Ƙungiyoyin Saudiyya na zawarcin Son, Napoli na son Sancho

Son Heung-min

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Son Heung-min
Lokacin karatu: Minti 2

Ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Saudiyya - Al-Ahli da Al-Nassr da Al-Qadsiah suna sha'awar ɗan wasan gaba na Koriya ta Kudu da Tottenham Son Heung-min, mai shekara 32 inda kowane kulob a shirye yake ya biya fam miliyan 34 domin sayen shi. (Talksport)

Bayern Munich za ta ƙyalle ido kan ɗan wasan Brighton da Japan Kaoru Mitoma mai shekara 28 da ɗan wasan Liverpool da Netherlands Cody Gakpo mai shekara 26, idan suka rasa Nico Williams mai buga wa Sifaniya da Athletic Bilbao mai shekara 22. (Sky Germany)

Manchester United ta amince ta ƙulla kwantiragin shekara ɗaya da golan Ingila Tom Heaton domin ɗanwasan mai shekara 39 ya ci gaba da zama a Old Trafford. (Fabrizio Romano)

Ɗan wasan Bournemouth da Ingila Max Aarons mai shekara 25 ya zama wanda Rangers take zawarci inda ƙungiyar ke neman sayen shi a matsayin ɗanwasan dindindin a maimakon na aro. (Daily Record)

Ɗanwasan Chelsea Zak Sturge mai shekara 21 na gab da koma wa Millwall a matsakin dindindin bayan ƙwazon da ya nuna a kakar bara lokacin da yake a matsayin aro. (Daily Express)

Trabzonspor na ƙyalle ido kan ɗan wasan Ipswich Town da Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo Axel Tuanzebe mai shekara 27. (Takvim – in Turkish)

AC Milan ta gana da wakilan ɗanwasan Bayer Leverkusen da Switzerland Granit Xhaka mai shekara 32. (Football Italia)

Napoli na ƙoƙarin sayen ɗan wasan Manchester United Jadon Sancho mai shekara 25 bayan rashin nasarar da ya yi a Chelsea a matsayin ɗanwasan aro. (Gianluca di Marzio - in Italian)

Nottingham Forest na sha'awar ɗan wasan Colombia da Palmeiras Richard Rios, mai shekara 25 wanda kwantiraginsa ta ƙunshi kuɗi na kusan fam miliyan 85. (Give Me Sport)

Leeds United da Aston Villa sun kafa sun tsare a zawarcin ɗan wasan Strasbourg da Senegal Habib Diarra mai shekara 21. (Sports Mole)