Shin ko zanga-zangar ƴan ƙwadago na samar da sakamako?

Asalin hoton, Getty Images
Ɗaruruwan jami'an ƙungiyar ƙwadago a Najeriya suka yi dafifi a fadin ƙsar domin nuna rashin amincewarsu ga ƙarin ƙudin wuta da gwamnati ta yi a watan da ya gabata.
Gwamnatin dai ta ce ta yi ƙarin ne saboda cire tallafin lantarki da ta yi, inda ƙarin ya shafi masu samun wuta ta tsawon awanni 20 ko fiye da haka da ake kira "Band A", inda aka ƙara musu naira 172 da farko.
To sai dai daga bisani gwamnati ta rage yawan kuɗin da naira 19, inda yanzu haka suke biyan naira 206 a kan kowane "unit"
Ba wannan ne karon farko ba da ƙungiyar ƙwadago ke ɗaukar matakin zanga-zanga ba amma kuma ba kasafai jama'a ke ganin tasirin matakn nasu ba.
Abin tambaya yanzu shi ne ko wannan matakin zanga-zangar kan wutar lantarki zai sa gwamnati ta sauka daga kan bakanta?
Wane tasiri zanga-zangar ƙungiyar ƙwadago za ta yi?

Masana da masu lura da al'amuran yau da kullum suna ganin abin da ƙungiyar ƙwadago ke yi a bu ne da ke sanyayawa 'yan Najeriya zuciya kasancewar jam'iyyun adawa sun gaza.
Kwamared Abdulmajid Babangida wani mai sharhi kan al'amura a Najeriya ya ce
"Dole ne a yaba musu kasancewar abin da suke yi shi ne 'yan Najeriya ke so. Ba za a kira ƙungiyar ƙwadago da kyanwar lami ba. A duk lokacin da suka ɗauki mataki za ka ga fa'idar abun ko da ba shi da yawa."
Ya ƙara da cewa "a lokuta da dama za ga yadda ƙungiyar ƙwadago sun ɗauki matakan da ko dai gwamnati ta sauya matsayinta ko kuma ta sassauta matakin.
Ƙungiyar ƙwadago ce ƙungiya mai kare muradun 'yan Najeriya a saboda haka idan har gwamnati ba ta ɗukar ƙungiyar da muhimmanci to wata rana fa 'yan Najeriya ne za su ɗauki hukunci a hannunsu." In ji Kwamared Abdulmajid.
Za dai a iya cewa tun bayan da ƙungiyar ta ƙwadago ta ja kunnen gwamnati kan ƙarin, sai gwamnatin ta sanar da ragin naira 19 daga 226 da aka sanya da farko.
'Ƙungiyar ƙwadago ta zama kyanwar Lami'

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shi kuwa wani mai sharhi kan al'amuran ƙwadago kuma tsohon shugaba a ƙungiyar wanda ba ya son a ambaci sunansa ya shaida mana cewa "yanzu ƙungiyar ƙwadago ta zama kynwar Lami wato ga tsoratarwa amma kuma babu cizo"
Tsohon ɗn ƙwadagon ya ƙara da cewa "rabon ƙungiyar ƙwadago da hana gwamnati ɗaukar wani mataki sannan kuma ta sami goyon 'yan ƙasa tun lokacin tsohon gwamnan jihar Edo, Kwamared Adams Oshiomole da Kwamared Abdulwaheed Umar.
Idan ba ka manta ba a 2012 lokacin tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya so ya cire tallafin man fetir amma ƙungiyar ƙwadago bisa goyon bayan 'yan ƙasa ta yi masa ca a ka har sai da aka fasa cire tallafin." In ji tsohon ɗan ƙwadagon.
Harwayau, mai sharhin ya kuma ce " ka duba ka gani tun da shugaba Tinubu ya hau yake fito da tsare-tsare irin na cutar da talakawa amma wani amfani matakan ƙungiyar ƙwadago suka yi?
Tinubu ya cire tallafin mai kuma 'yan ƙwadago sun yi zanga-zanga da yajin aiki amma me hakan ya haifar? Kullum sai jiya ya yau.
'Gwamnatin Buhari ce ta fara karya lagon 'yan ƙwadago'
Tsohon ɗn gwagwarmayar ya sake shaida mana cewa " gwamnatin shugaba Buhari ce ta fara karya lagon ƙungiyar kwadago sakamakon yadda gwamnati ta zuga 'yan ƙasa da ka da su biye wa matakan da ƙungiyar ta dauka a lokacin duk da irin matsin rayuwa da na tsaro da suka kasance a ciki a lokacin.
Ka ga kenan idan aka bi ta ɓarawo sai a bi ta ma-bi-sahu. Da a ce tun lokacin Buhari 'yan ƙasa sun bai wa ƙungiyar ƙwadago haɗin kai da yanzu ƙungiyar na da ƙarfinta irin na da."
Dalilai huɗu da suka ragewa ƙungiyar ƙwadago ƙarfi

Tsohon ɗan ƙungiyar ta ƙwadago wanda ba ya son a ambaci sunansa ya lisafa dalilai guda uku da ya ce su ne suka janyo wa ƙungiyar rauni a Najeriya.
Rashin kataɓus daga jam'iyyun adawa: A duk duniya, abin da ke ƙara wa ƙungiyoyin ƙwadago gwiwa bayan ’yan ƙasa su ne jam'iyyun adawa wajen yi wa gwamnati matsin lamba kan wasu matakai da take ɗauka waɗanda ka iya jefa rayuwar 'yan ƙasa cikin wani hali. "Idan ka duba yanzu a Najeriya tamkar babu jam'iyyun adawa, illa dai lokaci zuwa lokaci za ka ji Atiku Abubakar ko Peter Obi sun ɗan yi suka sai kuma su noƙe."
Tasirin ƙabilanci da addini: Sau da dama kan ƴan Najeriya kan rabu a duk lokacin da ƙungiyar ƙwadago ta kira zanga-zanga ko kuma wasu matakan yi wa gwamnati matsin lamba, "za ka ga idan shugaba daga arewa yake sai 'yan arewa su ce ai ana yi ne domin a kwace mulki daga hannun ɗan arewa. Haka idan Musulmi ne ko Kirisita ko kuma daga kudanci.
Rashawa da cin hanci: Duk da cewa duk wanda zai maganar rashawa da cin hanci sai dai ya yi zargi amma masu sharhi da dama ciki har da 'yan ƙungiyar ƙwadagon da BBC ta tatauna da su sun sha faɗin cewa matsalar rashawa ta taimaka wajen gurgunta ƙungiyar ƙwadago a Najeriya.
"Ai yadda rashawa da cin hanci suka shiga kowanne fanni na rayuwa kamar asibiti da kotu da jami'a da ɗakin watsa labarai da ofisoshin aiki hakan ka iya faruwa da ƙungiyar ƙwadago tunda dai su ma ai 'yan Najeriya ne. Ba daga wata duniyar suke ba." In ji tsohon ɗn ƙwadagon.
Amfani da matakan shari'a: Gwamnatoci sun sha zuwa kotu domin neman alkali ya dakatar da shirin yajin aiki da kungiyar ƙwadago ke shirin yi. "Ka ga wannan ma babbar matsala ce da ke ragewa ƙungiyar ƙarfi.
To sai dai daga ƙarshe masu fashin baƙin sun ce idan dai har kungiyar ƙwadago ta iya ɗaukar matakin da ya samar da mafita ga 'yan Najeriya to lallai 'yan ƙasa za su samu ƙwarin gwiwa kan ayyukan kungiyar ta ƙwadago wadda ita kaɗai ta ragewa 'yan Najeriya.
yanzu dai abin jira a gani shi ne wane tasiri matakin zanga-zanga kan ƙarin kuɗin lantarki da gwamnatin ta yi, zai yi. Kuma hakan ne zai bai wa 'yan Najeriya ƙwarin gwiwar da kungiyar ke nema daga wurinsu.











