An dakatar da mutum biyu kan zargin jima'i a motar Majalisar Ɗinkin Duniya

Vehicles of a convoy United Nations Interim Forces in Lebanon (UNIFIL) ride on a road along the border between Lebanon and Israel

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana sa ido kan Majalisar Ɗinkin Duniya saboda zarge-zargen rashin ɗa'ar aikata jima'i a 'yan shekarun nan

Majalisar Ɗinkin Duniya ta umarci wasu ma'aikatanta biyu su tafi hutun dakatarwa ba tare da albashi ba saboda zargin aikata jima'i cikin wata motar aiki a ƙasar Isra'il.

An ɗauki hotunan ma'aikatan ne suna cikin wata mota mai tambarin Majalisar Ɗinkin Duniya a kan wani babban titin birnin Tel Aviv.

A cikin bidiyon an ga wata mace sanye da jan tufafi ta ware ƙafafuwa a kan wani namiji da ke kujerar bayan motar.

MajaDuniya dai ta ƙaddamar da wani bincike kan hoton bidiyon mai tsawon daƙiƙa 18 bayan an yi matuƙar yayata shi a kafofin sada zumunta cikin watan jiya.

Mai magana da yawun Babban Sakataren MajaDuniya, Stéphane Dujarric ya ce ya "kaɗu kuma ya auka cikin damuwa" da abin da ke ƙunshe a bidiyon.

Yanzu dai ta ce an gano mutanen da ke cikin bidiyon a matsayin ma'aikatan Hukumar sanya ido kan Yarjejeniya ta Majalisar Ɗinkin Duniya, sojoji ne masu sa ido na MajaDuniya da ke da sansani a Isra'ila.

Jami'an biyu an dakatar da su daga aiki ba kuma tare da samun albashi ba a tsawon lokacin da za a shafe ana gudanar da bincike kan wannan al'amari.

Mista Dujarric ya faɗa wa BBC a ranar Alhamis cewa dakatar da jami'an daga aiki, abu ne da ya dace "saboda girman zarge-zargen da aka yi musu na gaza kiyayewa da mizanin halayen da ake tsammanin gani a wajen ma'aikatan hukumar ƙasashen duniya".

"Hukumar UNTSO kuma ta sake bijiro da wani gagarumin gangamin bunƙasa wayar da kai don tunasar da jami'anta game da wajabcin da ke kansu na tabbatar da aiki da Kundin Halayen jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya," cewar Mista Dujarric.

MajaDuniya na da tsauraran manufofi da ke yaƙi da rashin ɗa'ar aikata jima'i a tsakanin ma'aikatanta.

United Nations Interim Forces in Lebanon (UNIFIL) patrol the area around the southern Lebanese town of Kfar Kila on the border with Israel

Asalin hoton, Getty Images

Kuma ana iya ladabtar da wani jami'i idan aka gano ya keta dokokin halayyar aiki.

Haka kuma ana iya tura ƙeyarsu zuwa ƙasashen da suka fito ko kuma a haramta musu shiga duk wani aikin wanzar da zaman lafiya na MajaDuniya, amma alhakin ƙasashensu ne su sake ɗaukar ƙarin matakin ladabtarwa a kan su ko kuma gurfanar da su gaban shari'ah.

An shafe tsawon lokaci ana sa ido kan Majalisar Ɗinkin Duniya saboda zarge-zargen rashin ɗa'ar aikata jima'i daga jami'anta na wanzar da zaman lafiya da kuma sauran ma'aikata.

A 'yan shekarun nan, an yi ta samun irin waɗannan zarge-zarge.

A bara, an samu zargi 175 na jima'in ci-da-gumi da kuma cin zarafin lalata a kan jami'an MajaDuniya, in ji wani rahoto.

A cikin waɗannan zarge-zarge, an haƙiƙance da faruwar 16, sai 15 da ba a haƙiƙance da su ba yayin da kuma har yanzu ake ci gaba da bincika ragowar.

Babban Sakataren MajaDuniya António Guterres ya yi alƙawarin bin matakin "rashin lamunta ko ƙaƙa" ga duk wani nau'in rashin ɗa'ar aikata jima'i a tsakanin ma'aikatansa.