Yakin Ukraine: Me ake nufi da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, kuma ya yake aiki?

Asalin hoton, Reuters
An kafa Majalisar Dinkin Duniya ne bayan kammala Yakin Duniya na Biyu ta hanyar hada kan kasashen duniya wuri guda domin su warware matsalolin da suka addabi duniya.
A karon farko, Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya fara zama ne a 1946, kuma shi ne kwamitin da aka dora wa alhakin tabbatar da zaman lafiya a fadin duniya.
Bayan mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine, Shugaba Volodymyr Zelensky ya bukaci kwamitin tsaron da "ya dauki mataki nan take" domin dakatar da mamayar ta Rasha.
Mambobin kungiyar 15 ne - biyar cikinsu na dindindin ne goma kuma ba na dindindin ne ba - kuma su ke da ikon saka wa kasashe takunkumi da amincewa a yi amfani da karfin soji domin kwantar da hankula da tabbatar da tsaro.
Sai dai sau da yawa kwamitin ba ya iya daukan matakan da suka dace saboda mambobinsa na dindindin na hawa kujerar na ki wato su kan ki amincewa da matakin da kwamitin ya dauka saboda suna da ra'ayoyi mabambanta tsakaninsu.
Saboda haka, ta yaya Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ke aiki?
Mambobi na dindindin
Kasashe biyar na da wakilci na dindindin a Kwamitin Tsaron n Majalisar Dinkin Duniya: Amurka da Birtaniya da China da Rasha da kuma Faransa.
Wannan tsari haka ya kasance na lokaci mai tsawo, kuma ba a sauya shi ba tun shekarar 1946.
Hawa kujerar-na-ƙi
Wani muhimmin batu game da wadannan kasashen biyar masu wakilcin dindindi shi ne za su iya kin amincewa da dukkan wani batu da kwamitin ke yin muhawara a kai.
Wannan na nufin idan mamba daya ya ki amincewa da wata shawara da kwamitin ya yanke hukunci a kai, babu yadda za a iya aiwatar da kudurin ke nan.
Sai dai kwamitin na iya aiwatar da kuduri idan wata kasa ta ki kada kuri'ar kin amincewa da kudurin.
Saboda haka wannan tsarin yana da tasiri a wannan lokacin - musamman ma da Rasha ke mamayar Ukraine. Babu yadda za a iya kauce ma wannan yanayin.

Asalin hoton, Reuters
Mambobin da ba na dindindin ne ba
A kan zabi wasu kasashe goma cikin kowace shekara biyu domin su zama mambobin kwamitin da ba na dindindi ne ba.
Dukkan mambobin Majalisar Dinkin Duniya na iya zama mambobin kwamitin.
A watan Afrilun 2022 mambobi goma na kwamitin da ba na dindindin ne ba su ne: Indiya da Kenya da Ireland da Mexico da Norway, da Albaniya da Brazil da Gabon da Ghana da Hadaddiyar Daular Larabawa.
A kan kuma ba dukan mambobin kwamitin damar shugabantarsa na tsawon wata guda, ko mambobi na dindindin ne ko ba na dindindin ne ba.
Yadda yake ɗaukar mataki
Kwamitin na mayar da hankalinsa ne kan wanzar da zaman lumana da hana barkewar yaki tun da farko. Amma da zarar wani rikici ya barke, aikinsa na farko shi ne ya nemo a sasanta tsakanin masu rikicin ta hanyar diflomasiyya.
Idan rikicin ya ci gaba, kwamiti tsaron na iya samar da hanyar tsagaita wuta da tura dakarun da za su shiga tsakani.
Yana kuma iya bukatar kasashe sun kakaba wa wata kasa ko wasu kasashe takunkumi sannan idan haka bai samar da abin da ake fata ba, kwamitin na iya bayar da umarni a yi amfani da karfin soji kan kasar da ke mamaya.
Tilas ne dukkan mambobin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya su amince da hukuncin da kwamitin tsaron ya yanke.

Asalin hoton, Reuters
Suka kan gazawar Kwamitin Tsaro
An sha sukar Kwamitin Tsaron saboda kin daukar mataki yayin da wani abin takaici ya faru - duk da cewa an hango shi yana tafe, kamar kisan kiyashin da aka yi a Rwanda a shekarar 1994.
Jerin samamen da kungiyar tsaro ta NATO ta rika kai wa a Yugoslavia a 1999 an yi su ne ba tare da amicewar kwamitin tsaron ba.
Kasashe da ke cikin kungiyar tsaro ta Nato - musamman ma karkashin shugaban Amurka na wancan zamanin Bill Clinton - sun ce daukan matakin da suka yi a Yugoslavia ya dace kuma sun hana kashe dubban al'ummar Albaniyawa da ake tuhumar dakarun Yugoslavia ke yi a wancan lokacin.
Rasha kuwa ta ki amincewa da matakin na Nato, tana cewa rashin samun amincewar Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya kara ruruta wutar rikicin ne maimakon kwantar da shi.
Mamayar da Amurka da Birtaniya suka yi ma kasar Iraki a 2003 ma sun yi shi ne ba tare da amincewar Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ba.

Asalin hoton, Getty Images
Kwamitin ya dauki wasu matakan ba sani ba sabo a wasu lokutan.
Tsakanin 2006 zuwa 2015, ya kakaba ma Iran wasu matakan ladabtarwa da suka hana ta mallakar makamai da fasahar kera makaman nukiliya.
Kuma tun 2006, kwamitin ya amince da wasu kudurori 12 kan Koriya ta Arewa akan shirinta na kera makaman nukiliya.
A 2001 kuwa, ya amince da a kafa wani yanki a sararin samaniyar kasar Libya wanda ya taimaka aka hambarar da gwamnatin Muammar Gaddafi.
Sai dai har yanzu akwai sauran rikicin cacar baki da bai kau ba. A 2012, Rasha da China sun ki amincewa da wasu kudurorin kwamitin tsaron da aka shirya za su matsa wa gwamnatin Shugaba Bashir al-Assad - wanda ke da alaka ta kut-da-kut da Rasha.
Saboda haka dukkan wani kuduri da za a gabatar a gaban Kwamitin ba zai sami amincewar dukkan mambobin Kwamitin Tsaron ba domin Rasha za ta hau kujerar-na-ki domin kare muradunta da kanta.











