Ɓangaren shari'ar Najeriya ya fara farfaɗo da kimarsa - Masana

Asalin hoton, supreme court
Masana harkokin siyasa da shari'a a Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu game da hukunce-hukuncen da kotun ƙolin ƙasar ta yanke game da zaɓen gwamnonin wasu jihohi bakwai na ƙasar.
Wasu masana fannin shari'a na ganin hukunce-hukuncen sun farfaɗo da martabar ɓangaren shari'a na Najeriyar.
Wani lauya mai zaman kansa a birnin Abuja, Dakta Umar Mainasara Ibrahim Kogo, ya ce ya kamata a yaba wa ɓangaren shari'ar ƙasar saboda hukunce-hukuncen sun taimaka wurin inganta martabar ɓangaren a idon al'umma.
'Sun fara la'akari da cewa akwai giɓi tsakanin yawancin hukunce-hukuncen da suke yankewa da kuma yadda jama'a ke karɓarsu, musammman yadda suke dogara kan abubuwa marassa muhimmanci da ke danne ainihin zallar gaskiya idan aka zo maganar shari'a'. In ji shi.
Ya ƙara da cewa alƙalan sun yi ƙokari saboda ba su bari ka'idojin zaɓe sun shafe dokokin ƙasa ba, kuma sun hana a ɗauko wasu al'amuran da ba su shafi tsarin mulki da dokar ƙasar ba domin kawo cikas a harkokin shari'a.
Ya ce, ''alƙalai ya kamata su ɗauki kansu a matsayin wakilan al'umma wurin wanzar da adalci da gaskiya, ta ƙokarin tabbatar da cewa ba a yi amfani da dabarun lauyoyi wurin danne wa masu gaskiya haƙƙinsu ba.'
Dakta Mainasara ya yi kira ga hukumar zaɓen ƙasar da ta tashi tsaye wurin tsabtace yadda take gudanar da al'amuranta domin a rage aukuwar kura-kurai a ɓangaren zaɓe.
A ɓangaren masana siyasa, Farfesa Abubakar Umar Kari da ke jami'ar Abuja ya bayyana cewa hukunce-hukuncen kotun ƙolin za su taimaka wurin ƙarfafa dimokraɗiya a ƙasar.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ce, 'abin da dimokuraɗiya ta tanadar shi ne kowanne ɓangare ya yi aikinsa, hukumar zaɓe za ta gudanar da zaɓe ta kuma ayyana waɗanda suka yi nasara. Su kuma waɗanda ba su gamsu da wannan sakamakon ba dimokuraɗiya ta ba su damar cewa su kai ƙara kotu, ita kuma kotu ta saurari ƙara ta kuma yanke hukunci. Kuma a nawa ganin waɗannan hukunce-hukuncen sun sami karaɓuwa.'
Farfesa Kari ya ce dole ne a samu waɗanda hukuncin kotu ba zai yi masu daɗi ba, amma idan har an yi adalci wurin yanke hukunci kuma jama'a sun amince da hukuncin da kotu ta yanke, hakan zai taimaka wurin ƙara ƙarfafa dimokuraɗiya a ƙasar.
'Ni dai a ganina mafi yawan waɗannan jihohi, waɗanda aka ayyana cewa sun ci zaɓe, akwai alamun cewa su ne al'umma suka zaɓa. su waɗanda suka kai ƙara suna son ne su sami nasara kan waɗansu hujjoji na shari'a, amma ba wai a kan cewa su ne suka ci zaɓen ba.'
Waɗannan masana da wasu daga al'ummar Najeriya na fatan cewa ɓangaren shari'ar ƙasar zai ci gaba da ɗaukar matakan da suka kamata domin kauce wa duk wani lamari da ka iya haifar da shakka da za ta shafi ƙimarsa da kuma tabbatar da adalcin da ake tsammani daga gare shi a kodayaushe.










