi kadai akuya ne," 'yan uwana suna tsokanata", abin ya ba ta mamaki.
Somaliyan da muka taso muna gani a fuskarmu ta nuna 'yan jaridun kasashen Yamma da ke sansanonin 'yan gudun hijira suna magana da wadanda ke cikin matsananciyar yunwa. A baya a cikin shekarun 1990, ya kasance saboda yakin da aka yi.
Amma ana nuna hotuna iri ɗaya, a cikin 2023, sakamakon rashin zaman lafiya da sauyin yanayi.
Ba zato ba tsammani, mafi kyawun hoto na Somaliya da na samu shi ne ta TikTok.
#SomaliTikTok yana da girma kuma hashtag ya tattara ra'ayoyi wajen biliyan 77.
Na hango rayuwar yau da kullun a Mogadishu ta hanyar kafofin watsa labarun, da kuma labarin mazauna gida da kuma mutane kamar ni.
Hakan ya sa na je na ganta da idona har ma na yi tunanin komawa wajen da zama.

Asalin hoton, SORAYA ALI
Tabbas Mogadishu har yanzu wuri ne mai hadari, kungiyar al-Shabab mai alaka da al-Qaeda na ci gaba da zama barazana.
Wani harin da aka kai a watan Oktoba ya kashe mutane fiye da 100.
Sai dai akwai wani bangare na birnin da ba nunawa ba - fargabar rashin zaman lafiya na nufin yawancin 'yan yammacin duniya ba sa tafiya cikin walwala.
Farar fuska daya tilo da na gani ita ce a cikin kewayen filin jirgin sama mai tsaro.
Amma ainihin Mogadishu za a iya gani ta hanyar wajajen cin abinci, kasuwanni, bakin teku da mutane.
Garin yana rayuwa da dare kuma an fi zagaye a kan babur mai kafa uku (Bajaja).
"Akwai bajaja shida ga kowane mutum," wani direba ya fada da wasa.
Abincin ya tuna min da girkin mahaifiyata.
A ko yaushe ana bayar da abinci na Afirka kamar nama da shinkafa, da ayaba, tare da jita-jita kamar taliya mai yaji, daga ƙasar Italiya ta mulkin mallaka a da.
Masunta na yankin suna ɗauke da manyan kifaye a kafaɗunsu, wanda darajarsu ta kai dubun dubatar daloli a Japan.
Abin bakin ciki shi ne, rashin samar da ababen more rayuwa da saka hannun jari a masana’antar kamun kifi a kasar da ta taba tasowa yana nufin ba kasafai suke samun ci gaba ba.
Sai dai yayin da Shugaba Hassan Sheik Mohamud ke cika shekara guda a kan karagar mulki, ana samun karuwar fahimtar cewa kasar na kan hanyar sake ginuwa.

Asalin hoton, SORAYA ALI
"Kun ga ginin ko'ina, muna samun gyaruwa a hankali in shaa Allah," direban bajajan dan shekara 24 ya nuna.
Kamar mutane da yawa, har yanzu bai sami kwanciyar hankali a Somaliya ba. Yakin ya barke a shekarar 1991 kuma kusan kashi 75 cikin dari na al'ummar kasar ba su kai 30 ba.
Ya kasance mai kyakkyawan fata amma tattaunawar tamu tana nuna rashin daidaiton da ke bayyana.
Kamar ƴan ƙasar waje da yawa, ina da gata na zaɓin komawa.
Yayin da sauran Somaliyawa, musamman wadanda ke wajen babban birnin kasar ke neman mafita.
A shekarar 2022, Somaliya ce ta kasance kasa ta takwas mafi yawan 'yan gudun hijira a duniya, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
Somaliya dai na daya daga cikin kasashen duniya da ke fama da matsalar sauyin yanayi kuma matsanancin yanayi ya tilasta wa dubban mutane barin gidajensu, inda fari mafi muni cikin shekaru 40 da suka gabata ya haifar ambaliyar ruwa.
Yayin da muke kara shiga cikin birni, na lura da gine-gine, sababbi da tsofaffi, kuma na yaba da tsarin gine-ginen masu salo na kasashen Musulmi da Afirka da kuma Italiya.
An ƙarfafa su a bayan shingen kankare da tarin jakunkunan yashi. Kuma a kusan kowane lungu da sako na birnin akwai wani matashi dan sanda dauke da bindiga kirar AK-47.
Ana jin kiran sallah ta hanyar lasifika kuma ana tsaka da karar harbe-harbe daga nesa.
Duk da abubuwan nan, ina jin alamun abubuwa za su canza, kuma ba ni kadai ba ce.
Garin ya cika da sauran ƴan ƙasashen waje, yawanci daga Minnesota ko Toronto, da kuma ƴan Somaliya mazauna yankin da suka kuduri aniyar samar da kwanciyar hankali.
"Na yi imani da ƙasata," wata budurwa 'yar kasuwa ta gaya min.
Ta ce ba ta son tafiya.
Ta ƙara da cewa "Za mu iya dawo da Somaliyan da iyayenmu suka fada mana."











