Rikicin Ukraine: Duk ƙasar da ta shigar wa Ukraine faɗa ta kuka da kanta - Putin

Asalin hoton, AFP
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yi gargadin cewa duk kasashen da suka shigarwa Ukraine faɗa a yaƙin da take yi da ita za su gamu da abin da ya kira martani cikin sauri kamar ƙiftawar walƙiya.
Da yake magana da 'yan majalisar kasar a birnin Moscow, ya ce Rasha na da manyan matakan da za ta iya dauka idan hakan ta kama.
Shugaban na Rasha ya kara da cewa an riga an yanke hukunci kan abin da martanin zai kunsa, amma bai bayar da wani karin bayani ba.
A ranar Talata Mista Putin ya shaida wa sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres cewa har yanzu yana fatan tattaunawar sulhu da Kyiv za ta yi tasiri.
''Lamarin na iya kai wa ga Yaƙin Duniya na Uku''

Asalin hoton, RMOFA
Ranar Laraba ne ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya sake gargadin cewa akwai hatsarin rikicin Ukraine na iya kai wa ga Yaƙin Duniya na Uku, amma ya ce yana sa ran za a kawo karshensa da yarjejeniyar zaman lafiya.
Da yake magana da kafafen yada labaran kasar Rasha, ya ce Moscow na son kaucewa abin da ya kira hadarin wucin gadi na irin wannan rikici.
Mista Lavrov ya zargi NATO da shiga yakin, yana gargadin cewa kasarsa za ta kai wa tawagar kungiyar da ke kai makamai Ukraine hari ba kakkutawa.
Makonni kadan da suka gabata shugaba Putin ya umarci dakarunsa na nukiliya su kasance cikin shiri.
Amurka ta ce ba ta son shiga rikicin ta hanyar sanya sojojinta a ciki. domin hakan na iya haifar da yakin duniya na uku.











