Harin intanet uku na Rasha da ke firgita ƙasashen yamma

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Joe Tidy
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC kan intanet
Shugaban Amurka Joe Biden ya yi kira ga kamfanoni da hukumomi a Amurka su "toshe ƙofofinsu na intanet", yana mai iƙirarin cewa bayanan sirri sun nuna Rasha na shirin yi wa Amurka kutse ta intanet.
Hukumomin Birtaniya sun goyi bayan kiran da Fadar White House ta yi na "ƙara ɗaukar matakan tsaro na intanet", ko da yake babu wata hujja da ke tabbatar da Rasha na shirin yin kutsen.
Rasha a baya ta bayyana irin wannan zargin a matsayin na "nuna ƙyamar manufofin Rasha."
Amma, Rasha tana da ƙarfi ta ɓangaren intanet da ta mallaki abubuwan da za su iya kutse ta intanet.
Ukraine ba ta fuskanci barazanar Rasha ba ta kutsen intanet amma masana na fargabar cewa Rasha na iya yi wa aminan Ukraine kutse.
"Gargaɗin Biden na iya yiyuwa, musamman yadda ƙasashen yammaci suka sake tsawalla takunkumai, kamar yadda Jen Ellis na kamfanin tsaron intanet Rapid7 ya bayyana.
Ga wasu hanyoyin kutse da ake fargaba.
BlackEnergy - Yin kutse a wasu muhimman ayyuka
Yawancin lokaci ana kwatanta Ukraine a matsayin fagen kutsen Rasha, wadda ta kai hare-hare don yin gwajin dubarunta na kutse da kuma kayan aiki.
A 2015 cibiyar samar da wutar lantarki ta kasar Ukraine ta samu matsala sakamakon wani harin da aka kai ta intanet mai suna BlackEnergy, wanda ya haifar da katsewar lantarki na wani ɗan gajeren lokaci ga masu amfani da lantarkin 80,000, a yammacin Ukraine.

Asalin hoton, Reuters
Bayan shekara ɗaya, wani kutsen na intanet da kae kira Industroyer ya katse lantarki kusan ɗaya bisa biyar a Kyiv, babbarn birnin Ukraine na tsawon sa'a ɗaya.
Amurka da Tarayyar Turai sun ambaci suna tare da zargin sojojin Rasha da alhakin kai harin ta intanet.
"Rasha na iya aiwatar da irin wannan harin kan ƙasashen yammaci a matsayin wani abu na nuna ƙarfinta," a cewar wata masaniyar tsaron intanet ta Ukraine Marina Krotofil da ta taimaka wajen binciken kutsen katsewar lantarki ta bayyana.
"Amma babu wani kutse kan lantarki da ya haifar da rasa samar da lantarkin. aiwatar da hare-haren intanet kan na'urori abu ne mai wahala da kuma cimma tasirin ɓarnar na tsawon lokaci abu ne da ke da wahala saboda matakan kariya. "
Masana kamar Marina sun yi hasashen cewa Rasha na iya mayar da martani, kamar yadda ƙasashen yamma suke da mabuga ga intanet din Rasha.
NotPetya - ɓarnar da ba a iya sarrafawa
NotPetya ana tunanin shi ne kutsen intanet mafi tsada a tarihi kuma hukumomin Amurka da Birtaniya da Tarayyar Turai sun zargi sojojin Rasha da yin kutsen.
Manhajar mai illa tana boye ne a wata manhaja da ake amfani da ita a Ukraine, amma ta bazu a duniya tana lalata kwamfutoci na dubban kamfanoni tare da janyo hasarar aƙalla dala biliyan 10.
Masu kutsen intanet na Koriya ta Arewa ana zarginsu da haifar da illa ta hanyar yin amfani da irin wannan salo na kutse a farkon wata.

Asalin hoton, Webroot
WannaCry wata nau'in matsala ce da ke kama kwamfuta inda ta aka kiyasta ta lalata kamfutoci 300,000 a ƙasashe 150. Matakin ya tilastawa ɓangaren lafiyar Birtaniya soke bayanai da dama na masu son ganin likita.
"Wannan irin harin kan haifar da wata babbar dama da taɓarɓarewar tattalin arziki, wani lokaci ma har da rasa rai," in ji Jen Ellis.
Amma masanin kwamfuta Farfesa Alan Woodward ya ce irin wannan harin na iya tasiri ga Rasha ita ma.
"Irin wannan nau'in harin ya yi kama da makamin yaƙi domin yana da wahala ya kasance an kai wani wuri shi kadai. WannaCry da Notpetya ya shafi wasu a Rasha ma."
Bututun mulkin mallaka - Harin intanet da ke ƙaruwa
A Mayun 2021 akwia dokar ta-baci a wasu jihohin Amurka bayan masu kutse ta Intanet sun toshe bututun mai.

Asalin hoton, Getty Images
Bututun Turawan Mulkin Mallaka na ɗaukar kashi 45 cikin ɗari na samar da dizal da man fetur da man jirgin sama kuma samar da shi ya haifar da fargaba a fanfunan iskar gas.
Ba masu satar bayanan gwamnatin Rasha ne suka kai wannan harin ba, amma wata kungiyar DarkSide, wacce ake tunanin tana cikin Rasha.
Kamfanin bututun mai ya amince da biya dala miliyan 4.4 (£3.1m) domin dawo da aikin kwamfutoci.

Asalin hoton, Reuters
Makwanni bayan haka samar da nama ya yi tasiri a lokacin da wata tawaga ta REvil ya kai hari kan JBS, babban mai sarrafa nama a duniya.
Ɗaya daga cikin manyan fargabar da masana ke da shi game da ƙarfin kutsen Rasha na intanet shi ne cewa Kremlin na iya ba da umarni ga kungiyoyin masu aikata laifuka ta intanet da su kai hare-hare a kan Amurka, don dagula lamura.
"Manufar bayar da umarni ga masu kutse shi ne saboda ruɗanin d za su iya haifarwa. Suna iya haifar da mummunar lalacewar tattalin arziki," in ji Farfesa Woodward.
"Haka kuma na tare da ƙarin kari na rashin yarda da cewa wadannan kungiyoyi mataki ne da aka cire daga harin da gwamnatin Rasha ta kai."
Ta ya Amurka za ta mayar da martani?
A wani yanayi da ba zata ba cewa an kai wa ɗaya daga cikin ƙasashen Nato hari na intanet da zai haifar da hasarar rayuka ko kuma mummunar illa, ya kai ga amfani da doka ta biyar ta ƙawancen tsaro.
Amma masana sun ce wannan zai harzuka Nato shiga yaƙin da ba ta yi niyya ba, don haka duk wani martani zai kasance daga Amurka da ƙawayenta.
Shugaba Biden tuni ya bayyana cewa "mun shirya martanin da za mu mayar" idan har Rasha ta ƙaddamar da hari kan Amurka.
Amma abin da aka gani a baya bayan nan a Ukraine a makwanni da suka gabata daga masu kutse a ɓangaorrin biyu da ke yaki ya nuna cewa lamarin zai yi ƙamaru. Don haka duk wani mataki sai an yi taka tsantsan da shi.











