Chelsea za ta sha gaban Newcastle kan Joao Pedro, Liverpool na son Guehi

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea na shirin yi wa Newcastle karen tsaye wajen ɗaukan ɗanwasan Brighton da Brazil Joao Pedro mai shekara 23. (Sun)
Ɗanwasan Chelsea da Ingila Noni Madueke mai shekara 23 na haskawa a wajen ƙungiyoyi da dama a wannan bazara har da Arsenal. (Telegraph - subscription needed)
Har yanzu Liverpool ba ta samu tayi ba kan ɗanwasan Uruguay Darwin Nunez mai shekara 25 wanda shi ne ɗanwasan firimiya a baya-bayan nan da ake alakantawa da komawa zakarun Serie A, Napoli. (Liverpool Echo)
Liverpool ta zaƙu ta ɗauko ɗanwasan Crystal Palace Marc Guehi mai shekara 24. (Daily Mail)
Nottingham Forest na dab da kammala yarjejeniyar fam miliyan 30 don sayen ƴanwasan Botafogo Igor Jesus mai shekara 24 da Jair Cunha mai shekara 20. (Telegraph - subscription needed)
Ɗanwasan Sporting da Sweden Viktor Gyokeres mai shekara 27 ya kusa koma wa Arsenal a maimakon Manchester United. (Talksport)
Ana sa ran ɗanwasan Bayer Leverkusen da Jamus Florian Wirtz mai shekara 22 zai kammala shirye-shiryen koma wa Liverpool a ranar Juma'a. (ESPN)
Brighton ta karɓi tayin fam miliyan 25.6 daga Napoli kan ɗanwasan tsakiya na Denmark Matt O'Reily mai shekara 24. (Sky Sports)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Napoli da AC Milan na sha'awar ɗauko ɗanwasan Liverpool da Italiya Federico Chiesa mai shekara 27. (Kiss Kiss Napoli - in Italian)
Sunderland na son ɗaukan tsohon ɗanwasan Southampton Duje Caleta-Car daga Lyon. Ɗanwasan na asalin Croatia mai shekara 28 ya taka leda sau 13 a kakar firimiya ta 2022 zuwa 2023. (Newcastle Chronicle)
Everton ta soma tattaunawa da ɗanwasan Ingila Jarrad Branthwaite. Shekaru biyu suka rage wa ɗanwasan mai shekara 22 a kwantiraginsa na yanzu sai dai David Moyes na son ya tsawaita zamansa a ƙungiyar. (Liverpool Echo)
Ana sa ran ɗanwasan tsakiyar Ghana Thomas Partey mai shekara 32 zai bar Arsenal ranar 30 ga Yuni yayin da ba a samu wani ci gaba ba a tattaunawar sabunta kwantiraginsa. (ESPN)
Ɗanwasan Borussia Dotmund Jamie Gittens mai shekara 20 ya shirya koma wa Chelsea a wannan bazara kuma shi ne babban ɗanwasan da suke zawarci. (Standard)
Manchester United na jiran gani ko akwai yiwuwar sayen ɗanwasan Bayern Munich da Portugal, Joao Palhinha mai shekara 29, a matsayin aro bayan da ta yanke shawarar ƙin kashe maƙudan kuɗi kan ɗanwasan Atalanta ɗanwasalin Brazil Ederson mai shekara 25. (Givemesport)
Crystal Palace da Leeds United da West Ham na zawarcin ɗanwasan Liverpool Joe Gomez mai shekara 28 kuma ƙungiyarsa a shirye take ta sakar masa marar barin ta. (TBR Football)
Napoli da Inter Milan nasha'awar ɗauko kan ɗanwasan Poland Antoni Burkiewicz mai shekara 17 daga Rakow Czestochowa. (Teamtalk)














