Biden ya sassauta takunkuman da Trump ya kakaba wa Cuba

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Biden ta Amurka ta sanar da sassauta takunkumai kan Cuba da kara bude wasu ofisoshin jakadanci a tsibirin.
Wannan na nufin dubban 'yan Cuba a yanzu na iya neman bisar yin tozali da 'yan uwa ko iyalai, sannan za a kara yawan jirage da za su ke jigilar fasinjoji tsakanin Amurka da Cuba.
Za kuma a soke tsarin kayyade kudaden kashewa, ko da yake ma'aikatar cikin gida a Amurka ta ce za ta duba hanyoyi tabbatar da cewa kudaden basu da alaka da gwamnatin Cuba kai-tsaye.
Tun lokacin da shugaba Biden ya kama mulki, ana iya cewa babu wani banbamci da aka gani a tsare-tsarensa kan Cuba da mutum da ya gada, Shugaba Trump.
Sai dai a yanzu, ma'aikatar cikin gida ta sanar da cewa za ta sassauta wasu daga cikin manyan takunkumai da gwamnatin tsohon shugaba Trump ta kakabawa Cuba.
Musamman batun kara yawan ofishin jakadanci a Havana, domin bai wa mutane damar samun bisa ko takardun izinin saduwa ko tozali da 'yan uwansu.
Sannan za a janye takunkumin da ke kayyade kudin da za a iya kashewa wato dala dubu daya a cikin wata uku, sannan ana iya zuwa karatu ko ziyara domin samun ilimi.
Akwai kuma bada damar dawo da hada-hadar jiragen fasinjoji da wanda mutum ke iya shata shi kadai har zuwa gaba da Havana.
Sannan gwamnatin Biden ta alkawarta taimakawa masu sana'o'i a Cuba da wani tsari kasuwancin Intanet da Fasahar asusun ajiyar bayanai ta Cloud.
Wannan labari ya daɗaɗawa dubban 'yan Cuba wadanda ke cikin matsuwa domin ganin 'yan uwansu a Florida da wasu sassan birane a Amurka.
Tsibirin ya fusankanci wani mumunan yanayi da kwarara ko hijirar mutane irinsa mafi girma tun soma yakin cacar-baka, 'yan kasar da dama na balaguro zuwa Nicaragua, sannan su shiga tsakiyar Amurka don isa iyakar Amurka ta Mexico.
Bayan shekara ta 2016, gwamnatin Trump a wancan lokacin ta bijiro da sabbin takunkuman karayar tattalin arziki kan tsibirin da masu ra'ayin kwamunisanci ke mulki, bayan tsohon shugaban Obama ya sassauta musu irin wadannan takunkumai a baya.
Matsalolin annobar korona da suma suka yi tasiri ga tattalin arziki da kuma rashin tsari ko almubazaranci da kudaden al'umma, tattalin arzikin Cuba ya shiga tsaka mai wuya irinsa mafi muni a shekaru.
Wadannan sauye-sauye kusan somin tabi ne a kokarin da fadar White House ta Amurka a yanzu ke yi wajen daidaita alaka da Cuba a wannan lokaci.











