Coronavirus za ta sa mata miliyan bakwai samun ciki a duniya - MDD

Mace mai ciki

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar Da Ke Kula da Yawan Al'umma Ta Majalisar Dinkin Duniya UNFPA, ta ce cutar korona za ta haifar da karuwar juna biyu da ba a shiryawa ba.

UNFPA ta bayyana hakan ne a wani rahoto da ta fitar ranar Talata 28 ga watan Afrilu.

Hukumar ta yi hasashen cewa idan har aka yi wata shida cikin dokar hana fita, kusan mata miliyan 47 a kasashe masu karamin karfi ba za su samu kai wa ga hanyoyin da suka saba ba na matakan hana daukar ciki.

Hukumar ta ce a za a iya samun juna biyu sama da miliyan bakwai saboda kulle da al'ummar duniya suke ciki.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

Ta kuma yi gargadi kan karuwar rikici tsakanin ma'aurata da za a iya samu sama da milian 30 a tsawon wannan lokaci.

Shugabar UNFPA Dr. Natalia Kanem ta ce: "Sabbin bayanan sun nuna irin bala'in da Covid-19 za ta iya jawowa mata da 'yan mata nan kurkusa a duniya baki daya.

''Annobar na kara jawo rashin daidaito, miliyoyin mata da yara a yanzu suna fuskantar rashin yadda za su tsara iyalansu da kare jikinsu da kuma lafiyarsu.''

Rashin samun kulawa

UNFPA ta yi binciken tare da hadin gwiwar Cibiyar Lafiya ta Avenir da Jami'ir Johns Hopkins ta Amurka da Jami'ar Victoria ta Australia.

Hukumomin sun ce cutar korona na jawo tarnaki ga mata da 'yan mata saboda yadda aka yi wa cibiyoyin lafiya yawa wasu ma an rufe su. A hannu guda kuma mata na tsallake muhimman lokutan ganin likita don duba lafiyarsu saboda tsoron kar su kamu da cutar korona.

Sun kara da cewa tsayar da samar da kayayyaki ya janyo karancin magungunan hana daukar ciki.

Sannan tuni an samu karuwar cin zarafin mata saboda annobar, kamar yadda MDD ta ruwaito a farkon watam nan - kuma ta ce ana sa rana zai karu saboda mata za su kasance a kulle gida tsawon lokaci.

Wannan layi ne