Hotunan Afirka na mako: Daga 19 zuwa 25 ga watan Agustan 2022

Wasu ƙayatattun hotuna daga sassan Afirka a wannan makon:

.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Masu ibada na dosar kogin Saint George ranar Litinin...
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A Ethiopia, wajen ibada mai tsarki a Lalibela, ɗaya ne daga cikin wurare da dama da ke maraba ga mata zalla a bikin Ashenda domin tunawa da mahaifiyar Yesu.
.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ana gudanar da bikin Pollera Congo a Panama da ke Tsakiyar Amurka...
.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Bikin ya samu matsayi na wuraren tarihi daga Unesco shekaru hudu da suka gabata bayan gwamnatin Panama ta ce tana son "tabbatar da cewa al'adun Congo da wasu sassan Afirka sun ɗauki wani salo na daban a kowace ƙasa ta Amurka".
.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Dubban mutane a sassan Afirka ta Kudu sun fantsama titunan ƙasar ranar Alhamis domin gudanar da zanga-zangar gama-gari kan tsadar rayuwa.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Magoyin bayan Jam'iyyar hamayya ta Angola Unita yana warware tutar jam'iyyar ranar Litinin, kwanaki biyu kafin babban zaɓen ƙasa...
.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wata mai sayar da biredi tana wucewa ta gaban ƴan sanda a Luanda, babban birnin Angola, kwana guda bayan kammala kaɗa ƙuri'a.
.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ƙananun ɓutumɓutumi kan raƙuma yayin tseren raƙuma a Masar ranar Talata. An ga raƙuma fiye da 900 da suka fito daga sassa daban-daban na ƙasar a taron da aka yi a El Alamein.
.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ranar Laraba, Wani mutum ya yi amfani da ƙaho a matsayin mayen-ƙarfe da ya riƙe tuta yayin Ranar Tuta a Liberia.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ɗan wasan zamiyar teku na Afirka ta Kudu, Jordy Smith na fafatawa a gasar Tahiti Pro 2022 a tekun Pacific ranar Juma'a.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Yadda magoya bayan dan takarar Shugaban Ƙasa Raila Odinga suka gudanar da zanga-zangar ƙin amincewa da sakamakon zaɓen da hukuma ta sanar wanda fiye da rabin kwamishinonin zaɓen Kenya suka ƙalubalanta a gaban kotu.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wannan matar ɗaya ce daga cikin ɗaruruwan da suka ɗaiɗaita bayan da wutar daji ta lalata garuruwa da ƙauyukan Algeria har zuwa lokacin da aka kashe ta ranar Juma'a...
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Sama da mutum 80 sun mutu a wasu yankunan Sudan inda aka samu ambaliyar ruwa. A ranar Litinin kuma, an ga yadda mutane ke hawa jaki domin tsallake fadama a garin Iboud.
.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ranar Asabar ne a Tunisia, mawaƙiya Sherine Abdel Wahab ƴar Masar ta hau mumbari tana rera waƙoƙinta a wani bikin waƙoƙi na duniya.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Tawagar ƙawayen amarya na tattaunawa yayin ɗaukar hoto a gaban teku a Luanda, babban birnin Angola ranar Lahadi.
.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A irin wannan rana a Netherlands, Fitaccen mawaƙin Najeriya Burna Boy ya nishadantar da mutane a bikin Lowlands.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kwana guda kafin a naɗa sabon Sarkin Zulu a Masarautar KwaKhangelamankengane da ke Lardin Kwazulu-Natal a Afirka ta Kudu.
.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A ranar Juma'a kuma, mutane ne suka yi dafifi wajen wata jana'iza a Offa da ke jihar Kwara a Kudu maso Ymamacin Najeriya. A wajen al'adun Yarabawa, mutuwa ba ita ce ƙarshen rayuwa ba amma sauyi ne zuwa wani tsarin rayuwa na daban.