Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wani kamfani daga Amurka ya sayi Inter Milan
Kamfanin hannun jari daga Amurka, Oaktree ya mallaki Inter Milan, bayan da masu kungiyar Suning daga China suka kasa biyan bashin £336.5m.
Oaktree ya sanar da cewar ranar Laraba ya mallaki Inter Milan, wadda ta lashe Serie A na kakar nan, bayan da Suning ya kasa biyan bashin da wa'adin da ka gindaya 21 ga watan Mayu ya cika.
Suning, wanda ya sayi ƙungiyar a 2016 ya sallamar da jan ragamar Inter Milan kwana uku da Simon Inzaghi ya lashe babban kofin Italiya na kakar nan.
''A matsayin mu da muka mallaki Inter mun kwan da sanin yadda kungiyar take da mahimmaci ga al'ummar birnin da tarihin dake tatttare da ita,'' in ji darakta Alejandro Cano a wani jawabi da aka fitar.
Oaktree ya ce ya samar da kudin da Inter za ta ɓukata tun cikin watan Mayu, domin ta samu damar taka rawar gani da gudanar da ita, har da na sayen fitattun ƴan ƙwallo.
Ranar Asabar a wata wasika da shugaba, Steven Zhang ya yiwa magoya baya - mai shekara 32 ɗan gidan wanda ya mallaki Suning, Zhang Jindong - ya ce ya yi ta kokarin cimma yarjejeniya da Oaktree, amma hakan bai yiwuwa.
Inter ta lashe Serie A na 20 jimilla tun kan kwana biyar a kare kakar bana, bayan da ta doke AC Milan abokiyar hamayyar a cikin watan Afirilu.