Majalisar Wakilan Amurka ta amince da ba Ukraine tallafi cikin gaggawa

Asalin hoton, JOE BIDEN
Majalisar Wakilan Amurka ta amince ga gagarumin rinjaye, da gwamnatin kasar ta sake bai wa Ukraine wani taimako na dala biliyan arba'in saboda yakin da take yi da Rasha.
Yawancin 'yan majalisar na jam'iyyar hamayya ta Republican suma sun bi sahun 'yan Democrats wajen bayar da goyon bayansu ga kudurin, wanda ake sa ran su kuma 'yan majalisar dattawa za su hanzarta amincewa da shi, sannan shi ma Shugaba Biden ya rattaba hannu a kai.
Wannan tallafin kudi da majalisar Wakilan ta amince da shi cikin gaggawa da kuma gagarumin rinjaye ba tare da la'akari da bambancin jam'iyya ba, ya dara abin da Shugaba Biden ya gabatar da dala miliyan dubu bakwai.
Za a yi amfani da kudin ne wajen sama wa Ukraine tallafin soji da kuma taimakon fararen hula wadanda kutsen da Rasha ke yi a Ukraine ya shafa.
Yanzu dai za a nufi majalisar Dattawa ne domin su ma 'yan majalisar su amince da shi kafin kuma a nufi fadar shugaban Amurkar, domin shi ma ya sa hannu, a 'yn kwanakin da ke tafe

Asalin hoton, Reuters
Shugabar majalisar wakilan Nancy Pelosi - wadda a baya-bayan nan ta ziyarci, babban birni Ukraine din Kyiv, ta bayyana wa takawarorinta 'yan jam'iyyar Democrat muhimmancin wannan kuduri saboda su gaggauta amincewa da shi.
Ta ce, ''yayin da Putin ya dage ba ji ba gani a yakinsa na ban tsoro da mugunta, tayar da hankali da rashin imani a Ukraine lokaci yana da muhimmancin gaske.
Wannan ne ya sa muka ji dadin cewa za mu iya ci gab kai tsaye da wann kuduri a yau domin ya samu wucewa ga majalisar dattawa, da kum tebrn shugbn ksa, domin taimakon ya kai ga al'ummar Ukraine da gabashin Turai.'' in ji Pelosi.

Asalin hoton, Empics
Su kuwa hukumomin tattar bayanan sirri na Amurkar sun yi gargadin cewa Shugaban Vladimir Putin na Rashar na shirin tsawaita yakin na Ukraine, inda ko da ya yi nasara a gabas ba zai dakata ba.
Hukumoimin sun yi gargadin ne yayin da fada ke kara rincabewa a gabashi, inda Rasha ke kokarin kama yankin.
Rasha ta mayar da hankalin dakarunta wajen kama yankin Donbas bayan mayakan Ukraine sun hana kama Kyiv.
Kuma uk da wannan yunkuri, dakarun Rasha suna nan ba gaba ba baya in ji hukumomin na Amurka.










