Saudiyya ta gayyaci mutum 50,000 zuwa gasar kiran sallah da karatun Alƙur'ani

Asalin hoton, @MAKKAHREGION
Saudiyya ta yi wa fiye da mahadatta Alƙur'ani 50,000 daga kasashe 165 rajistar halartar gasar karatun Alƙur'ani da na kiran sallah wadda aka bude ranar 4 ga watan Janairu.
Wannan ne karo na biyu da ake yin gasar, inda jami'ai suka fara da tantance mahaddatan da sauran waɗanda suka shiga gasar domin zaɓo waɗanda suka cancanci zuwa mataki na gaba.
Wannan ce gasa irinta mafi girma a faɗin duniya.
Hukumar kula da harkokin Nishadi ta Saudiyya wato General Entertainment Authority (GEA) ce ke shirya gasar wadda za ta raba wa waɗanda suka yi nasara kyaututtukan da suka kai riyal miliyan 12 jimilla.
Dukkan wadanda suka shiga gasar za su fuskanci matakai har guda huɗu, inda uku cikinsu na latironi ne, wato za a yi amfani da wani shafin intanet ne domin masu bibiyar gasar su zaɓi waɗanda suka fi nuna hazaƙa.
A mataki na huɗu kuwa, za a gabatar da su ne a gaban wasu alkalai da kuma 'yan kallo yayin wani shirin talabijin mai suna Otr Elkalam Show, wanda za a rika haska bangarorin shirin yayin watan Ramadana a tashar talabijin ta MBC.
Gasar Otr Elkalam ta kasance ta farko irinta a duniya kan samar da kwararrun masu kira'ar Alƙur'ani da kuma masu kiran sallah a lokaci guda.











