Kotun ƙoli ta tabbatar da nasarar Abba a matsayin gwamnan Kano

Abba Kabir Yusuf

Asalin hoton, facebook/Abba Kabir

Bayanan hoto, Abba Kabir Yusuf

Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP, a zaɓen gwamnan jihar Kano na 2023.

Mai shari'a John Okoro wanda ya karanta hukuncin ya ce kotun ɗaukaka ƙara ta yi kuskure wajen tabbatar da hukuncin kotun sauraron ƙorafin zaɓen jihar, wadda ta ce Abba Kabir bai samu rinjayen ƙuri'u a zaɓen watan Maris ba.

Saboda haka, kotun ta yi kuskure wajen zabtare wa Abba da NNPP ƙuri'u.

A game da batun rashin kasancewar Abba Kabir ɗan jam'iyyar NNPP, kotun ta ce jam'iyya ce kawai take da ikon tantance ɗanta ko wanda ba ɗanta ba.

Saboda haka ne kotun ta amince da ɗaukaka ƙarar jam'iyyar NNPP, tare da yin watsi da hukunce-hukuncen kotun ɗaukaka ƙara da kuma na kotun sauraron ƙorafin zaɓen Kano.

Wannan shi ne matakin ƙarshe a turka-turkar shari'a da aka kwashe tsawon watanni ana yi, game da sahihancin sakamakon zaɓen gwamnan Kano.

Tun da farko, kotun zaɓen gwamnan Kano a watan Satumban 2023 ce ta soke ƙuri'a 165,633 wadda in ji ta, aka yi wa ɗan takarar na jam'iyyar NNPP aringizo, bayan hukumar zaɓe a watan Maris, ta ce ya samu ƙuri'a 1,019, 602.

Gwamna Abba dai bai gamsu da hukuncin ba, don haka ya wuce zuwa kotun ɗaukaka ƙara.

Sai dai, ita ma kotun ɗaukaka ƙarar ta bai wa jam'iyyar APC nasara bisa hujjar cewa Abba ba ɗan jam'iyyar NNPP ba ne lokacin da aka tsayar da shi takara, don haka ta nemi a rantsar da ɗan takararta Nasiru Gawuna.

A ranar 20 ga watan Maris na 2023 ne Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ta ayyana Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan na jihar Kano.

Babban jami'in tattara sakamakon zaɓen gwamnan, Farfesa Ahmad Doko Ibrahim ya bayyana cewa Abba Kabir ya samu ƙuri'u 1,019,602, yayin da Nasiru Gawuna ya samu ƙuri'u 890,705.

Hujjojin da kotun ta dogara da su

Mai shari’a John Okoro wanda ya karanta hukuncin, ya ce shari'ar ta dogara ne a kan zargin da ake yi wa Gwamna Yusuf na yin jabun katin jam'iyyar NNPP da kuma aringizon ƙuri'u, waɗanda aka ce Inec ta yi masa.

Batutuwa ne a cewar Mai shari'a Okoro za a tantance a wannan ɗaukaka ƙara.

Ɗaya daga ciki shi ne ƙaramar kotu ta yi daidai da ta soke ƙuri'a 165,616 a cikin ƙuri'un da aka kaɗa wa Abba Kabir.

Da kuma ko tambayar ko ƙaramar kotu ta yi daidai wajen ɗauka cewa tana da hurumi a kan batun ko gwaman ɗan jam'iyyar NNPP ne.

'Ƙuri'un da ƙaramar kotu ta rage wa Abba, halastattu ne'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayan bitar muhawarar da lauyoyin ɓangarorin biyu suka yi, Mai shari'a Okoro ya ce: “Na gano cewa hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓe na zaftare ƙuri'a 165,616 daga sakamakon Gwamnan, ya dogara ne a kan tanade-tanaden Kundin Dokar Zaɓe na 2022”.

Sai dai, alƙalin ya ce sashen kundin bai fayyace tsarin yadda harkoki za su gudana a rumfunan zaɓe ba. Ya kuma yi tambayar, "Ko mene ne tasirin kuri'ar da ba ta da tambarin hukumar zaɓe?”

“Ƙuri'ar da ba ta da tambarin Inec, ba za ta zama lalatacciya ba”.

Mai shari'a John Okoro ya ce sai lallai an tabbatar da hujjar cewa ƙuri'ar, ba ita ce hukumar zaɓe ta aika don gudanar da zaɓen ba.

“Babu wata hujja da ke nuna cewa ƙuri'un da ake magana a kansu, ba su ne aka yi amfani da su a zaɓen ba. Don haka hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke tabbatar da hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓe, kamata ya yi a jingine shi,” in ji Mai shari'a Okoro.

A ƙarshe, ƙaramar kotu ta yi kuskuren fashin baƙi kan batun ƙimanta ƙuri'un nata. Wannan daidai yake da karkatar da adalci.

Don haka abin da ya dace, shi ne a mayar wa Gwamna Yusuf dukkan ƙuri'unsu,” cewar Mai shari'a Okoro

'Batun ko Abba ɗan NNPP, ba al'amarin shari'a ba ne'

Dangane da batun ko Gwamna Abba Kabir Yusuf, ɗan jam'iyyar NNPP ne, Mai shari'a Okoro ya yi bitar muhawarar lauyoyi.

Jam'iyyar APC da ɗan takarar gwamnanta Nasiru Yusuf Gawuna sun yi musun cewa Gwamna Yusuf bai tsaya takara a zaɓen 18 ga watan Maris, bisa doron jam'iyya ba.

Mai shari'a Okoro ya ce kotun sauraron ƙararraki ba ta taɓa yanke hukuncin cewa Gwamna Yusuf bai cancanci tsayawa takara ba, kamar yadda Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yi kuskuren cimma matsaya”.

Don haka ta yanke hukunci kamar yadda Mai shari'a Okoro ya karanto cewa batun fitar da gwani, al'amarin cikin gida ne na jam'iyya ita kaɗai. Don haka ba za a iya hukunci a kansa ba.

A cewarsa, Sashe na 177 ƙaramin sashe na (c) na Tsarin Mulki, ya yi hani ne kawai ga ɗan takara mai zaman kansa (indifenda), babu ƙarin wani abu.

Saboda haka ƙaramar kotu ta yi kuskure bisa tanadin doka, da ta shiga bincikar batun ko gwamnan ɗan jam'iyyar NNPP ne ko a'a, Okoro ya ƙara da cewa.