Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ana fargabar Tamowa za ta tsananta a arewacin Najeriya
Kungiyar likitoci ta 'Doctors Without Borders' ta bayyana cewa an samu ƙaruwar yara masu fama da tamowa a jihohi 11 da ke arewacin Najeriya da suka haɗa da Borno da Katsina da Sokoto da Zamfara da Bauchi.
Kungiyar ta bayyana hakan a cikin rahotonta na rubu'in shekarar nan ta 2024, inda ta ce an samu yara 1,250 a jihar Borno kaɗai da ke fama da tamowa mai alaka da rashin abinci mai gina jiki, wanda ya nunka da kusan kashi ɗari a wasu yankunan, arewa adadin da ya zarce na shekarar bara.
A cikin sanarwar da ta fitar MSF ta ce: "A cikin makonnin nan an samu gagarumar ƙaruwa a yawan yara masu fama da mummunar cutar rashin isasshen abinci, wadda ke barazana ga rayuwarsu - waɗanda ake kai wa asibitocin ƙungiyar".
Ta ƙara da cewa wannan "abin tashin hankali ne idan aka yi ƙiyasin abin da zai faru lokacin da matsalar za ta kai matuƙarta a watan Yuli".
Shugaban ƙungiyar ta MSF a Najeriya, Dr Simba Tirima ya ce: "Tun shekaru biyu da suka gabata muke ta gargaɗi game da yiwuwar munanar rashin abinci mai gina jiki. Shekarun 2022 da 2023 sun kasance masu muni, amma abin da zai faru a 2024 ya fi muni".
Jihohin da aka bayyana a matsayin waɗanda matsalar ta fi shafa, akasarin su jihohi ne masu fama da matsalar tsaro.
Borno, inda abin ya fi ƙamari ta kwashe kusan shekara 15 tana fama da rikicin Boko Haram, lamarin da ya tagayyara kimanin mutum miliyan 2.5.
Wanna matsala ta yi tarnaƙi ga ayyukan noma da kiwo da harkar kasuwanci.
Mutane da dama sun zama ƴan gudun hijira, inda aka samar da sansanonin tallafa wa ƴan gudun hijira a faɗin arewa maso gabas.
Duk da cewa gwamnatin da ta gabata ta Muhammadu Buhari ta sha ikirarin cin galaba a kan ƙungiyar, har yanzu tana ci gaba da kai harin ɗauki ɗaiɗai.
Kamar wuraren da sukan fuskanci rikice-rikice a faɗin duniya, masana na ganin cewa za a ɗauki tsawon lokaci kafin abubuwa su daidaita.
Rahoton ya ƙara da cewa wasu jihohin arewa maso yammacin ƙasar ma an samu ƙaruwar yaran da suka kamu da tamowa.
‘’A cibiyoyin kula da ƙananan yara na Zurmi da Shinkafa da ke jihar Zamfara an samu ƙaruwar kashi 30 na yaran da suka kamu da tamowa a watan Afrilu idan aka kwatanta da watan Maris, sannan a Talata Mafara aka samu ƙarin kashi 20’’, in ji MSF.
Haka kuma ƙungiyar Likitocin ta ce an samu ƙaruwar matsalar tamowa a biranen Kano da Sokoto da kashi 75 cikin 100.
‘’Haka ma an samu ƙaruwar yaran da ke fama da matsalar rashin abinci mai gina jikin da kashi 20 a cibiyar kula da masu lalurar da ke jihar Kebbi tsakanin watan Maris da Afrilu’’, in ji sanarwar.
Ƙungiyar ta ce tun a shekaru biyu da suka gabata take gargaɗi game da yiwuwar fuskantar ƙaruwar matsalar tamowa tsakanin yaran arewacin ƙasar, to amma ta ce na wannan shekarar ya zarec yadda ake tunani..
A watan Mayun ne Majalisar Dinkin duniya ta gwamnatin Najeriya suka yi kiran buƙatar dala miliyan 306.4 domin magance matsalar tamowa a jihohin Borno da Adamawa da kuma Yobe.
To sai dai da alama wannan kuɗi ya gaza duba da yadda matsalar ya bazu a wasu sassan jihohin yankin arewacin ƙasar, kamar yadda ƙungiyar MSF ta yi bayani.
Medicine San Frontiers ta ce akwai bukatar kara wayar da kan jama'a da hada karfi wuri guda domin kawar da wannan matsala da ma cutuka da dama da suka hada da maleriya sauran.