Cigaban mai haka rijiya aka samu a shekaru biyun Tinubu - Buba Galadima

Asalin hoton, OTHERS
Jigo a jam'iyyar hamayya ta NNPP, a Najeriya, Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa ba wani abin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kawo wa kasar illa cigaban mai haka rijiya.
Dansiyasar yana mayar da martani ga jawabin da shugaban kasar ya yi a ranar Alhamis, 29 ga watan Mayu, 2025, ranar da gwamnatinsa ta cika shekara biyu a kan mulki.
A jawabin nasa, Shugaba Tinubu ya ce, gwamnatinsa ta samu nasarori da dama musamman a tattalin arziƙin ƙasa da inganta tsaro da rage cin-hanci da rashawa da kuma fitar da ɗumbin al'ummar ƙasar daga talauci, tare da rage dimbin bashin da ake bin Najeriya.
A tattaunawar da Buba Galadiman ya yi da BBC, inda yake martani ga kalaman shugaban, na cewa gwamnatinsa ta samar da cigaba ta fannoni da dama.
''Mu ba mu ga komai ba – mun ga cibaya domin abin da naira goma za ta saya ma a da yau naira dubu ma ba za ta iya saya maka ba,'' in ji jigon na NNPP.
Ya ce, idan aka yi waiwaye a baya darajar naira a kan dala za a ga cibayan a zahiri, kasancewar a yanzu dala daya tana daidai da naira 1650.
Ya kara da cewa : ''Idan gwamnati ta ce tattalin arzikin kasar ya habaka, dala ta zama naira 1650, shin naira 1650 me za ta iya saya maka? Wannan ita ce magana.''
Dangane da farashin kayan abinci da gwamnatin ke cewa ya sauko, wanda take alfahari da hakan a matsayin cigaban da zai saukaka wa talaka rayuwa, dansiyasar ya ce wannan ma ba abu ne da za a yi murna da shi ba.
Ya ce: ''Ka san kowa da nashi ilimin, na yarda da maganar gwamnati cewa farashin abinci – shinkafa, alkama, masara ya yui kasa. Amma kai ka san abin da zai biyo baya?''
Ya ce abin da zai kasance a nan gaba shi ne, ''yanzu na kori manoma daga gona ba za su sake komawa gona ba bana saboda matsalar tsaro, in ba su koma gonar ba dole su ci abinci, to kuma ba su da kudin da za su iya sayen abincin komin araharsa, saboda haka sata da fashi za su shiga.''
Ya kara bayani da cewa duk da yadda farashin kayan abinci ya sauka a halin da ake ciki za a kai gabar da manoma ba su da kudin, shi kuma manomin bai yi noma ba, domin buhun masara ba zai iya saya masa taki ba.
Game da ikirarin da gwamnatin ta Tinubu ta yi cewa an samu karin kudade a aljihun gwamnati, Buba Galadiman ya musanta hakan da cewa idan gaskiya ne, to jama'a su gani a kasa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya yi nuni da aikin gini titin gabar teku da ya tashi daga Legas zuwa Kalaba:
''Yanzu an bayar da aikin tiriliyan 16 a kudancin kasar nan, an biya fiye da rabin kudin a soma-tabi, har yanzu ba a yi kilomita talatin ba, kuma kilomita 700 ne, in ka kirga kowane kilomita talatin za a shekara biyu ana yi – a shekara nawa za a yi?'' Ya ce.
Hakazalika shi ma aikin titin Abuja zuwa Kano, ya yi nuni da shi cewa har yanzu ba a gama ba, da cewa duk maganar da gwamnatin ta yi cewa za ta karasa aikin, ya ce soki-burutsu ne kawai.
Dangane da harkar tsaro kuwa, nan ma Buba Galadima ya zargi gwamnatin da gazawa a tsawon mulkin da ta yi na shekara biyu.
''Ka san abin da ke aukuwa a Borno? Kusan rabin kasar Boko Haram ta karbe,'' in ji shi.
Ya kara da cewa, ''ka san abin da ke aukuwa a Katsina da Naija da Sokoto?''
Ya ce : ''Muhimmancin gwamnati shi ne ta kare rayuka da dukiyar al'umma, randa ba ta yi ba nene ne sunanta?''
Injiniya Galadima ya kuma bayar da misali da yadda gwamnatin ta ware naira biliyan goma domin sanya wutar lantarki mai amfani da hasken rana a fadar shugaban na Najeriya, inda ya ce – ''wannan shi ne cigaban da gwamnatin ke cewa ta samar? ''Cigaba ne na mai haka rijiya,'' in ji shi.











