Cuba ta soke bikin Ranar Ma'aikata saboda karancin man fetur

Taron ranar Mayday a Cuba

Asalin hoton, Getty Images

Matsalar karancin mai ta tilasta wa gwamnatin Cuba soke bikin shekara-shekara na ranar ma'aikata ta duniya, wato Mayday.

Biki ne dai wanda a bisa al'ada dubban ma'aikatan gwamnati ke gangami da maci da ake gudanarwa a dandalin Juyin-juya-hali na Revolution Square a babban birnin kasar, Havana.

Gwamnati ce ke samar da motocin da ake dauko ma'aikatan daga sassan daban-daban, to amma a bana sakamakon karancin man fetur shugaban kasar, Miguel Diaz-Canel, ya soke bikin.

Babu wata rana da kasar ta Cuba ke bikinta a tarihinta na juyin-juya-hali kamar wannan rana ta daya ga watan Mayu.

Dubban ma'aikata ne ke gangami a dandalin inda suke nuna goyon baya da jaddada mubaya'arsu a bikin da fareti mai kayatarwa ga shugabancin kasar na tsarin kwaminisanci.

Soke wannan kayataccen biki mai matukar muhimmanci ga kasar ta Cuba, saboda karancin man fetur hakan ya nuna irin tsananin halin matsin tattalin arziki da kasar ta tsibiri take ciki.

Yayin da masu akida ta ga-ni-kashe-ni ta goyon bayan juyin-juya-halin na kasar ke halartar bikin na ranar ma'aikata na Cuba bisa radin kansu, su kuwa ma'aikatan gwamnati da dama daga cikinsu wasu bayanai na nuna cewa ana tilasta musu halartar bikin ne, ta hanyar kai su a motoci domin a ga taron ya yi armashi da yawan jama'a.

Masu ababan hawa kan shafe kwanaki a layin man fetur, kuma kasar ba ta da wadatar kyakkyawan tsarin sufuri na zamani da za ta yi jigilar dubban likitoci da malamai da ma'aikatan gona zuwa wannan dandali a Havana.

Cuba na fuskantar matsalar tattalin arziki mafi muni tun bayan shekarun da suka biyo bayan yakin cacar baka.

Tana fama da tsananin karancin muhimman kayan masarufi, wanda ake ganin rashin tsantseni na gwamnati da kuma takunkumin tattalin arziki na shekara sittin da Amurka ta sanya wa kasar suka haifar.