Anya tallafi na kaiwa ga 'yan Ethiopia kuwa?

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Ethiopia ta ce suna samun tallafi sosai a Tigray, inda miliyoyin mutane ke cikin bukatar gaggawa.
A farkon wannan wata, gwamnati da 'yan tawaye a yankin Tigray suka amince su tsagaita wuta a wani bangare na kawo karshen yakin shekaru biyu.
Sai dai anya tallafin na isa ga yankunan mabukata?
Me gwamnatin Ethiopia ta ce?
Redwa Hussein, mai bayar da shawara kan harkokin tsaro ga Friminista Abiy Ahmed, a ranar 11 ga watan Nuwamba ya ce suna samun ‘tamaiko sosai sama da ko-da-yaushe’.
Ya ce wannan ya kunshi manyan motoci 35 makare da kayan abinci da motoci uku da ke dauke da magunguna zuwa garin Shire da ke lardin Tigray.
Ya kara da cewa an shigar da kayayyakin tallafi yankunan da ba wai kadai ke hannun dakarun Ethiopia ba, har yankunan da baya karkashin ikonsu na samun tallafi.
Ya kuma ce babu wani batun tsaiko ko akasi da ake samu kan batun shigar da tallafi.
Mista Redwan daga baya ya shaida wa Reuters cewa motoci 35 da yake batun an kai su Shire na gwanatin Ethiopia ne, sannan na kasashen ketare zai soma shigowa kowanne lokaci daga yanzu.
Shire ya fada karkashin ikon dakarun gwamnati a ‘yan kwanakin nan.
Mun nemi karin haske daga Mista Redwan kan ko tallafin ya isa ga wasu yankunan, sai dai har yanzu bai ce komai ba.
Wata sanarwar gwamnati da aka fitar kwana guda bayan abin da Mista Redwan ya wallafa a shafin Tuwita, na cewa ana iya kokarin wajen ganin an shiga da kayan tallafi yankunan Tigray da dama da ke karkashin mayakan ENDF -[Ethiopian National Defence Forces].
Mene ne martanin Tigraya?

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar TPLF ta ‘yan Tigray ta ce batun da gwamnati ke yi kan kawo tallafi ba gaskya ba ne.
Getachew Reda na kungiyar ya shaida wa BBC cewa har zuwa ranar 13 ga watan Nuwamba, babu wani tallafi da ya shiga yankin Tigray.
Yana wannan maganar ne a matsayin martani kan sakon da aka wallafa a shafin Tuwita na wani wakilin TPLF Kindeye Gebrehiwot: “Mutanenmu na ci gaba da bukatar tallafi ba tare da tsaiko ba a cikin gaggawa…Muna fatan ganin an cika alkaura!”
A wani taron manema labarai a ranar 12 ga watan Nuwamba a babban birnin Kenya, Nairobi, bangarorin biyu sun hadu domin amincewa da yarjejeniyar zaman lafiyar, tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo da ke shiga tsakani, ya ce ya kamata tallafin ya soma isa garesu tun a “jiya”.
"Ya ce a gaggauce za a shigar da tallafi ba tare da wani tsaiko ko jinkiri ba, a cewarsa, lokacin da BBC ke masa tambaya.
Me kungiyoyin agaji ke cewa?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce jeren gwanon motoci dauke da magunguna ya isa Mekelle, birnin yankin Tigray, a ranar Talata kuma ana sa ran kari na da ‘yan kwanaki masu zuwa.
Kafin wannan lokaci, tun ranar 22 ga watan Agusta rabon da aka shiga da kayan agajin Majalisar Dinkin Duniya Tigray wanda ke ratsawa ta yankin Afar mai makwabtaka da birnin Mekelle.
Sannan a ranar 23 ga watan Agusta an shigar da kayan agaji ta jirgin sama Mekelle daga Addis Ababa.
Sama da mutane miliyan biyar ke fama da yunwa a Tigray a wannan lokaci, a cewar shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya.
Mun tuntubi Majalisar, da ke gudanar da ayyukanta a Tigray, domin samun bayanai ko kayan tallafin RedCross ko wata kungiyar agajin kasa da kasa ya isa yankin.
“Mu tare da sauran kungiyoyin agaji, na ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin dawo da ayyukan agaji a Tigray,” a cewar kakakin sashin ayyukan agaji na Majalisar Dinkin Duniya.
"Kungiyoyi agaji a shirye suke so soma rarraba kayayyakinsu cikin sa’o’i 48 zuwa 72 bayan samun amincewar hakan.”
Wannan na nufin kawo yanzu, ba a amince wa tawagar Majalisar Dinkin Duniya ba da za ta yi amfani da jirage wajen kai tallafi Tigray.
Sannan ikirarin cewa mahukuntan Ethiopia sun shigar da kayan agaji yankunan da gwamnati ta kwace na Shire, ma’aikatan agaji na yankin sun yi watsi da batun.
"Babu wani tallafi da aka bari a shigar birnin Shire,” a cewar wani ma’aikacin agaji.
Yaushe tallafi ya isa Tigray?
Shigar da kayan agaji yankin Tigray a wadace ya kasance babban kalubale tun lokacin da yaki ya barke a watan Nuwamban 2020.
Akwai lokacin da kungiyoyin agajin kasa da kasa sai cikin watan Yuli zuwa Disamba 2021 da tsakanin Afrilu zuwa Agusta 2020 ke samun damar kutsawa.
Amma kuma akwai watanni da kwata-kwata aka tsayar da damar kai tallafi da amincewa ma’aikata shiga yankin sakamakon yadda manyan hanyoyi suka datse saboda yaki, sannan an lalata hanyoyi da rufe manyan tittuna.
Tsaiko wajen amince wa ma’aikatan agaji ratsawa ta tittunan yankin da ke hannun gwamnatin tarayya da jihohi ya kasance babbar matsala.
Gwamnati ta kuma bijiro da matakai masu tsauri kan kai kayayyakin agajin ta jirgi – da kuma bukatar cewa dole duk wani kaya sai an soma kawo su birnin Addis Ababa an yi bincike.











