Gyokeres zai bar Sporting, Liverpool ta shirya karya tarihin sayen ɗan wasa a Premier

Asalin hoton, Getty Images
Ɗanwasan da Arsenal da Manchester United ke zawarci Viktor Gyokeres mai shekara 27 ya ƙi ya tattauna da Sporting inda kuma ya yi barazanar yajin aiki yayin da yake ƙoƙarin tilasta barin kulob ɗin na Portugal. (Mirror)
Fulham ta yi watsi da tayin fam miliyan 26 da ƙarin fam miliyan shida daga Leeds kan ɗanwasan Brazil Rodrigo Muniz mai shekara 24. (Standard)
Sai dai Fulham na duba yiwuwar sayen Ricardo Pepi na ƙungiyar PSV Eindhoven da Amurka wanda ƙungiyoyi da dama na Sifaniya da Italiya ke farautar shi. (Fabrizio Romano)
Ɗanwasan Arsenal Myles Lewis -Skelly na gab da sa hannu kan sabon kwantiragi da zai sa ɗanwasan mai shekara 18 ɗan asalin Ingila ya zama ɗaya daga cikin matasan ƴan wasa da aka fi biya a duniya. (Athletic - subscription required)
Sai dai mataimakin kocin Arsenal Carlos Cuesta na dab da ficewa daga Arsenal domin karɓar matsayin koci karon farko a ƙungiyar Parma ta Serie A. (Guardian)
Chelsea na nan kan bakarta ta son ɗaukan ɗanwasan tsakiya na Ingila Morgan Rogers mai shekara 22 idan Aston Villa ta shirya cefanar da shi. (Mail+ - subscription required)
Liverpool ta shirya karya tarihin cinikin ƴanwasa a Birtaniya don sayen ɗanwasan Newcastle da Sweden Alexander Isak mai shekara 25 a wannan bazara. (GiveMeSport)
Aston Villa a shirye take ta sefanar da ɗanwasan tsakiya Emi Buendia mai shekara 28 idan ta samu tayin da ya zarce fam miliyan 20 kan ɗanwasan. (Caught Offside)
Chelsea ta tuntuɓi Brighton game da ɗanwasan Brazil Joao Pedro mai shekara 23, wanda ita ma Newcastle ke zawarcin shi. (Fabrizio Romano)
Brentford ta yi wa ɗanwasanta Yoane Wissa farashi - fam miliyan 50 yayin da ɗanwasan na Jamhuriyar Congo mai shekara 28 ya zama wanda Nottingham Forest da Tottenham da Arsenal da Fenerbahce da Galatasaray ke zawarci. (Teamtalk)
Tauraruwar ɗanwasan Nice da Ivory Coast Evann Guessand mai shekara 23 na haskawa a wajen Leeds da Tottenham waɗanda suka tuntuɓi wakilan ɗanwasan. (TBR Football)
Golan Ingila Nick Pope mai shekara 33 ba ya san barin Newcastle duk da zawarcinsa da Leeds take, ma'ana ƙoƙarinsu na sayen ɗanwasan Burnley James Trafford mai shekara 22 na iya fuskantar cikas. (TBR Football)













