An gayyaci Yarima Bin Salman zuwa Birtaniya, cewar majiyar gwamnati

Bn Salman

Asalin hoton, Reuters

An gayyaci yariman Saudiyya mai jiran gado, Mohammed Bin Salman zuwa Birtaniya, a cewar wata majiyar gwamnati.

Fadar firaministan Birtaniya ta Gini mai Lamba 10 ta ce za su ba da tabbaci a kan tattaunawar da zai yi da firaminista ta hanyar da aka saba.

Sai dai wata majiyar gwamnati daban ta ce babu dalilin da zai sa a yi tunanin cewa ziyarar ba za ta yiwuwa.

Idan ta tabbata, ita ce ziyara ta farko tun bayan kisan gillar da aka yi wa an jarida Jamal Khashoggi a ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Istanbul a 2018.

Jaridun Financial Times da the Times ne suka fara bayar da rahoton wannan ziyara ta Yarima Bin Salman.

Ƙasashen Yamma sun yi tofin Allah-tsine a kan kisan gillar da aka yi wa Jamal Khashoggi, mai sukar gwamnatin Saudiyya a lokacin.

Ministocin Birtaniya sun ce an aikata kisan ne ta hanyar "ƙeta mai tayar da hankali" inda daga bisa suka sanya takunkumi a kan 'yan Saudiyya 20 da ke da hannu a kisan.

Hukumomin leƙen asirin Amurka sun ƙarƙare da cewa yariman jazaman shi ne ya ba da izinin aikata kisan, duk da yake ya musanta duk wani hannu a ciki.

An kuma faɗa wa BBC cewa Saudiyya tuni ta fara shirye-shirye kan wannan ziyara aƙalla tsawon wata ɗaya da ya wuce.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mai yiwuwa ne ziyarar za ta gudana a cikin watan Oktoba, ko da yake zuwa yanzu ba a sa rana ba.

'Yan jam'iyyar Liberal sun soki lamirin wannan ziyara, inda suka ce ziyarar tana aika wata manuniya cewa yarima mai jiran gadon "na iya ci gaba da yin gatsalinsa kuma mu da abokan ƙawancenmu, ba za mu yi komai ba".

Mai magana da yawun harkokin waje ta jam'iyyar Layla Morgan na cewa: "abu ne da ya shallake hankali a ce Rishi Sunak ya shimfiɗa dardumar karɓar Mohammed bin Salman.

"Wannan mutumin - wanda ya ba da izinin aikata kisan ƙeta ga Jamal Khashoggi kuma ya jagoranci tarihin kare 'yancin ɗan'adam na ƙasƙanci - bai kamata ya samu kyakkyawar karɓa daga gwamnatin Birtaniya ba."

Ƙungiyar Amnesty International, mai rajin kare 'yancin ɗan'adam ta yi kira a ɓullo da wata sabuwar hanyar tunkarar alaƙa da masarautar "wadda ta ƙunshi wani matsayi da zai kasance a kan wata ƙa'ida mai tsauri game da mummunan tarihin kare haƙƙin ɗan'adam ɗin Saudiyya".

Saudi Bn Salman

Asalin hoton, Getty Images

Ministocin Birtaniya sun nuna sha'awar ƙarfafa danƙon zumunci da masarautar Saudiyya a watannin baya-bayan nan. Ƙasar dai ta buɗe wani ofishi a London don asusun zuba jarin fam tirliyan ɗaya da nufin baza komar tattalin arziƙi maimakon dogaro kacokan a kan man fetur.

Tun a farkon wannan shekara, lokacin da yake riƙe da muƙamin sakataren kasuwanci, Grant Shapps ya gudanar tattaunawa da Saudiyya a kan ƙara ƙulla ƙawance a ɓangarori kamar binciken sararin samaniya da fasahohin ƙere-ƙere da muhimman ma'adanai.

Gwamnati tana kuma duba hanyoyin tallafa wa wata yarjejeniyar kasuwanci da Majalisar bunƙasa ayyukan haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Gulf. Sakatren harkokin wajen Birtaniya James Cleverly a baya-bayan nan ya kai ziyara zuwa Qatar da Kuwait da kuma Jordan.

Shi ma firaministan wancan lokaci Boris Johnson ya gana da yarima mai jiran gado na Saudiyya a Riyadh bara, a wani ɓangare na tattaunawa da shugabannin yankin Gulf game da katse dogaro a kan man fetur da iskar gas ɗin Rasha.

Sai dai ya ƙi amsa gayyata don halartar jana'izar Sarauniya a watan Satumba, inda ya wani babban jami'in Saudiyya ya je a madadinsa. Ziyararsa ta ƙarshe a Birtaniya, ita ce ta watan Maris ɗin 2018, lokacin da Theresa May take mulki, wata shida kafin kashe Khashoggi.