Mbuemo na sha'awar komawa United, Walker ya amince da tayin Everton

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan gaban Brentford da Kamaru Bryan Mbeumo, mai shekara 25, ya fi karkata kan zuwa Manchester United a madadin Tottenham Hotspur, duk da cewa tsohon kocinsa Thomas Frank ya koma ƙungiyar ta arewacin Landan. (Sky Sports News)
Ɗan wasan bayan Manchester City da Ingila Kyle Walker, mai shekara 35, ya amince ya koma Everton kan kwantiragin shekara guda. (Sun)
Newcastled United ta tuntuɓi Brighton kan sayen ɗan wasan gaban Brazil Joao Pedro, mai shekara 22, kuma tana sha'awar ɗan wasan Sporting Lisbon da Ivory Coast Ousmane Diomande, mai shekara 21. (Telegraph)
Manchester United ta fara tattaunawa da Eintracht Frankfurt kan cinikin ɗan wasan gaban Faransa Hugo Ekitike, mai shekara 22, amma har yanzu ba a kai ga cimma matsaya ba (Sky Sports)
Juventus ta yi wa ɗan wasan gaba na Sporting Lisbon, Viktor Gyokeres tayin albashin fam miliyan 11 duk shekara yayin da s ta ke ƙoƙarin doke Arsenal da Manchester United kan cinikin dan wasan na Sweden mai shekara 27. (Mirror)
Napoli na shirin sayen ɗan wasan Manchester United da Argentina Alejandro Garnacho, mai shekara 20, ko kuma ɗan wasan tsakiya na Manchester City da Ingila Jack Grealish, mai shekara 29, amma zakarun na Italiya na son kashe fam miliyan 45 kacal. (Sun)
Atletico Madrid za ta yi zawarcin ɗan wasan bayan Aston Villa da Faransa Lucas Digne, mai shekara 31, idan ba ta yi nasarar daukar ɗan wasan Scotland da Liverpool Andy Robertson, mai shekara 31 ba. (Times)
Chelsea ta fara tattaunawa da Lyon kan ɗan wasan gaban Belgium Malik Fofana, mai shekara 20, duk da cewa Nottingham Forest ma ta nuna sha'awarta kan ɗan wasan. (L'Equipe)
Golan Barcelona da Jamus Marc-Andre ter Stegen, mai shekara 33, ya yi watsidatayin da zakarun Turkiyya Galatasaray su ka yi masa. (Sport)
Athletic Bilbao da Marseille da Arsenal da Aston Villa, da Inter Milan, da kuma Napoli duk sun nuna sha'awarsu akan ɗan wasan baya na Al Nassr da Sifaniya kuma tsohon ɗan wasan Manchester City Aymeric Laporte, mai shekara 31 (AS)
Liverpool ta bi sahun Manchester United da Chelsea da kuma Newcastle wajen zawarcin ɗan wasan gaban Southampton Tyler Dibling mai shekara 19 (CaughtOffside)
Tottenham na shirin fara tattaunawa da Rennes kan ɗan wasan Faransa Arnaud Kalimuendo, mai shekara 23. (L'Equipe)










