Shin Putin na da karfin fada a ji a yankinsa?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Steve Rosenberg
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Moscow
Ko ka taba kokarin haɗa wani abu wanda babu rabin kayayyakin haɗa shi a ƙasa.
Abu ne mai daure kai da cin rai. Ba za ka taɓa ganin cikakken hoton abin ba kenan.
To kamar yadda wancan yanayin yake, haka siyasar Fadar Kremlin ta ke.
Kokarin gane tunanin da Vladimir Putin ke yi da abin da yake shiryawa abu ne mai daure kai. Kuma haka Fadar kremlin ke son lamarin ya kasance: wato ba ta son kowa ya san inda ta sa gaba.
Shin mene ne shirin da Shugaba Putin ya yi kan kasar Ukraine? Ko Moscow na shirin kai hari ne don mamaye kasar? Ko hari za ta kai na takaitaccen lokaci? Ko kuwa tayar da kura ta ke yi, domin ta tilasta wa wasu kasashe su karkata zuwa wurin da take nuna mu su?
Babu wanda zai iya sanin yawan karfin ikon Rasha a wannan lokacin.
Abubuwan da ke damun kasashen Yamma kan siyasar Rasha sun hada da:
- Akwai sojojin Rasha kimanin 100,000 da ta jibge kan iyakarta da Ukraine
- Jerin rawar dajin da Rasha ta kaddamar a doron kasa da kuma a teku
- Wani atisayen soji da Rasha ta shirya yi da kasar Belarus
- Yadda Fadar Kremlin ke kafa wasu sharuddan da ta san Amurka ba za ta amince da su ba (misali cewa ba ta yarda Ukraine ta shiga kungiyar Nato ba)
- Ikirarin da Shugaba Putin ke yi cewa Rashawa da Ukrainawa "al'umma daya ne"
Amurka ta aika wa Rasha amsa a rubuce kan abubuwan da ta ce ke damunta. Rashar ta ce za ta yi nazarin abubuwan da Amurka ta rubuta cikin wasikar.
A halin yanzu, kasashen na ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya.
"Kada a kuskura a kai kayan yakin Nato a cikin Ukraine. Mun bukaci 'kawayenmu na kasashen Nato da su fice. Ku fice daga cikin yankunanmu. Ku fice daga tsofaffin kasashen tarayyar Soviet, saboda barazana ce ga al'umar Rasha," inji Yevgeny Popov.
Mista Popov, wanda ke gabatar da wani shirin talabijin a tashar talabijin mallakin gwamnatin Rasha, dan majalisa ne kuma da ya fito daga jam'iyyar United Russia mai mulkin kasar.
"Lokaci na kurewa," Mista Popov ya gargade ni. "Tilas ka yanke hukunci cikin hanzari."
"Idan kuma ban yi ba fa?" na tambaye shi.
"To sakamakon da zai biyo baya zai kasance mai matukar hatsari ga duniya baki daya. Wasu jami'an kasashen Yamma na cewa Rasha raguwar kasa ce. Anya kuna son a tabbatar muku da gaskiya ko karyar wannan hasashen?"

Asalin hoton, Reuters
A bainar jama'a, jami'an gwamnatin Rasha na ikirari cewa Nato matsala ce ga tsaron kasar Rasha.
Sai dai kashi 6 cikin 100 na kan iyakar kasashen Nato ne suke iyaka da na Rasha. Kuma Rasha na da dangantaka mai kyau da wasu kasashen da ke mambobin Nato, kamar Italiya da Hungary; kuma a baya ma ta taba sayar wa Turkiyya makamai - wadda ita ma mamba ce ta Nato.
Kuma a tuna cewa Nato ta shafe shekara fiye da 70 a matsayin makwabciyar Rasha (wato kasar Norway).
Kuma babu alamar Nato za ta shigar da kasashe kamar Ukraine da Georgia da ma sauran tsofaffin kasashen da ke tarayyar Soviet cikin kungiyar a wani lokaci nan kusa.
Saboda haka me yasa Fadar Kremlin ke kafewa kan batun dangantakarta da Nato?
Dalili na farko shi ne domin hadin kan kasa: Batu ne da ke hada kan Rashawa idan suka ji tana fada da wasu abokan gaban kasarsu.
Akwai kuma batun Rasha na neman dalilin sauya alkiblar tsaron yankin Turai domin ta amfana da shi; domin kuma ta kara karfin fada ajin da ta ke da shi a shekarun baya, ta kuma sauya tarihi ta bangaren Yakin Cacar Baki da aka yi wato "Cold War".
Shin wane mataki Rasha za ta dauka nan gaba?
Tun da babu dukkan cikakkun bayanai, da wuya a iya sanin inda za ta sa gaba. Yana yiwuwa Amurka ta nemi tattaunawa da Rasha kan tabbatar da tsaron a Turai, matakin da ka iya gamsar da Vladimir Putin.
Idan haka bai samu ba, kuma shugaban na Rasha na son wargaza tsarin tabbatar da tsaron nahiyar Turai, to babu makawa sai an gwabza yaki baya ga zaman doya da manja na lokaci mai tsawo da za a yi tsakanin kasashen gabashi da na yammacin Turai.











